_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* @2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......3
Alhamdulillah gida ya tsaru iyakar tsaruwa,babban gidane mai fat Kala Kala wanda saboda girman Abota irin ta su Alhaji farouk yace da Amininsa jafar yazo su zauna tare,har kuka yayi saboda farin ciki haka suka dawo gidan rana guda, komi sabo aka loda masa yayinda tuni angyaare ma Inna wancan gidan ba zaka tab'a cewa shine bah.
Rayuwar ta cigaba da kasance masu Cikin jin dad'i da kwanciyar hankali,yayin da Wata irin shak'uwa mai K'arfin gaske ta shiga tsakanin *AREEF* da k'annensa *khairat da salma* idan Sun dawo makaranta shine wankansu ya shiryasu ya zubo abinci yaringa basu har sai sun koshi, sannan assessment d'insu zai zauna ya tusasu gaba yana guarding d'insu yaga Sunyi shi lafiya lau, Areef saboda k'annensa ko fita baya yayi, Duk nacin *mujahid* haka zai rabu dashi, haka shahid da shahida Duk yadda suka so Cikin weekend ya ringa binsu shopping sai yace bazai bisu bah, saboda suna cin zalin sweetheart dinshi,dole sukai hakuri saidai driver ya kaisu shikuma Ya ware rana ya kaisu da kanshi.........wata guda kenan da kammala secondary d'insa,tunda twince suka girma Maah ta hana yaringa masu wanka da shiryawa,tunda yanzu ko wacece zata iya yiwa Kanta wanka da shiryawa, yanzu suna js one yayinda shahid da shahida Suke ss2, Muhajid tare sukai graduation da Areef, Neenah ce take js3.
Shirye shiryen tafiyar Areef da Muhajid ake zuwa UK jamia,wanda idan suka tafi baza su dawo bah sai Sunyi har masters d'insu........
Motarsu na tsaya wa suka fito Aguje suna kyalkyata dariya,kowa so take ta riga y'ar uwarta isa cikin gida wajen yah Areef kafin Su shiga saiga su sun fito shida mujahid Aguje sukai kanshi, dariya suke masu shida mujahid......kafin ya ankare *salma* ta mamuk'eshi tana dariya har da yiwa *khairat* gwalo aikuwa me zatayi banda kuka, bilhakki da gaskiya ta shige gidan tana rera kukan shagwaba,duba Maah tayi bata ganta ba yasa ta nufi b'angaren Anni tana shiga sukai kacib'is Anni ce ta tatareta.
"lalalala kairyn Anni waya tab'aki zo zo taho muji."
Ta jata jikinta Maah tace,
"Uhm bai wuce rigirmarsu ita da salma, yanzu haka riganta tayi isa wajen Areef."Annin tace,
"wai haka ne yar gidan Anninta."
Wani kukan ta sake fashe wa dashi tana cewa,
"Anni kingani salma ko, kullum sai ta ringa rigana wajen Yah Aree,kuma nace mata yau ta barmun in rigata shine ta k'iya,gasu can suna mun dariya."
..........ta sake rushewa da kuka.Dariya Maah tayi tace,
"ai na gaya maki kullum rigimar kenan, salma ta rigani,salma ta rigani tunda ke lusara ce komi babu hanzari,ba dole komi salma ta rigaki ba ko wanka da shiryawa sai bakina yayi tsawo kike gama wa inhar Areef baya nan."Anni zatai magana Areef ya shigo rik'e da hannun salma, har tayi wanka da ga dawowar ta ga lollipop nan Areef ya bata tana ta sha.
"Ayya sweetheart gamu munzo biko,ke baki yin zuciya kiringa riganta kema, Amman kullum sai Kinyi kuka, Kinga zo zo mu shirya."
Maah dai ficewa tayi tabarsu Inda sabo sun saba wannan fad'an basu wuce d'an lokaci kad'an sun shirya.
Anni ta mik'e tace,
"sorry y'ar gidan Anni kije yayanku zai shirya ku,sanan kiyi wanka anjima ma zaku rakani unguwa."Salma tace,
"Anni irin wannan gurin da kikaje damu rannan,har aka bamu chocolate."Dariya tayi tace,
"shazumamu sarkin Shan zaki bacan ba,wani wajene kama hannun y'ar uwarki kuje ki taya ta shiryawa. "Kan ma salma ta iso wajenta ta fashe da kuka,
"ba zanje wajensu bah."
Ta ruga can cikin gidan Annin ta barsu sake da baki."Don irin hakan bai tab'a faruwa ba, Duk yadda suka b'ata da juna to kafin anjima sun shirya kansu, ko kuma wata sa, in Yah Aree ya shiryasu.
Salma tace kamar zatayi kuka, don idan sukai fad'an duk rud'ewa take ko kau itace aka kwara.
"Yah Kaga sweetheart ko."
Idonta ya cika da kwallah
Murmushi yayi ya d'an sunkuyo yace"kar kidamu my Angel, sweetheart dinki zata huce zo muje muci abinci."Anni tace,
"zan lallasar maki ita kinjiko salma yar albarka."
D'aga Kai tayi tana sake goge kwallarta,janta yayi suka fita, Annin ta wuce wajen Khairat d'in.💕💕💕💕💕💕💕💕
Wasa wasa Khairat ta k'i shirya wa da salma, haka Shima Areef d'in ta daina shige masa,tama koma gaba d'aya wajen Anni bacci ne kurun yake maido ta cikin gidansu, hakan ya saka salma cikin damuwa saboda tunda suka taso irin haka bata faruwa tsakaninsu.
shi kanshi Aree ya shiga damuwa ba kamar k'iriniyarta da tsalle tsallenta, da rigimar ta.Amman duk yadda yaso ya jawota jikinsa ta k'iya,don da ya tunkarota zata fashe da kuka,dole zai barta don subiyun baya son kukansu.
shahida ce ta sameta b'angaren Annin tace tazo Yah Aree yana kiranta,
Dole tataso suka taho shahidar nayi mata fad'an fushin da take da salma, wadda gata can bata da lafiya saboda taurin kanki Khairat.Cikin muryar kuka tace,
"da gaske kike Addah.""gata can ma tak'icin Abinci har yah Aree yayi yayi Amman ta k'icin komi. "
Aguje ta k'arasa cikin gidan falon farko ta same su,
Zube wa tayi gabanta tana kuka tace,
"sweetheart Miye haka, don kawai Ina fushi shine zaki wani sheme kina wani pretending,kinga ki tashi na huce bazan sake fushi da sweetheart d'ina ba,tashi kici kinjiko inhar baki son na cigaba da fushin."Kamar almarah haka suka ga salma ta Mike tana cin abincin,suna hirar su cike da so da kauna.
Areef wani sanyi yaji don ko kad'an baya son fushin ko wace cikinsu.
Cikin k'an k'anen lokaci komi ya daidai ta, saidai fah Khairat ta canza salo ta daina shigewa Areef, ko assignment ne ta k'asa yah mujahid shine zata je ya koya mata, ta daina rigima da salma akan Areef, ko k'iriniyarta da take masa ta daina Magana ma sai ta Kai makura take masa........gashi lokacin tafiyarsu ya taho don yanzu bai wuce 2 weeks masu zuwa.Amman gefe guda Khairat kullum cikin lissafin tafiyar take, duk kwanan duniya sai tayi kuka ahankali ta fara ramewa duk ta fice hayyacinta,haka akai jarabawa tashiga js3 aman saboda rashin maida hankali saida aka mata repiting......wannan dalilin ya jawo b'atawar *Khairat da Areef*
Taufah ana wata ga wata.
Mrs bb ce
Mom muhsen.

YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda