_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......29
Washe gari mukai shirin koma wa school,nasa rigima dole yah shahid zai kaimu don inada wani plan..........saida yabiya damu mukai shopping sosai saboda semister mai tsawoce,duk da dai Auren yakusa inso samuna nane abarshi nagama aji ukuna,sai ayi lokacin mana cikin hutu,zan ma dr magana yayi wa su Abbu magana abarmu mukarasa wannan semister.
Hira muke tayi yana taya mu,ahaka har na sako batun husna inacewa.
"Wallahi yah meenah ban tab'ayi kawa irin Husna ba,tana da kirki ga kokari,kisan idan akai abu class tasan ban ganeba muna dawowa hostel mungama duk abunda zamuyi zata ce inxo muyi bita.....bata barina har saina gane,ina sonta sosai gashi akwai natsuwa."
Ina maganar ina satar kallon fuskarshi murmushi yake amma baice komi ba,nace"yah kaima ai ka lura da haka ko rannan daka sameta gida."
Shan mur yayi yace"don ubanki zama zanyi inta kallonta har naga wani abu tattare da ita."
Shiru nai ina kunshe dariyata yah meenah na tayani,
Sai kuma yace"kawai dai tana da tarbiyya akwai girmama nagaba."
Dadi naji ya kamani nace"sosai kuwa wallahi husna tayi,shiyasa cousin dinta dake sonta yake bala,in jida ita bayason kowa yana rab'arta kishinta yake sosai."
Kallon fuskarsa nayi naga dandanan ta canza yah meenah banda dariya babu abunda take,ni kuwa na sha mur irin dagaske haka maganar take,bacin karya ce kurun na shatata don ingane yana ciki ko haukana nake.Bai sake ce mana komi ba amman yanayin sa gaba daya ya canza,magana zan ciga gaba dayi ya dakan tsawa dole naja bakina naguntse,banji haushiba nasan kishine yake damunsa dadi yakamani na kaga mu isa in fesa mata albishi.
Har bakin get din hostel ya kaimu muka tsaya fiddo kaya,don suna da yawa saboda kayan yah meenah.
Kin tafiya yayi yana ta danna waya,zuwacan yace "kikirata ta taya ku daukar kayan mana."
Wayyo dadi haka naji aikuwa nai maza na shiga contact dinta na danna mata kira.
"Besty nah gamu bakin get pls kizo ki taya mu kwasar kaya tare muke da yah meenah."
"Besty ina hangenku ganin bayanku yanzu nadawo daga cefane bari in karaso."
Dadi kamar yayi yaya dani don inson wannan kaunar ta jone,
Kamar wasa sai gata sai fara,a take tunma kafin ta san waye amotar,
"Yah meenah oyoyo,wallahi naji dadin zuwanku zaman nika dai ya isan,kewa tayi mun yawa."
Rungume juna mukai ina mata oyoyo.
A kunne nayi mata rad'a nace"kalli gefenki pls."
Juyawa tayi ta ganshi zaune cikin mota,kirjinta yabada rassss duk ta diririce daker tace tana yar fara,"yah shahid ur welcome."
Dagowa yai ya kawata fuskarsa da murmushinsa mai kyau yace"Asma,u ykk ya makarantar."
Tana wasa da hannunta tace"dasauki makaranta yah angode Allah."
Jinjina kai yayi yace"Allah ya bada sa,a ga friend dinki nan na maido maki na fita ko."
Dariya tayi kadan ta kalleni na kashe mata ido guda tace"ka kuwa kyauta wallahi thank you."Murmushin yayi mata yana tada motar,
"Ga wannan akara kudin siyen garin rogo."
Dariya tayi ta ansa tana godiya tace"ai mu bama cin irin wadannan yah mu fa inkaga dish din damuke ci zakaso kazauna dakinmu."
Yana dariya yace "ok zan gani wataran zan maku shigar bazata."
Matsowa mukai muka mashi sallama yayi mana jan hankali kan karatu sannan yafita.Ihun murna nake harda taka rawa,bada dariya babu abunda suke man har mukaje daki............nan fa na sata gaba da tsokana badai tace komiba wai kunyar yah meenah take,
"Nace bur wallahi lallai kin ma daina wallahi,wai besty ya kuka kare rannan."Mikewa tayi zatabar dakin nai saurin rikota,
Yah meenah tana dariya tace"husna ya haka mun zama daya fa ki bar jin kunyata ni banajin taku,inkuwa haka ne daki zan canza."
Dole ta dawo na matsa mata saita gaya man yadda sukai.
"Wallahi besty kinfi ciwon ciki katsawa,bafa wani abu ya faruba kawai ya na ta jana da firar school ne tare da cewa kardai na biye samarin makaranta su hanani karatu,shikenan fah."
Murmushi nayi nace"soon zakiji ya kiraki yana cewa Asma,u in bakeba sai rijiya mai kwalabe."Gaba daya muka saka dariya,tun tana nokewa taki sakin jiki da yah meenah har ta sake,ranar munsha fira don babu mai lectures cikinmu sai tomorrow morning.
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
A hankali rayuwar take gurgurawa har gashi fara shirin exams,saboda nayiwa dr magana yayiwa Abbu magana yabarni na gama aji uku na,ya kuma yi mashi yayarda ga shirye shiryen biki ga na exams,dole dr ya hakura da takura man kan kira da kuma zuwa,don ma ba sosai muke haduwa ba ko acikin schol din.
Saidai koran weekend yazo ya dauke mu muje yawo da shopping.Duk abunda nakeyi ba wai na mance da *ABIN CIKIN RUHINA* ba ne Aa babu second ko awa da zuciyata bata bugawa dashi,daidai darana guda bai tab'a barin zuciyata da *ruhina* huta wa ba,banda wani abun tunawa dashi,illa kalaman sa na karshe nidashi airport.
_ina maki fatan Alkairi matar muhammad kaseem,sai wata rana bazaki sake ganina ba,kiyi hkr dani mun haramta ga juna har abadan,domin bazan iya karya wa maah Alkawarin taba,zanje nayi jinyar zuciyata kikula da kanki And plsss forget About Areef farouk,good by ummulkhair._
Wadannan kalaman sun zamar mani kamar fatiha cikin sallar farillah,duk daren duniya sune suke amsa kuwwa cikin kunnena,juriyace da karfin hali kawai suke rike dani,don nayiwa Abbu Alkawarin hakuri da kaddarata,yace man na tai makeshi karya rasani,in nabiye shiga damuwa komi zai iya faruwa dani,don ciwon zuciyata zai iya tashi kuma likita ya sanar da su cewa inhar nasa ke irin wannan kwanciyar,komi zai iya faruwa dani don haka inyi hakuri kowa da kalar jarabawarsa ke kuma taki haka tazo,don haka ki yi wa Allah godiya tare da kokarin ganin kin cinye jarabawar.
Kalaman Abby kenan ranar dazan dawo makarnta,naji nasihar sa sosai don inason Abbu na ba zanso ya shiga wani hali ba saboda ni.Zuciyata ta azalzaleni akansa har nakusan shiga wani yanayi,kalamnasa da ya gaya man ranar kafin mufita mota sune suke tunzura bacin raina,har ma inji to miye na kwallafa raina dashi tunda koda babu dr nasan yadda ya fadi kalaman hakan nanufin nai mashi kadan.
_k'wailaye daku berori da bakusan kanku ba._
Wadannan kalaman sunfi komi kona man rai,har nakan kalli kirjina dake cike masha Allah,wanda nasan idan za,a tara mata goma cinkinsu da wuya asamu biyu masu irin breast dina,shine yake ceman k'waila,to nayarda dai salma k'walarce Amman ni wallahi ba ita bace.
Haka dai nake ta abuna abu wanda yasan halin nake ciki,illah yah meenah da besty husna.Suma ba suda abun yi man face lallashi da ban baki,insuka na yini daki ko lecteres ban jeba nakicin abinci sosai sun san abunne ya tukoni,zasuyita lallashina suna gaya man kalamai masu kwatar da hankali,sai inji nasamu natsuwa.
Rannan dai nazauna nayi wa kaina karatun ta natsu,nace shifa wanda nake wannan haukan donshi yana can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali,wata kila man ya shafe babina ya bude wani sabon shafin,kilama yayi budurwa ko ince yayi yanmata don nasa shi gwanin farin jinine akansu.
Tunda natuna haka nacire ma raina yah Areef,ganin gamai sona kamar yayi mani sujada saboda tsananin kaunar da yake mani,to akan me zan dorama kaina damuwar wanican da ko kirana mu gaisa baiyi,saidai najishi suna waya da yah meenah amman ko agaidani baicewa,to kan wane dalili wata jotter ta sabuwa da ban fara komi cikin taba nayi rubuta kamar haka.*_NI UMMULKHAIR FAROUK,NAYI ALKAWARIN SHAFE BABIN SA CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN MAN TASHI CIKIN RAYUWATA,NAYI ALKAWARIN DAINA YIN CIWO SABODA SHI,BAZAN SAKE SAKA YAN UWANA DA IYAYENA CIKIN HALIN DAMUWA BA SABODA SHI,ZAN FARA SABUWAR RAYUWA DA MASOYINA KUMA MIJINA INSHA ALLAH._*
na jefata cikin tarkacena ban sake bai takan taba,don promise ne bazan karya ba zanba marad kunya inaha Allah.
Cikin yardar Allah muka gama exams,kuma muduka muna fatan samun sakamako mai ktau,daga wannan hutunne zamutai pratical sai munyi six months sannan mudawo makaranta.
Shirye shiryen bikinmu ake babu kama hannun yaro,duk kullum husna nagidan mu sai dare yah shahid yamaida ta,kasancewar yanzu babu laifi sun saki jiki dajuna amman ban tunanin yafurat mata yana sonta,suduka dai idan kagan su tare kasan akwai soyayya mai karfi,amman kowa jinkai dajan class ya hanashi,amman inanan ina hada masu tarko sai yah shahid yafurta da tsiya ma bada arzikiba.Mom muhseeen✍🏻
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda