_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira3461🅿️.......27
Missing page💕
Silalewa nazoyi zan zube sabo yadda jikina gaba ki dayanshi babu kuzari,babu karfi tare dani jinai anyi azamar rikoni,bazan iya gane ma kowaye ba nadaiji muryar yah jahid yan cewa abude mota,kilan shine yatareni.
Motar aka sakani sannan nafara gawowa natsuwata,ina hango jirgin ya lula cikin sararin samaniya,wani kuka ne ya kubceman mai rikitarwa,na dunkule waje guda inayin abuna.........Anty ce tarungumoni jikinta tana lallashina,
"Kiyi hkr mana ance makine yatafi kenan,duka wata nawane in Allah yakaimu."
Jinai yah jahid yace"nima cikin satin nan zantafi ai."
Cikin rudewa tace"rufaman asiri kabari idan anyi auren saimutai duk inda kakeso,amman wlh banda yanzu azan iya jurewa ba."Murmushi yayi yace"to taya kike tunanin ita zata iya jurewa,kinsan irin d'acin da takeji cikin zuciyarta kuwa."
Daina kukan nai don inason tabbatar wa shin dagaske auren za,aimun don maganganunsu sun nunaman cewa ansan da kaunarsu agida."Anty,wai dagaske aure Abbu zaiman."
Kallona tayi tace"ina kiji maganan nan,bacin anhana kowa yi maku ita."
Jinai wani kullutu yazo man wuya ya tokare,shiru nai ban sake tankawaba.
Don wani abun yafi gaban kuka sonake naje naji shin dalilin dazaisa atsigeman karatu ayiman aure,bayan ni nace baso banasoshi yanzu abarni nayi karatuna mana,wallahi duk wanda yayi dalilin wannan maganar Allah ya isarmu.Muna isa gida afusace nafito na wuce bangaren maah,bata nan na zube kan gadonta ina sharar kwallah jinake kamar nayi tsutsuwa na bishi,wani irin yanayi nake ciki rashisa yafi mun ciwo matuka akan auren da akece za,aimana,jinake banda wani sauran farinciki ko annashuwa akan tafiyarsa,duk wani feeling's dinsa danakeji ada can baya,na yanzu yalinkashi goma kirjina nakejin yana mun nauyi,jinake bazan iya kaiwa har wannan lokacinba,wata hudu koma fiye dahaka wannan abun danake ciki zaibarni kuwa.
Maah ce tafito daga bandaki tayo wanka,kallona take yi batace komiba.
Ina ganinta natashi na fada jikinta narushe dawani irin kuka mai tsananin cin rai.............bata kokarin lallashina ba kuma tabace mun komiba yinake yi har inajin kamar numfashina zai dauke,cikin kukan nake cemata"maah Meysa zaki yarda aiman aure nan,maah kinfi kowa sanin banso ni banso karatuna nakeso ayazu nakeson aurenba,maah wallahi in akayishi zanshiga wani hali kitai amakeni,kiyiman rai............rungumeni tayitsam jikinta muka kara sa saman gado da ita sai lokacin tashiga lallashina,
"Ya isa haka kidaina kuka,inkinason nayi maki bayani idan kuma bakyaso to kiyita kukan."
Dole nayi shiru ina sauke ajiyar zuciya sai shan majina nake,shiru duk mukai ina sauraronta.
Cikin taushin murya da lallami tafara man bayani."Bayan tafiyarki makaranta kinkoma hostel,zuwan inna gidannan yafi biyar tana zuwa wajen mahaifinku bai dawo ba,bayan yadawo tasake zuwa muna tare lokacin ko ansa gaisuwata bataiba,take yiwa Abbunku magana akan tana bashi umurnin cikin wata uku ya aurar da duk yaran dake gidannan,don salma taje tasameta akan cewa itafa batason karatu,aure takeso kuma wanda takeson ni nahana shi ya amunce da ita,ina son dole sai nabashi aurenki."
Anan tasan cewar Areef banau bane,tayi fada tatashi hankalin kowa agidannan,har takecewa sai yabar gidan tunda bana uban shi bane,wallahi idan baibar gidanba saita tsinema mahaifinku.
Ananfa shima yanuna mata nashi b'acin ran,yace Areef bazai tafi ko inaba shine ubanshi har duniya tatashi.
Tace to kuwa wallahi zaiga bacin ranta kuma muddin bai aurar dakuba tasan matakin da zata dauka akai,kuma wallahi muddin tana raye cikin ku jikokinta babu wacce zata auri Arref,.
Anan nace ta kwantar da hankalin duk cikin yarana baida mata,domin Areed dana nacikina nake kallonsa,yayansune shi tsayyae kan lamuransu,nan tace naimata rashin kunya ke tashin hankali babu kakkautawa,saida ker Annie tafiddata gidannan.

YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda