_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......6
Nasan da labarin tafiyar su Amman ko Anni ban nuna ma halin da zuciyata take ciki ba, tabbas inajin babu dad'i ba kamar jin danai wai salma zata yi masu rakiya har can, ita da Abbu da Dadyn meenah.
Wanda da sanda ana maganar tafiyar Abbu cewa yai hada ni za,a rakiyarsu shine yanzu don banyi k'ok'ari ba za,atai abarni basu san yanzu duk abunda zai had'ani da Yah Areef ba bana sonsa, ko sunyi mun tayin zuwa zance bana zuwa.
I think kun san yadda feeling d'in missing yake, Wanda da kaji wannan yana yin gara kayata rusa kuka, to haka Khairat takeji,duk yadda taso yin kukan abun yayi mata wuya saidai zafin da takeji cikin ranta, haka tak'i bari Anni ta fahimci komi akan tafiyar tasu,wanda hakan halin Khairat ne inhar bakaso gane abu ba is hardly ka fahimci yana yinta.
tana kwance kan gadon meenah wanda yanzu d'akin ya koma nasu su biyu,karatun English novels nake na soyayya, jin abud'e k'ofa yasa nayi saurin b'oyewa don yah mujahid ya hanani ni kuma sun shiga jikina bazan iya daina waba.
Ganin salma ce yasa nafiddo naci gaba daga Inda na tsaya, suna rage mun k'uncin da nake ciki,zama tayi kusa da ni ban kulata bah ganin kuma ba kulatan zanba yasa tace,"sweet............"
Katseta nayi da cewa,
"pls idan kinsan takura ce ki barni don Allah."Shiru salma tayi don iya wuya yau Khairat ta kai salma, wannan halin ko inkulan da take mata ya isa haka, ba ita takar zomon ba rataya aka bata.......cikin k'uluwa tace man.
"enough is enough *Khairat* haba ko ni nayi maki laifin iyakar horan da zakiyi mun kenan, Amman taya zan ringa binki kina mun wulakanci,to nagaji nagaji haka nan idan kin gadama Kizo yah Areef na kira."
Anni ce tashigo taga ficewar salma rai b'ace abunda zaka jima baka gani tare da ita ba, mutunce mai hakuri sosai Idan don ita zata jaka fad'a zaku shekara aru aru bakuyi bah, tabbas tasan Khairat ce ta tun zurota.
Cikin fad'a Anni ke tambayarta abunda ya had'asu, banji komi ba nayi mata bayani fad'a tashiga yimun tana cewa tunda banjin magana tafita harkata, gashinan naja wadda keta son ganin farinciki na tayi fushi dani, kuma intashi maza inje kiran kafin raina ya b'aci, muddin naci gaba da wannan halin zamu b'ata da ita sosai.
Ganin duk yadda ta tada hankali tana fad'a yasa na bata hakuri ashe k'ara kular da ita nayi,moper ta d'auko zata maka mun na tashi na rugo ina dariya, ban tsaya ko Ina ba sai falon su Yah mujahid shida yah Areef.
Kuka na samu salma nayi tana gaya masu,abunda ya faru, sai naji tabani tausayi matuk'a jiki babu kwari na shiga can gefe na zauna na gaida yah mujahid sannan Shima Nace masa,
"yah ina wuni."
Kallona yake bazan iya fassara shiba, kawai dai nasan kallon mai laifi yake mun kafin ya Kauda idonsa yace,
"haka zan tafi kuna fad'a da junan ku ko,na lura kin fara rainani *Khairat* sunan da ya anbata yasa babu shiri na kallesa, akai sa,a idonsa na kaina kallon Cikin ido mukai ma juna, sai naji ko kad'an banji dad'in sunan da yakira ni dashi bah, sadda kaina nayi naji kamar kwallah zata zubo mun,danne wa nayi daker ta tsaya.
Yace,
"kiba ta hakuri abunda kika mata, idan kuma kuka sake naji labarin kun sake b'atawa Allah takakkiya zan maku oya maza Kunshirya ina gani.""tabarshi kawai Yah bana so."
Cewar salma.B'ata fuska yayi.
yace,
"bana son taurin kai Kin sani salma ban sanki da haka ba, don haka karki fara kwai kwayon halayen da basuyi maki kyau kinji *my Angel*."Saida kirjina ya yi Wata irin bugawa na runtse idona kawai jinai ya dakan tsawa.
