_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......49
"Yah kace infito mutai kuma naga kusan ten minute baka tada motarba, plss bacci akeji wlh."
Shanyayyun idanunsa ya zuba man kamar maijin bacci,yana wani juyasu duk sun rikita man lissafi,dauriya kurun nake wlh yau yaya duk ya susutani don nikadai nasan menakeji wanda ban tab'ajin saba............"suger nah babu inda zamu har sai kinfurta man abunda nakeso,inba haka ba daga nan kinsan inda zan kaiki.?"
D'an shagwab'e fuskata nai ina dan juya kai nace cikin shagwabar da bansan inayiba"nidai gaskiya aa,kamaidani gida kuma niba suger dinka bace."
Wani irin yanayi yatsinci kanshi ciki,lumshe ido yayi yanajin kamar yakamota yasa cikin kirjinsa,daurewa yayi murya can ciki kamar yn tsoron yi tace"ta waye idan ba tauba,koshi wanda kike kiran tashice ke bakiga da yake Allah yasa ke rabona bace ya daukeshi,don haka kibar wani cewa keba suger na bace ur my honey sweet and suger for me."
Juyowa yayi sosai yana fuakanta ta duka hannayena yarik'o yana d'an mammatsasu kad'an,wanda jinake kamar nayita kuka saboda hanayin danake ciki,wani feeling ne da ban tab'a jinsa ba,sabone agareni wata irin kasala da mutuwar jiki sun lullub'eni..........cikin taushin murya da lauya harshe,yada zai idasa kashe man sauran d'an kuzarin daya rage man..........*INA SONKI UMMULKHAIRAT,INASON MALLAKARKI KIZAMO ABOKIYAR RAYUWATA,INASON KI ZAMO UWAR Y'AY'ANA KISANI TSAWON SHEKARA ASHIRIN DA BIYU INA DAKON KAUNARKI,KECE _ABIN CIKIN RUHINA_*
Tuni hawaye suka wanke man fuska kukana nake kasa kasa,inajin kaunarsa shaukinsa suna sake mamaye man dukan nin gangar jikina........shashshekar kuka nake na matse hannunsa sosai nafara magana cikin kuka da bayyana duk wani shaukin kaunta.
"Yah kayi hkr........kayi hkr bazan iya bujire umurnin mahaifiyata ba,idan na bujire mata na zama diya marar sanin ciwon kan ta dana uwarta,kuka ya sake kubceman nacigaba da cewa.
Aduk duniya bacin iyayena yah kaine mutun daya danake ma wani irin so wanda ni kaina bazan iya sanin iyakar saba,insonka yah Areef ina kaunarka tundaga farkon zuciyata har karshenta,amman bazan iya butulcewa mahaifiyata ba,koda hakan nanufin rasa raina.......wani kukan ya sake kubceman mai cin rai......tuni hankalinsa yayi masifar tashi,sake matsowa yayi kusadani duk ya rikice jikinsa anshi rawa yake,yace"oh my god sorry sweetheart,karkice aka karkiyi kokarin ganin kin janye dag gareni,ke kadaice hope dina insonki wlh khairat ina kaunarki,bazan iya yin waa rayuma mai dadi inbabu ke ba,wlh na tabbatar maki da cewa awannan karon muddin kika yi saken auren wani wlh wlh mutuwa zan hawayensa naji suna sauka kan hannuna,idonsa yayi wani irin jajawur bakinsa banda rawa babu abunda yake,bakinsa yasa yana sumbatar hannuna kamar zararrare,duk ya susuce."Plss babyna karki bari arabamu,zanje in samu maah inroketa tabarmu da juna,nasan Abbu bazai zama matsala ba kamar ta ba,na rokeki karki gujeni inada heart attack kuskure kadan zai iya jefa rayuwata cikin hadari,kece kadai zaki iya cetona plssss baby sweetheart wlh ina sonki kiyafe man laifina danayi abaya zafin sonki ne da kishinki,,,,,,,,kamar karamin yaro haka yayita kuka yana kissing hannu na ni kaina kukan nake saboda na tabbatar shim din mutuwa zai ya barni,shikenan ni rayuwata haka zata cigaba da kasancewa,duk wanda na kwallafa raina dashi saiya barni........kukana yayi karfi sosai ya tallabo fuskata idonsa har lokacin kwallah na zuba,fuskarnan tayi jaa gefen kuncin sa yasa yana gogeman hawayena,yayinda nashi basu dakata daga zubarba..........kamar yadda ya tallabo fuskata nima hannuna dake rawan nasa na rik'o nashi muka k'urawa juna ido kowane yanajin zazzafan son d'an uwansa...........ban yi auneba naji tattausan lips d'insa kan nawa saida na sauke nannauyen numfashi,saboda yadda naji wani irin shock ya kamani.
Cikin natsuwa yake tsotsar bakina har lokacin nidashi kukan muke,tsawon five minute ya d'auka yana sarrafa harshena.........kafin ya janye bakinsa muryarsa ta dishe sosai yace"kisani duk randa namutu cikin wannan halin kece da kaso sittin da alhakin hakan,zan kyaleki bazan sake maki wanan maganar,tunda har bazaki tayani yak'in da nakeyi ba,sannan har kice kina sona kindamu da halin da muke ciki,haba baby kinmun adalci kenan shikenan muje gida"
Abunda yace kenan ya tada motar,zan iya cewa har muka iso gida nidashi babu wanda yasake cewa komi,jikina yayi masifar sanyi da kalaman sa,bakin get yayi parking ya bude zai fita nai saurin rik'o hannu sa kwallah share share cikin idona.
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda