46

20 3 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461

          🅿️.......46

Washe gari tun asuba da mukai wanka nida Airah bamu tashiba sai eleven,sadda na fito ina sab'e da ita zanyi break naji gidan ya rage hayaniya.
Lami mai aiki na tambaya ina mutan gidan tace"maah dai tana ciki itada su shahida,salma da mimi sunje rakiyar Areef,.........tundaga sannan naji jina gaba daya ya dauke bansan me take sake cewa ba.
Zamanai da Airah ga hannu kamar kwai ya fashe man ga ciki.

Kamar marar lafiya haka na koma,kukan airah ya dawo dani daga duniyar tunanina.har cikin raina banso tafiyar ba,duk da haushinsa dana kwana dashi,hakan bai hana ni jin kewarsa ba.
Dayanzu ya dauki baby bai maido man ita sai tafara kuka kokuma tayi bacci,hawaye naji sun cika idona nai saurin sharewa saboda mutsin danaji bayana.
Maah ce da anty shida suka shigo falo,ina kan dining nayi tagumi ga Airah sai kuka take bam jin kukan,saboda halin da zuciyata take ciki.

Jinai kurun Anty ta dauketa tana rirrigata,maah ta banka man harara.
"Wahalalla,kicigaba da yi kar Allah yasa kidaina,."
Idona cike da kwallah nace"maah menayi menamaki kuma."
Tsaki taja ba wuce warta ta cigaba da huddodinta,kuka na rushe dashi saboda banson abunda kuma nayi ba,meyasa maah keyin haka duk dan sabida ita nake treating yah Areef haka,Amma Ku ma still ban yi daidaiba............Anty shida tace"ansheta kibata tasha sai kicigaba."
Ansarta nai natashi na koma dakina abincin da banci ba kenan,yini nai daki duk mai son ganina can yake samuna.
Babu wanda yadamu da damuwata,abun ya hademan biyu koma ince uku.
Ga soyayyar wanda nasan har abadan bazan samesa ba,ga canjin hali daga maah sai hantara ta take,.........ga kewa da tsananin begen Dr sai tunaninsa ya dawo man sabo.
Ganin abun ya isan naje na samu Abbu da safe kafin yafita.
Duk nayi zuru zuru cikin kwana biyu ita kanta airah,don Annie na shigowa tana ansarta da wuyar da xata sha tana da yawa,don ma tafara wayau yanxu.
Break yakeyi keyi na samu Maah tana saving dinsa,harara ta watsa man naji kwallah sun cika idona.
"Ta alkairin abbu iso mana."
Shiga nai ina rakub'ewa jikin kunera nesa dashi,ina goge kwallata,
"Zomu Karya nasan baki kaiga yin nakiba,"
Girgiza kai nai cikin sanyin murya nace"Aa kaci naka Abbu idan nafita zanyi nawa,dama nazo ne kan batun makaranta anshiga sabon session."

Kunun gyadarsa ya kurb'a ya saka tsokar nama baki sannan yace"nasan da haka,zan tura jahid sai yayi maki duk abunda yadace.,sai mekuma."

Sadda kai nayi nace "bakomi"

Na zo tashi yace "zauna ban sallameki ba."
Zama nai ina wasa da yatsuna........duk gudan yafita kaina ummi kanta duk ta canza to wai menayi masu haka.

"Meke damunki kwana biyu,bakida walwala kina yini dki bki shiga cikin y'an uwanki...........meke damunta daya wuce wahala,yarinya tana son kunyatani tadauki son duniya ta dorawa mashi,kamar shikadaine autan maza........"duk maah ke wannan maganar.

Tuni hawaye sun wanke fuskata shashshekar kuka nake kasa kasa,saboda jin abunda maah tace,ni yaushe nayi wani abu har da zai nuna masu cewar har yanzu inason sa,to banyi karya ba inasonsa har gobe amman me wlh yadda ta nuna bata sona dashi nima shiyasa nake mashi duk abunda nai,shine zata ce haka.

"Badake nake maganaba saudah karna sake jin bakinki."
Ta banko man harara nasadda kai ina cigaba da kukana.
"Bakiban ansa ba ta Alkairi."

Ina sharben majina nafara magana cikin rawar murya.
"Abbu maah ce..........sai kuka ya kubceman na  tayin sa ina jan numfashi bai hananiba don daman kukan shine nakeyi nasamu sauki,
Saida nagaji nayi shiru nacigaba da cewa,
"Abbu bansan menayi mata ba,tun ranar da yah yatafi take daureman abu kadan taita hanta rata,kuma taki fitowa fili ta gaya man laifin danayi mata,inma don yah Areef ne wlh tallahi Abbu bana kulashi,ban shiga sabgarsa,shine yake damuna saboda ita ko maganar arziki bamuyi dashi.inbanda gaisuwa amman shine tace haka,wlh niban karya dokarkiba........na karashe ina kukana."

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now