5

27 2 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira7531

          🅿️.......5

Hana kowa shiga akai har sai nafarka daga baccin dasu kai Mani Allurarsa.

Anni aka bari wajena da Anty shahida sauran yah mujahid yakoma dasu,salma hada kukan ta bazata tafi ba saida Yah Aree yayi mata jan  ido sannan.
Shima d'in bai tafin ba zamanshi yayi duk yadda Anni ke fama dashi yak'iya,dole ta kyaleshi haka sukai ta zaman zuru har ten thirty,sannan nurse din ta lek'o tace shishiga na tashi,Amman wani Cikin su yaje doctor nason ganinsa.

Areef ya tafi Anni da Anty shahida suka shiga,

Gaisawa sukai da likitan sannan ya zauna,
Bayani yayi mashi akan abunda ke damunta.
"cewa damuwa ce ta sakar mata masassara sannan da alama ma andoketa ne hada wannan dalilin yasa fever d'in tayi zafi, sannan dole akula da cin abincinta don bata cin abinci sosai,idan ba haka ba ciwon ulcer zai iya kamata, ga magani kasiya can phamercy."

Godiya yayi mashi sannan ya fito yaje yasiyo maganin ya jiyo zuwa d'akin da aka kwantar da ita,jiya ke kamar ya kama dukan kanshi haushin kansa yakeji sosai akan abunda yayi wa sweetheart d'insa, tsoro yake kar tayi dogon fushi da shi, don yasan halinta akan rik'o.......sallama yayi Yashiga Ya ajiye magungunan gefe ya kalli Anni,

"lafiya dai ko Anni."

"da sauk'i dai tunda muka shigo ta k'iyiwa kowa magana, sai kuka da take duk lallashin munyi Amman taki yin shiru."

Kallona yayi nayi saurin kawar da idona, Ina shashshekar kuka k'asa_k'asa yana son lallashin ta Amman Idan ya yiwa Khairat saku saku babu tantama raini zai shiga tsakanin su, so yake ya koya mata tsoransa wanda nan gaba baza ringa yi masa taurin kai bah,ya nason bata hakuri dukan jiya da yayi mata, Amman ya girmansa zai kasance a wajenta ba makawa raina shi zatai, Wanda shi bazai so haka ba zai nuna yama manta da abunda ya faru, Shan mur yayi wanda dole idan ta ganshi haka tashiga fargaba...... Cikin dakakkar murya yace,

"jiyo nan nace."

Jiyowar tayi gabanta na fad'uwa yace,
"goge wannan kwallar banzai, me akai maki yanzu da zaki kama yiwa mutane kuka, kin ma gaidasu tukun koko islanci ya hanaki."

Bani kad'ai ba su kansu sunsha mamakin Areef d'in,don basu tab'a ganin yayi mana irin wannan kakkausan lafazin, sab'anin y'an kwanakin baya ko fad'a zai mana cikin taushin murya da lallashi yake yi mana, baison ma wani yaji idan kuwa d'ayan mu tana kuka kamar ya taya ta saboda baya son kukanmu,amman yau shine ke d'aga mani murya yana kwatsata dole kowa yayi mamaki katseni yayi da cewa.

"maza ki goge wannan kwallar ki gaidasu Idan kuma na dawo baki saki jikinki kamar da ba nida ke ne."

Ya maido dubansa ga Anni yace,
"Anni bari naje na kawo maku abun break, zo muje *shidah*."
sunan da shikad'ai yake ce mata kenan.

Fita sukai suka barni da Anni, matsowa tayi jikin gadon da nake ta rik'o hannun da aka cire mani drip, tana kallona kallon da ban tab'a ganin Anni tayi Mani shiba jinai tace mun.

"y'ar gidan Anni yajikin naki."

idona ya ciko da kwalla nace,
"Anni Ina kwana."

Murmushi tayi tace,
"lafiya lau yajikin naki."

"da sauk'i Anni saidai inda yah ya dokeni jiya Anni ciwo yake mun ko zaki gasa mun."

tausayi ta bata Amman ta danne bata nuna hakan sosai bah tace,
"Ayya sannu kinji bari Antynku ta kawo ruwan zafi sai agasa maki."

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now