28

22 2 0
                                    

_*ABIN CIKIN RUHINA*_

*{RE-POST}* ©2019

Mrs bb
Mom muhseen.

Watt pad name
Humaira3461

          🅿️.........28

Gida na koma bayan an sallaman,don maah kin yarda tayi danace abarni makaranta na samu sauki,wai ita aa tafison ina gabanta har na idasa wartsakewa.
Yah meenah kamar ita ke ciwon duk tabi ta damu,kin komawa tai hostel wai saina warke mukoma tare,Abbu kanshi yashiga damuwa matuka inhar yana gida yini yake zarya dakin maah yana dubani,in yatadda ina bacci zai sunbaci goshina yace"Allah yayaye maki ta alkairi,Allah yana tare dake."
Cikin ikon Allah nasamu sauki sosai,har nakan fito falo adanyi fira dani,sabanin kwanakin baya da ko magana banson yi,kuma banson aiman,don idan aka cika man magana zan fashe maka da kuka,dole suka kyaleni amman yanzu ni da kaina nake fita can.
Dr yau yace zai zo ya sake dubani,kasancewar yanzu muna waya ba laifi,don anyi komi game da maganar auren mu,manyan shi sunzo anyi komi cikin mutuntawa.
Han itama salma nata sunzo duk rana daya za,a daura amman nasu Anty shida ba yanzu ba,yajahid yace ayi mashi hkr sai nan gaba akwai abun da yake maimuhimanci.

Nayi kokari matuka wajen ganin na cire damuwa da tunaninsa,amman lokaci lokaci nakan boye nayi kukana don shine abunda zai rageman radadin da nakeji na rashinsa.

Na fawwalama Allah komi na anshi dr matsayin mijina,tunda na lura son da yakeyi man maigirma ne,soyayyar sa mai sanyi da shiga ran duk wanda akemawa,hakika nayarda da maganar maahda take  cewa ya nada duk abunda za,a soshi,nafarko dr handsome guy ne dan gayune sosai,daga ya nayin shigarsa zaka gane hakan, sannan ma,abocin son kamshine kamar dai yah Areef,don shi kafinma ya iso waje turarensa ne d first dazai sallama wajen,to shima dr haka sannan ga fara,a ban taba ganinsa yana shan murba ko cikin aji fuskarsa asake,baza kace yana dariya ba kuma ba zakace yana shan mur ba,kadaran kada han,ya iya barkwaci,duk yadda kake cikin bacin rai zai iya saka ka dariyar dabaka shirya ba.

Dr Ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya daidaita natsuwata,nadawo cikin hayyacina shiyasa maah takejin dadi duk randa yazo,itace hada wannan itace hada wancen,haka Annie kai duk yan gidanmu kowa yana son dr sosai,amman banda salma don har yau salma bata shiga sabgar kowa.
KO Ameer dinta yazo babu mai wani rawar jiki,idanma ya samu gaisuwar kirki wajen yan gidanmu,saboda shima halinsu guda da ita,daidai gwargwado maah tana kwatanta adalci tsakaninmu duk da cewa ba itace ta haifeta ba,amman duk abunda ta siya man to zata soya mata itama,saboda tace har gobe salma diyace wajenta haihuwarta ne kurun ba taiba,don haka zatai mata duk abunda uwa take ma yarta.
Duk da wannan abun bai saka salma taringa gaida maah ba,bata gaidakowa yanzu,har gara idan yah shahid nanan zai ci ubanta yace kuma sai ta gaida duk wanda ke saman ta,duk randa akai irin haka bata kwana gidan sai tayi tafiyarta gidan inna,wannan abun da ta keyi ya kara sakaman salma tafita raina,don duk wanda bai girmama mahaifana ba nayi dashi.
Abbu duk yasan wainar da ake toyawa baidaice komiba,don inajin inna  tayi kalami mai kaushi akan salmar,bansan dai me tace mashi ba.

Rannan Abbu yazo har dakin maah yayi man ya jiki,ya saman ina bacci hirar su ta tadani,sai ban nuna na tashin ba,naji maah tana mashi complain din salmar yace"saudah,kiyi hkr kibar yiman zancen yarinyarnan,tunda kinsan bazan iya yin komi  ba,akan kunnenki inna tayi man Allah ya isa idan na sake takurata ko nayi mata wani abu daya bata ranta,kibarta tayi duk abunda ta ga dama kowa rai yaima dadi baya ga maishine,Godiyar danake ma Allah daya bata miji daidai ita,munanan daku Allah shine zaiyyi maganinta."
Maah bataji dadi ba tace"karkayi mata baki Dear,hannunka baya rubewa ka yanke kayar,ya kama ta kayi mata addua kurun."

Murmushi yayi yace"hakika samun mace kamarki mai tsarkakakkar zuciya sai antona,Allah yai maki Albarka Addua kuma ai tunda aka haifeta nake mata ita,don haka kifita batun salma karki ma sama ranki damuwa."

ABIN CIKIN RUHINAWhere stories live. Discover now