"zaki bata hakurin kokuwa sai na tattakaki awajen nan."
Yah mujahid yace,
"haba Areef Meyasa Kwanan nan kakoyi yiwa yarinyar nan tsawa ne,ehyi ba halinka bane kadaina."Bai kula saba jikina yana rawa kaina na k'asa Ina zubar da kwallah ba tare da Sunyi shawara dani bah,bakina yana rawa Amman na kasa furta komi........ Azafafe ya tashi ya d'auko dorinarsa jinai zau zau ga bayana..........k'ara na fasa inafashewa da kuka Yah mujahid ya anshe dorinar yana masa fad'a,kamar zai dakesa Shima Cikin zafin ran da bansan yana da shiba yace.
"wallahi muddin ba ta bata hakuri ba jikinta sai ya gaya mata, raini ya fara shigowa tsakani da ke ko, to mun k'ulla kenan nida ke daga yau wlh, zan saukar maki da wannan girman kan naki."
jikina rawa yake kamar mazari, sosai na tsorata da dukan sa yanzu kam tsoran sa yafara shiga ta tabbas,don babu abunda yake firgita ni kamar duka, ganin zai fizge ya yo kaina yasa na sake rushewa da kuka ina mamuk'e kujera.
Saida Yah mujahid yace,
"oya Khairat ba y'ar uwarki hakuri kinjiko ai ba fad'uwa kikai bah."Bawai inajin k'yashin bada hakurin bane taurin kai ne irin nawa, Amman ganin zai sake dukana yasa nace ina kuka.
"kiyi hakuri bazan sake bah."
Amman salma tai mun shiru jin haka yasa yace sai nayi ta bata har sai tayi magana.
saida na bata sau uku sannan tace tayi.
Zuwa lokacin fuskata tayi jajawur kamar tumatur, tashi nayi zan tafi ya fizgoni nayi wata irin fad'uwa saida yah mujahid ya tadani........saboda haushin abunda yayi fita yayi yabar falon.d'akin yayi shiru sai shashshekar kuka nakurum, da karar AC.
Ina jin sanda Ya ke Ajiyar zuciya kamar mai iska naji ya fara magana Cikin taushin murya,abun mamaki yabani yanzu fa yake kamar zai tashi sama saboda zuciya, Amman jibeshi kamar bashi bah.
"zan tafi na barku don haka kusan mekuke ciki, kar na sakejin wai kunyi fad'a,sanan maganar karatunku karkuga ban nan kuce zakuyi abunda kakeso, wallahi Ina biye da duk motsinku don haka amaida hankali a ajiye mun k'yak'k'yawan results,ke kuma da akama repiting sai ki maida hankali agaba kuna iya tafiya........salma ta fara mik'ewa sannan ni bazan Iya kwatanta yadda zuciyata ta keba, nasan dai ina cikin kunan zuciya da wani irin yanayi marar misltuwa,daker nakai k'ofar har salma ta wuce jinai yace,
"zonan"
Tsaye nayi na kasa juyowa kuma na kasa tafiya,saida ya dakan tsawa sannan jiki na rawa na isa gabansa na sadda kaina..........shiru tsawon lokaci baice komi ba, nima ban motsa ba, na sadda kaina kurun kwalla na zuba suna d'iga ga hijabina.
Jinai dai kawai ya d'ago fuskata nayi hanzarin rufe idona yayin da wasu kwallan suke zuba, handcif ya saka mai fitinennen k'amshi ya na goge mun kwallar.............amman wasu na sake silalowa bai daina gogewar ba har saida suka k'afe, sannan ya saki fuskar.
Yace Cikin muryarsa da tayi matukar sanyi,
"idan kika sake kukan nan ko bayan kin tafi d'aki nida kene swe.....Khairat."Fita nayi inajin k'afafuna kamar ba zasu iya d'aukata ba,
wannan ranar yadda naga rana haka naga dare, tun asuba akafara shirin tafiyarsu, inajin sadda salma tatashi nayi kamar bansan me take bah.......sai tara na tashi nafito wanka kenan Ina tsane jikina naji muryarsa yana tambayar meenah Ina nake, tace ina d'aki.........yana bud'e k'ofar ina shigewa toilet na da tse k'ofar...................
Mom muhsen ce
YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda