43

31 3 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461

          🅿️.......43

Yau aka kai kayan saka ranar yah Areef da zulfa,ar sa.,ni yini nai ma ina bacci bansan wainar dasuke toya waba,kasanewar iyaye aza sukaje Abbu daya dawo yaga salma akai mai bayani,bai sake cewa komiba maah kuwa tsaye take don ganin ta karya asirin da raihana tayiwa Ameer,don muddin ba akarya shiba wataran ma sakinta zai.
Hangar da tabi wajen karya wanda sukaiwa khairat da Areef,yanzu ma ita tabi ta saka ayi saukar qur,ani sau bakwak,tace da iznin Allah da kanshi zai biyota har gida.
Don saubiyu Dady yana aikawa kiran ameer din yace zaizo in yasamu lokaci,wannan shine yakara b'atawa Abbu rai maah ce ke kwantar mashi da hankali cewa akyaleshi zai kawo kanshi.

Zuwa yanzu yah Areef so yake muna magana,amman kallon mutunci ma bai isan ba,sautari idan yana falon zajani da magana,idan na ansa to kujerar da nake zaune ta ansa itama,babu irin fad'an da maah batai mani ba naruntse idona cewa banda makiyi saishi,don shine yayi silar kashe man miji......wannan maganar tafi komi kona mashi rai shida maah.
Har rannan take cewa"wai don ubanki ke bakisan kaddaraba,eh akwai wanda ya isa ya kashe wani inhar kwanansa basu kareba,koda bai bankeki wayar ta fad'iba sai yabar duniyar alokacin da Aka rubuta barinsa,amman dayake bakida tawakkali kin kasa hakuri ki mance."
Kuka na saka mata nace"wlh maah baki tausayina,mai makon kigoyi bayana shine zakice man haka.......dalla rufe man baki tashi kiban waje."

Duk yana wajen ake wannan dramer jikinsa yayi sanyi,ganin irin kukan danake yace"kiyi hkr maah kidaina mata tsawa kingani ba ita kadai bace,sorry khairat kiyi hkr i don't mean 2 hot u.......wata harara na banka mai na mike nace"banyin hkr bazanyi ba,hankalinka dai ya kwanta dr yabarmaka duniyar kadauki duk abunda kake so cikin t...........jikake tass tasss maaah ta dauketa da mari mai tananin zafida d'i maucewa.........saurin tashi yayi ganin jiri zai kadani ya rikoni.......idona har duhu nake gani saboda tsananin yadda marin ya ratsani,
Fizgewa nai nafice dafe da kuncina,dayan hannun kuma dafe da marata da ta daure man,zuwa yanzu cikina yaki wata takwas.
daker na isa dakinmu na kwanta naita kuka kamar raina zaifita duk tambayar duniya mimi da Antu sida sunman amman bance msu komiba.
Ranar ban sake lekowa faloba,washegari naishigewata shashen Annie.......inajin ana cigiyata naki fita saida Abbu yakirani sannan naje.

Yana falon shi shida yah Areef din na samesu suna hira harda dariya,shiga nai da sallama daker nake d'aga kafata saboda nauyin cikin,daker na zauna ina gaidashi.

"Ta alkairin Abbu sannu kinjiko."
D'aga kai kurun nai kwallah na cika man idona,
Shafa kaina yake yana cewa"sorry don't cry,gaya man me yayanku yayi maki har bakya gaidashi,baruwanki dashi imfact ance har zaginsa kike."
Dagowa nai idona hawaye share share naceciki rawar murya"Abbu shine silar da dr ya rasu kuma ni wlh ban zagaiba."sai kuka ya barkemun bai hanani ba naitayi ina shashsheka.
"Sorry my dear,daina kuka muyi magana."sha fa kaina kurun yake yana lallashina daker nai shiru.
Yace"kiyi hkr ta Alkairina,Areef baiyi haka don wani abu yasamu dr kiba,kidauka daman haka Allah ya rubuta,dr bazai rayudake ba kiyi hkr kibar dora laifin kan shi,kingani babu kyau duk wanda kwanansa yakare babu tsumi babu dubara sai yatafi.don hk kibar zagin yayanki kuma kina ringa gaidashi,oky."

Ina kuka nace"Abbu nace maka ni ban zaginsa ni kawai yafita harkata  sabodashi fa maah dazun ta maran gashinan ma cikina ciwo yake."na sake rushewa da kuka.
"Subhanallahi,itaa dakanta aikuwa bata kyauta bazan mata magana,yanzu yayanki yakaiki asibiti."

"Ni Abbu banson ya kaini ciwonma yadaina."
Suduka murmushi sukai aranshi yace"rigimamma kawai."

"To shikenan daga yau kun shirya din haka yanzu ma yimashi magana."

Ido nad'ago na hararai dariya yayi yashgwabe fuska yace"kagani ko Abbu hararata take,kuma damun fita zata cigaba da daureman fuska."
Murmushi Abbun yayi yaa kallonsu sai hararashi take shikuma yana mata gwalo.

Yace cikin dan bata fuska"ta alkairina kinga tun kafin ajimu yiwa yayanki magana,kibashi hkr akan abunda kikaimai.daganan komi yawuce."
Kai na kasa ina hawaye"kayi hkr bazan sake ba."
Tashinai nafito nabarsu wajen.
Ranar yini nai inakunci duk wanda yamun magana sai kuka jnta masifa,ga ciki ya addaban abinci ma yanzu ban iya ci sosai gashi bana samun bacci isashshe,ayita halbina acikin......infalka inyita kuka.

Salma kusan watanta guda gida ta murmure ta saki jikinta sosai,kuma duk wasu d'abiu nadacan ta barsu kowa girmamawa take,ga son aiki yanzu kusan itada mai aikinmu yare suke aikin gidan,maah tayi tayi tabari tace ai zaman isarta yake.

Hajiyar su dr sunzo sunkawo kayan haihuwa duk abunda mai haihuwa take bukata sunkawo,harda kayan damukasiyo daga saudiya da kuma turkey,,,,,duk sun kawoman. Ranar mutuwar dr ta dawo man sabuwa banson iyakar lokacin dazan dauka ina missing dinsa ba,abunda sani kwai shine har abadan bazan mance dashiba bakina bazai gajiya wajen yi masa addua ba.

Cikina yashiga watan haihuwa,ummi ma tayi siyayya kamar hauka,har mamaki nake narasa waye yafi kaunata da hajiyar dr da ummi da kuma Annie,don kowa yayi shirinsa tsaf don tarbar baby.
Maah kuwa  ganin fushi nake da ita yasa ta kirani tayi man nasiha sosai har muka shirya.

Ina wajen ummi mimi na mammatsamun kafafuna dake ciwo, kasancewar bamu jima da dawo daga awo ba yah jahid da yah Arref suka kaimu,nida mimi wai saina kara sati biyu kozan haihu,jinai kamar nadunga cin ubansu don basu san yadda na k'agara na juye wannan nauyina ba wlh,ina zaune k'asa jingine da kujera salma ma tashigo anata hira,yah meenahnkuwa bata dawo daga wajen IT ba,anty shida kuwa daman bata faye shiga cikinmu ba.

Ummi tana d'akin Abban su mimi don yaune zai iso daga dubai,fitowarta kenan shikua yashigo ri'eda leda ga hannunsa babba,zama yai yana cewa "washhh,salma ban ruwa pls."
Tatashi tatafi ta kawo mashi mimi tace"yah sannu da dawowa."
Jinjin mata kai yayi baiyi magana ba,,,,,satar kallona yayi nai kamar ban ganiba,daker na danne zuciyata nace mashi "ina wuni."
Kamar jira yake yayi zak'al yace"lafiya lau uwar biyu."
Shiru nai bansake cewa komiba mimi tacigaba daban labarin wasu masoya ina dariya.
Ummi tashigo takallai "kaikuma fa?,daga ina haka da uwar leda meye aciki" ta jawo tana dubawa.
Kayan jariraine rigunan mata hadaddu,kai da kagansu kasan zasuyi masifar kud'i,santinsu kurun ummi keyi dasu salma.
Ni kaina kamar na tanka amman banson inyi dariya gabanshi,tunda na kalla sau d'aya ban sake kallonsu ba.
"Areef ina kasamu wadannan kayan,sunyi kyau sosai ina zaka dasu."

Mik'a yayi yana cewa"gata nan gabanki ta wani baje kamar kayan da ba,aso."
Dandanan raina ya b'aci ganin duk dariya ma suke,aikuwa kamar yasan ba shiru zanba,yamike zawuce yana dariya.
Naita sababi kamar me suma bawanda ya kulani  don sunsan halina idan akatab'oni.
Saida na huce nashiga yaba kyan kayan tace ai naune shi yasiyo man,nace tace ina godiya.
Ina mamakin yadda ya kwaso duk na mata,to kdan namijine fa saidai yamayar abashi kudinsa.

Lokaci nata ja har nashanye sati biyunan ban haihuba,duk nashiga damuwa hankalina duk yatashi,Su ummi ke kwantar mun da hankali don wata sa,in sai ince ma ummi,"ummi wai don Allah haihuwa akwai zafi,inkinsan akwai zafi kawai mune acire manshi banson inwahala."
Satace ina ai babu wata wahala,kina zaunema zakiji kin haihu taita kwantar mun da hankali da wannan na sakankance cewar kilanma ina bacci zan haihun.
Amma sai me cikin dare ciwo ya tasoni gaba kamar zan mutu.






Mom muhseen✍🏻

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now