_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......14-15
Basai na kwatan ta muku yadda daren ya kasancewa khairat ba,domin kuwa bacci duk yadda ya kware wajen sata to fah wannan ranar ya gagara satar khairat,yadda taga rana haka taga dare,don kasa kwana tayi dakin su itada salmar,kuka tun tanayi da hawaye har ya dawo idon ya bushe,wani irin zafi takejin kirjinta nayi kanta kamar zai rabe gida biyu,haka meenah tayi lallashin tagaji tayi bacci ta barta.
Duk wani tashin hankali da na kejin zuciyata aciki, nayi iyakar yina nayi control din kaina kafin gari ya waye,don nayi wa kaina rantsuwa da alkawarin idaniyata ta gama kukan *SO* kuma insha Allah zanba marad'a kunya.
Shirin bacci jahid keyi yana yi yana kallon Areef da ya kwanta kasa saman kafet din dake malale tsakiyar dakinsu,ko combus din dake kafarsa bai cireba balle ya samu damar fara canza kaya,girgiza kai kawai Jahid keyi don lamarin Areef abun yana kaishi Bango,tsaki yaja wanda Areef baisan ma yana yi bah..........
"Dallah malam tashi anan,kawani sheme kasa kamar Wanda aka aikowa sakon mutuwa."
Kallon jahid din yayi yana sauke ajiyar zuciya,lumshe kyawawan idanunsa yayi yana sake yin filo da hannayenshi,baice ma jahid komi ba.
Haushi ne ya sake turnik'e jahid,don ganin yaki kulashi wani tsakin ya sake ja yana hayewa gadonsu wayarsa yafiddo yana danne danne........tsayin mitina babu wanda ya sake kula kowa har jahid ya gama abunda yake yayi addua ya kwanta.
Sai lokacin yyi magana."Jahid baka ga kamar Abbu ransa ya baci sosai ba."
Cikin kuluwa yajuyo yana cemashi,
"Au sai yanzu kagane haka ashe,ai babu anfanin hakan wallahi kabani mamaki Areef,yadda ka bashi kunya ka nuna cewar kana bayan maah,kasan me hakan kenufi kuwa.?to bari ni na gaya maka,kanuna cewar bai isa dakai ba,kuma shi ba matsayin mahaifi yake wajenka ba."Sai lokacin yayi saurin tashi zaune idonsa ya canza kala saboda damuwa yace,
"Karka fassarani haka jahid,taya zan dauki mutumen da ya haskaka rayuwata irin haka,kasan matsayin da naba Abbu ciki zuciyata kuwa."Wani tsakin yaja yace mashi,
"Duk irin matsayin da kabashi baida wani anfani,tunda har ka wulakanta bukatarshi gaban kowa,kadaina cewa yana da babban matsayi wurinka."Rutse idonsa yayi da karfi yana jin kamar ya kama jahid da mugun bugu,don jin irin kalaman da yake anbata mashi.
Cikin muryarsa data canza sauti saboda bacin rai yace,
"Karka sake anbata mani irin haka,na fadi iyakar gaskiyata ne saboda banson ya dauki amanar ta yabani inakasa rikewa,because i don't love her salma nakeso itace wadda na zabarwa kaina matsayin abokiyar rayuwata,akanme zanyi karyar yin abunda nasan ba zan yiba,idan kadamu ne saboda nace bason pls and pls jahid marry her."Murmushin takaici yayi yana kallonsa kafin ya gyara jinginarsa jikin gadon yace,
"Areef kenan wallahi tallahi kaji rantsuwar dan musulmi ko,da ace babu wata acikin raina ban riga na furta inasonta ba,jiya dana baka mamaki gabankowa zan ce ni yabani aurenta,saboda khairat matan dake ma maza wuyar suce,kuma kaima nan gaba am sorry 2 say wallahi u will regretting."Wani wawan tsaki yaja ya mike yashige toilet yana cewa,
"U are not in ur sense wlh,nidin zanyi regretting akan wannan yarinyar marar hankali,mtsss amman babu wanda ya kasheni irinka Allah ya isana wallahi."
.......yashige warshi.Jinjina kai kawai jahid yayi yana hango yada lamarin zaikaya.
*************
Tun da na tashi da asuba nayi sallah nake karatun qur,ani saboda in kara samun kwarin guiwa,saida naji zuciyata tayi sanyi sannan na tashi yah meenah har ta koma bacci,fita nayi don har lokacin banajin bacci sosai saidai kaina da yayi nauyi saboda rashin baccin,kitchen nasamu anni tana had'a break dinsu Dady don dashi suke tafiya,itada maah idan yau wanan yyi gobe wannan yyi,tsarinsu gwanin burgewa.
"Annie ina kwana,ai ina cewa sadaqallahul azim nayo nan,saboda k'amshin girkinki d a ya hana hancina sak'at."
Murmushi a kan fuskarta tana motsa fruit salad da ta gama had'awa tace,
"Lafiya lau yar gidan Annie,Amman dai kinsan ko lashe bazan y'an maki ba ko."Ansa nayi ina zubawa cikin mazubin da take niyar zubawa nace,
"Ba komi k'amshin ma da naji is okay for me,zai cika mun cikina."Kallona tayi ina cigaba da idasa hada basket din break din nasu,cikin tausaya wa tace mun.
"Y'ar gidan Annie kallanni."Banyi musuba na d'ago ina kallonta.
Hannuna ta rik'o dana gama saka komi tace,
"Bakiyi bacci ba khairat,karkice mani abunda yafaru jiya shine ya hana idonki runtsawa,idan kuwa haka ne to banji dadi ba,khairat shin ko kin manta da cewar yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau imani ne,ladace mai tarin yawa karki soma yin halin irin na marasa ilimi,ke yarinyace mai ilimin addini dana zamani,zanso aduk sanda kika tsinci kanki acikin wannan halin kiyi anfani da iliminki,don haka kiyi mani alkawarin wannan shine karon farko kuma na karshe."Kaina yana k'asa nace,
"Annie nayi maki alkawarin haka insha Allah.""Yawwa diyar albarka naji dadin haka,nasan kuma tunda kikayi man alkawari bazaki karya ba,Allah yayi maki albarka ya kuma cigaba da karfafa maki akan komi,dauki break din kikai falon Abbunku shizai wuce dashi,dadynku sabko yayi don suna da bak'i."
Dauka nayi na nufi cikin fat dinmu,
Kowa bacci yake don lokacin karfe bakwai da rabi,falon na sameshi yana karanta jarida,maah na zaune gefenshi, yana yin dana gansu ya nuna akwai damuwa.
Sallama nayi na ajiye ina gaida maah,ta ansa cikin kulawa shima na gaidashi.Nai zaune ina jiran ya fadan abunda yasa yace in sameshi da safe,jinai yace mum.
"Ta alkairi kije zuwa dare mun hadu,amman ki tabbatar kiyi baci isashe don idonki ya nuna jiya bakiyi bacci ba."Ina wasa da hannuna nace,
"Insha Allah Abbu,saika dawo Allah ya kiyaye."Cikin kulawa yace,
"Amen Allah yayi maki albarka."Nace"ameen"na baro falon
Mom muhseen
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda