_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......44
Tunda uwar data haifani ban tab'a jin ciwo irin wannan ba,tashi nai nashiga toilet inyo fitsari da rarrafe na isa,amman ko kad'an yaki fitowa bansan sadda na kwalawa Annie kiraba,don ina bangarenta dakin yah meena,ita asibiti ta kwana.
Kankace me ciwo yayi kaca kaca dani,nifita hayyacina,duk wanda ke gidan yasan yau ina cikin tashin hankali,Abbu yace babu bukatar azauna gida atai asibiti kurun.
Kankace me yah Areef yafiddo mota jikinsa babu inda bai rawa,duk yafirgice zan iya cewa yafi kowa firgicewa,,,,,,,yah jahid yazauna mazaunin driver sai Annie da ummi baya nidasu shikuma yah Areef yashiga gaba,gudu yah jahid keyi amman Yah Aref cewa yake.
"Dalla malam kataka mota,baka ganin halin da take ciki inbaka iya bani waje."duk ya gigice yafita natsuwarsa ummi tace"banson hauka Areef duk wannan gudun baima ka ba,to sama kakeson ya tashi kome."
Hkr Annie tabaketa badawa "haba banson wutar ciki,ko anbaka motar awannan yanyin naka iya janmu kake kaje ka jefamu rami duk mu mutu."
Duk da halin da suke ciki saida suka dara,nikuwa banda ihu da kiran Abbu da maah babu abunda nake,Annie tace "yi hkr khairat insha Allah zaki sauka lfy."
Cikin azaba nace"banyin hkrn wlh bazanba aikunsan da wannan azabar kuka ki gayaman ko Wayyo Abbu nashiga ukuna bayana ummi marata zata fashe."
Me jahid zai ba dariya ba wani uban bugu Areef ya kaimashi yace"baka da imani dariya ma yakake ko."
Ummi ma dariyar tayi tace"barshi yayi wlh don ubanki ai kinji yadda take ko,tukunna ma bakina tunanin kina bacci zata zo ba,aikidauka ma baccin kike."
Annie tace"daurewa ake kiringa kiran hazbunannallhu wani imal wakil,yahayyu ya qayyumu birahmatika astagisu aslihli sha,ani kulluhu wala taqilni ila nafsi d'arfata ainin,ko kuma Allahumma la sahla illa ma ja,altahu sahlan wa,anta taja alul hazna iza shi,ita sahlan."Amman bud'ar bakin khairat tace"banyi wlh ban iyawa nabani zan mutu wlh kilan mutuwa zan,kuncuceni kun kasheni kucire man cikin nashiga ukuna ihu kurun nake ina kuka don ni kadai nasan azabar danakeji.
Ummi kuwa mezatai ba dariya ba tace"yo dan ubanki sadda kikai cikin mun sanine."
Jahid kunya kamar ta kasheshi Areef kuwa sai kunci yake don ganiyake duk basu damu da halin da take ciki ba cikin rashin jin dadin abunda tace yace"haba ummi waibaki tausaya mata ne kiga fa yadda take murd'e murd'e."
"Inkasake magana saina ci ubanka zaka sauka yanzu wlh,ni ban san ma uwar data sa kabiyo muba,kokaine zaka anshi haihuwar."
Shiru yayi yajin yadda khairat take sauke nishi da kakarin amai........sun isa asibitin cikin gaggawa aka ansheta,wata likitar matace ta dubani tace"ke wannan ai duka 3cm,ku koma kawai bama yanzu zaki haihuba sai kinkai yamma........ai ban bari ta k'arasaba na shak'o wuyanta cikin azaba nace"karya kike wlh,muguwa Azzaluma wlh baki isaba saikin cireman wannan cikin,kicireman shi ko in kasheki muguwa Macuciya....."
Ba karamar shak'a tayiwa wannan likitarba cikin wuya tace"ke sakeni kicikani yoni naimaki cikin,sadda kike shan dadinki ni saninai,shine zaki huce haushin kaina......sake fizgota nai duk su annie sun rik'eni amman kamar mai hanun doki sunkasa kwatar ta wani uban nishi na saki nace,
"Don uwarki ni ban sha dadiba,ubanwa yace nasha dadi,zaki cireman kokuwa saina cire kanki.........duk yadda kake tausayinta sai kayi dariya,yadda duk ta haukace gashinan ya warwartse,ta had'a wata uwar zufa ta masifa......ganin duk sun kasa ansheta yasa ya isa wajen yace"ku aketa pls,,,,,,,likitar zaro ido tai jin ance su ummi su saki khairat,kallonsa take da idonta daya fito sosai kwallah ta cika,tace"haba kaikuwa idan aka saketa sokake ta kashini."
Shikanshi dariyar yayi don wannan dramer dole tabaka dariya.
Yace"bazata kasheki ba ku saketa Annie kuga."
Sakinta sukai matar tasake zaro ido jin yadda khairat tasake shaketa tana nishi,da huttai tana wani irin gurnani.
Cikin sanyin jiki ya riko hannunta yana goge mata uwar zufar da takeyi,yace"sorry saketa kinjiko janki take,ko minty biyu bazaki k'araba zaki haihu,saketa tsokanarki take."
Kamar magic sukaga ta saki hannunta dake kan wuyar matar,tana dalalo ido takalli Areef tace cikin nishi da shashsheka"pls kace masu sufitar mun da cikinan wlh kashenj zaiyi plsss.........tafad'a hawaye na silalowa jiyai shima kwallah sun cika idonsa don tausayi,da yanada ikon ciremata ciwon da takeji ya mayar kanshi da bazata sha wannan wahalar ba.
Cikin lallashi da lalama da babu wanda yasan Areed ya iya yace"sorry my angel,zasu cire maki yanzu bada jimawa ba,kiyi hkr kedai kibar gardama komi nace kiyi karkiyi gardama kiyi kinko,inkikayi gardama bazasu cire maki shiba."
Duk da yadda nakejin wani irin masifar ciwo hakan bai hana ni cewa to ba,........su ummi kallonsu kurun suke suna mamakin yadda yake lallashinta,bayan su sunyi kamar ma zugata suke.
Kamani yayi muka sauko daga kan gadon.
Ummi tace"inazaku kuma."
Baice mata komiba toilet suka shiga alwallah yayi man,sosai nidai banda wash da innalillahi danake kira ban komi,itama innalillahin shiyace inyita kiranta,don bakina dimaucewa yake inkasa yin adduar.
Fitowa mukai yashimfid'a kallabina k'asa yayi ya d'auko hijab d'ina yasaman,duk suna kallona.
Zaunar dani zai nace daker"zan iyayi atsaye."
"OK good daure kinjiko insha Allah kina gamawa zasu cire maki wannan cikin."
Sallar naeyi daer na runtse ido,ban tab'a sanin haihuwa zaune tada d'uwawunta ba sai yanzu.
Raka,a hud'u nai adaddafe daker na sallame,nafashe da kuka ina cewa.
"Kuwa girman Allah kurabani da cikin nan wallahi kasheni zai........hannu ya d'ora kan lips dina yagirgiza man kai,idonsa duk kwallah sun cika su,yasha fa kaina yace"karki sake cewa haka,maza kiyi addua kuma duk adduar da Annie ta karanto maki cikin mota suzakiyita nanatawa,nasan kinsansu kinkuma iya.oya maza kiyi kowace sau uku uku kiroki allah duk abunda kikeso daure wa zakiyi kinjiko,ina murd'e-murd'e da hawaye nace to.likitar tace ma su ummi "wannan yaron akwai dubara,hakan da yai shine daidai,don bazamu iya control d'inta ba gaskiya ya iya kula da marar lafy."
Su kansu su ummi abun ya burgesu,ganin suduka babu wanda ya iyayi mta wannan.
Inayi ina kuka da murje murje, idan ta katsa saina mamuk'eshi gadagam duk shaddarsa nayi mata sqeuzing,ba damuba lallashina kawai yake mun dauki almost one hour sannan dr tace bari tasake dubani,kasamcewar dana gamar sallar ba zaune nakeba,yawo nake cikin d'akin,inta motsa idan na kamashi shikanshi sai yaji ajikinsa.amman ba damuba,sannu kurin yake mun.
Tana dubani tace"wow it's 7cm insha Allah yanzu zaki haihu kedai sake dagewa kina yawon,daure kinjiko insha Allah yanzu zaki haihu."
Zuwa lokacin jikina yafara galabaita duk karfina yafara karewa,durk'ushewa nai ina murzarshi sai hkr yakeban bansan ma yanayi ba,can wajen karfe shad'aya na safe data dubani tace aiga head nan ma,yah yafita shida su ummi.
Duk inda hankalina yake ya tashi nishi nake sosai ina rikea wuyar rigara ga,nace wlh baifita babu inda zaije........atakaice danai maishi wani irin rik'o saiga kukan jinjira,wata irin damk'a nai mashi wata jinjirai tasake sillob'owa........haba tuni na some.nanfa duk hankula suka tashi,tun lokacin ake nemo numfashina har azahar abun ya faskara,Areef kuwa kuka yake kamar Allah ya aikosa,rirs haka yake kuka,duk su Abbu sunzo,da su maah kowa yazo jin khairat ta haihu yan biyu amman daya ta rasu,sannan tunda ta suma bata farkaba tunda .........cikin ikon Allah gaf da la,asar tafarfad'o wata nannauyar ajiyar zuciya yasauke,baibi ta kan jaririyarba don gudar har anbinnota,gwanin ban tausayi,kowa baiso rasuwar taba amman ya suka iya,sungodema Allah ma da yasa uwar ita tafarka.
Kuka na nasha jikin Abbu jin cewar jaririyar daya takoma,sosai nake kuka har saida akaiman allaurar bacci sannan baccin ya saceni ina sauke ajiyar xuciya.
Tunda yaga tafarka yabar asibitin.
Gida yaje yasha kukansa kamar karamin yaro,don wani irin kishine maizafi ya turnekeshi,wai yau *ABIN CIKIN RUHINA* ce tahaihu da waninsa,shikenan yarasa abunda yake kwad'ayi,dukda badanshi yake sonta ba,Allahne kadai yasan yadda yake kaunar ta,amman baisan taya zai mallake taba,yanajin kunyar sake tunkarar Abbu da maganar ta,don kuwa yasan wancen karon bai kyautaba maiba.
Amman ya ya iya da azabar da soyyyarta ke ga namai,ga wannan kaddareren auren da ummi ta takura saiya aureta,saboda tana diyar qawarta.baisake komawa ba wanka yayi yafice office don yana da aiki sosai,hankalinsa kwata kwata yana kan khairat,don ya tsorata sosai ganin halin da take ciki dazun.
Duk da irin yadda jikinsa ke tsananin ciwo kuwa,don yasha damk'a bakad'anba kafad'unsa kamar yaji targad'e da cinyoyinsa,daker ya iya tuka kanshi ga bacci cike da idonsa amman sanin ayyukan dole yayisu yau yasa ya hkr ya tafi.*********
Kwanana biyu asibitin,sabida jinina daya hau don mutuwar jaririyar ta kasa barina,nasha kuka sosai saida naga b'acin ran Abbu sannan nayi shiru na hkr nabar kukan gaban mutane amman dana kadaice sainayi,saboda yadda naso ace naci kawa dr alkawarinsa na mallaka ma umminsa guda,yanzu ya zataji babu dai kokadan.
Nai mamakin rashin dawowar yah Areef,saibaza ido nake inga yazo har aka sallame mu baizoba,sanda mukazo gida angyara mana d'aki guda nida babyna,salma kamar ta had'iyae babyn,itadasu mimi sai nan nan suke da ita,yah meenah kuwa tani take sai sannu takeman.
Ranar umminsu tazo kasancewar batanan randa na haihu,rungumeta nai ina kuka nace"ummi kiyi hkr naso ace baby ta rayu nabaki ita,kiringa ganin jinin dr kina tunawa dashi,saidai kashh Bansan meyasa ubangiji ya ansheta ba .........kiyi hkr plssss."
Lallashina take itama tana goge kwallah tace babu komi wannan ma Ta wadatar uabngiji yayi mata albarka,yakuma rayata yasaka tayo halin mahaifinta.
Ranar nayi kuka saboda tunawa da mijina nai mashi addua sosai tare da abunda nahaifa,wata irin kaunace nakemata nan take Abbu yayi mata huduba da sunan ummin dr watau *maryam* aikuwa ba karamin dadi tajiba don hada kwallarta taita sunbatar babyn tana hawaye,kafin tatai nace saita fadi nickname din daza ringa fadamata daker da sidin goshi nasata tafada tace akirata da *Airah* sunan yayi matukar dadi saidare tatafi.
Ina tunanin ganinsa da daddare amman har wayewar gari baizoba,annie keman wankan jego intayi mata shagwaba.
Airah kuwa ummi ke mata kusan kwana hudu kenan,duk wanda yakamata yasan anyi haihuwar angaya mashi,husna kullum tanan saidare yah shahid ya maidata.Ina zaune falo inata kuka saboda ummi ta tsareni sananba Airah nono,nikuma zafin danakeji yasa nace nidai aa,shine ta ulaman bulala dole nabata ina hawaye itakuwa tsotsa kirun take kamar Allah ya aikota.......kamar ance na kalli kcofar shigowa naganshi yana murmushi,bayansa wata budurwace fara tas kamar zabaya,tasha gayu kamar zata zab'en sarauniyar kyau,babu karya akwai kyau jinai kirjina yabuga.
Mom muhseen.
![](https://img.wattpad.com/cover/322019083-288-k243490.jpg)
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda