_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......41
Cikin kwanakin nan biyu da dawowarmu,ko kusa bana iya kai lomar abinci bakina,dama kuma ga kwaikwai ya tasoni gaba,kamar jira yake dr ya mutu ban iya ko d'aga yatsana.
Yanxu ko ice cream din nasha saiyafito,balle wani youghout ko wani abucan,xuciyata banda kuka babu abunda take kullum ganin abun nake kamar za,a tasheni daga nannauyen baccin dana fad'a......amman ina it's the reality babu abunda ke canzawa,tun hawayena suna zuba har suka zo suka kare.
To karewa mana tunda bayadda banyi don suzuba ko zan samu saukin zuciyata amman kemadagus basu fitowa,saidai fitinennen zafi da zuciyata keyi,inji kamar ankunna wata gagarumar wuta cikinta.Lallashi da ban baki kuwa ba abbuna na ba ummi ba ba Annie ba ba maah ba,kowa yi yake bakin kokarinshi,shiyasa nake iyakar yina don nima na karfafa kaina.
Yan school dinmu sunzo man gaisuwa sosai ranar ban iya sanin inda kaina yake ba,saboda banson abunda zai tuna man mutuwar,duk da ba mancewa da ita naiba.
Shiyasa idan anzo mana gaisuwar bama su isowa inda nake,saidai ayiwa su maah da su ummi,don yanzu ummi fat guda ake gyare masu suma danasu b'angaren,da cewa tai gida zasu siya suzauna Abbu yace aa gadai isasshe waje dazai wadacesu, basai sun wani sayi gidaba.
Bedroom uku ne bangaren,amman kowane akwai tazara tsakaninsa da d'an uwanshi,guda na Abbansu idan yazo aka gyaremashi shi fesss,daya kuma na ummin sai gudan na sadam,don mimi tana nan bangaren maah shidama oga kwatakwata da bangarensu shida jahid.Akwana atashi babu wuya wajen ubangiji har anyi wata guda da rasuwar Dr,har su yah meenah sun koma makaranta,yayin da ni dole zan ajosting semester har sai na gama takaba,watau na haihu kenan,gashi IT zamu tafi da mu dawo sai muyi exam daganan zamu shiga final year........amman gashi ni zanyi westing one year saboda rasuwar mijina dole zan mashi takaba,inda Allah ya taimakeni ma baiwuce nayi ta wata hudu ba na haihu,tunda gashi har anyi one month........an daga bikin su yah jahid dasu yah meena har saina haihu.
Lokacin nafita takaba abun zaifi armashi,Tunda muka dawo gida magana bata shiga tsakanina da shiba,domin kallonsa ban sonyi wata irin tsanarsa nakeji sunan sa ma banson inji wani dake kusadani ya anbata,inda zan ganshi ma bana kallo don jinake banda mak'iyi irinsa,duk sanda natuna shine dalilin rushewar farincikina shine silar da har dr ya rasa ranshi,akanme bzanji haushinsa ba kari da cewar tunda akai rasuwar baimun gaisuwaba,ko kallona baiyi balle ya tausayama halin danake ciki.
Sannan ga wani bakin cikin naji kishin kishin aurensa tareda nasu yah jahid........zaniya cewa inajin haushi zan iya cewa banaji,bazan iya yankewa kaina hukuncin abunda nakejiba kan maganar aurensa dana faraji kasa kasa,zuwa yanzu babu laifi nafara sakin jikina magamace dai har yanzu bakajin inayi sosai,inba da Abbuna ba.Yau husna tazo itada momin su sake dubani,kasancewar yanzu zmunci ake sosai tunda za,a hada zuria.
Ganin husna yasa nasaki jikina muka sha hira ,take bani labarin IT dinsu yadda yake kasancewa,sainaji inama nima inayin nau amman kaddara tariga fata,ga mimi gabyah meena sai ynin ranar yayi mun dadi,sai bayan sallar magruba suka tai.bayan tafiyarsu
Na wuce wajen ummi don yau tace mun tayi sinasir miyar zallar hanta tasha Alayyahu sai k'amshi take,don yanzu babu laifi cin abinci nake kamar jakadon cikin dandanan yake sani jin yunwa. Kasancewar yafara nauyi don yashiga wata shida, baje baje nayi falonta nida ita inaci tana karaman,muna hira rabon danaci abinci mai yawa irin wannan zan iyacewa tun kafin nasamu cikin nan,ita kanta ummin dadi takeji yadda nasaki jiki yau sai labari muke.
Kamar daga sama ya shigo falon cikin wata irin kyakkyawar shiga tatashin hankalin duk wacce ta ganshi,wata dankareriyar gizner ce brwon tasha wani arnen aiki jigunanne ya hadu iya hadu wa,har naka sa gane wane yafi mun haduwa shi da shaddar........baki da hanci kai har dama ido da kunne na saki ina kallon shi waya yake fuskarsa cike da tsananin murmushi,har kyawawan hakoransa suka bayyana,dumful d'insa guda d'aya ya fito sosai.......juya hannuna kurun nake cikin kwanon miyar dake gabana,yayinda ummi ta zage sai zuba man labari take.
Jin nayi shiru yasata d'agowa tana kallona bansan ma tana kallon nau ba,inda taga ina kallo tabi da kallo itama."Okay I'm sorry yau ai bazan ce haka ba,yanzu ma i'm on my way insha Allah......dariya yayi yana sauke wayar daga kan kunnensa.
Sai lokacin nai saurin kawar da kaina ina sauke wani wahalellen numfashi, ga kirjina da yake dukan tara tara.
Ummi ta kalleshi tace"wannan gayun fa Areef,kamar wanda zashi d'aurin aure,yaushe rabon daka saka manyan kaya kaga yadda suka maidaka babban mutun."Murmushin yake har lokacin ya zauna yana d'aura agogo yace"wlh ummi nima sai yanzu nagane hakan, don jahid da maah haka suka fad'a suma,zan cigaba da sawa insha Allah."
"Allah yasa,yanzu ina zaka haka gaf da isha,i."
Ya gama saka agigon kenan ya d'ago daidai idona yana kanshi,karaf sai cikin najuna kallon secon biyu mukaima juna yajaye idonsa,yana cewa"wlh ummi wajen *zulfa,a* zanje kullum dana saka ranar zuwan sai wani abu yashigo,kuma tana ta mun complain akan hakan,shiyasa nace yau bari naje kafin sadda zan koma Spain."
Sinasir d'in dake cikin bakina ina kokowar had'iyeshi shine ya kwareni,,,,wani irin tari ya tirnik'eni babu k'ak'k'autawa gaba d'aya hankalin ummi ta yo kaina tana bubbuga bayana ahankali amman hakan bai hanantarin ba,sosai nake tarin don bakaramar kwarewa nai ba,yana zaune yana kallonmu sai bubbuga bayan take......mik'ewa zai fita aikuwa yabata haushi tace,
"Ubanka nace gidan ubanwa zaka maza bani ruwa marar sanyai kitchen."
Fuskarsa babu alamun wani haushi ko bacin rai yajuya yaje ya kawo cikin cup,ta ansa taban kirba biyu nai na ajiye ina sauke numfashi..........jinai yace"zan iya tafiya yanzu."
Harararsa tayi yayi dariya yajuya yanabtafy ayana cewa.
"Wallahi ummi ke kowa mai laifine indai akan wannan kundubar yarinyarne."
Afusace ta mik'e tabishi da jifa da filo tana cewa,
"Ubanka nace ja,iri zaka dawo kasaman."
Sannu take ta faman yiman tana cewa"muje cikin gida cikin mutane rabu dashi don kundun ubanshi,zaisan da wanda yake magana."
Daker nake taka k'afafuna muka fita,banda duka babu abunda nakeji cikin zuciyata,wata babbaka nakeji kirjina namun.......wacece *zulfa,a* meke tsakaninsu wata zuciyar tace mun "toke miye naki kiji da rashi mijinki ma,koma meke tsakaninsu babu ruwanki."
Afiki kuma nace "hakane kuma,"
D'akinmu nawuce nabarta wajen su Annie suna hira.
Mimi nat waya yah meena na ta seaching ga system,na zube gefe ina sauke numfashi hira muke da ita amman kwata kwata hankalina baya kanta,bazan iya cewa ga kalma guda danake fahimta cikin zamcen da take man ba,ashe hawaye nake ni bama saniba saina naji tace.
"Subhanallahi!khairat kuka kuma meyafaru,badai har yanzu bazaki sakama zuciyarki hkr ba."
Share fuskata nai nace "sorry nadaina bari nayi wanka inxo na kwanta nagaji sosai."Mom muhseen✍🏻
09934722970.
Follow me on wattpad *Humaira3461**_Abdoul-nasser (Alfah) is very nice and sweet story,don't miss it,very soon zaifara zuwa maku karki bari abaki labari ABDOUL-NASEER (ALFHA) zai nishadantar daku*
![](https://img.wattpad.com/cover/322019083-288-k243490.jpg)
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda