_*ABIN CIKIN RUHINA*_
*{RE-POST}* ©2019
Mrs bb
Mom muhseen.Watt pad name
Humaira7531🅿️.......21
Yau lecture biyu garemu sai pratical d'aya,shiyasa muka tashi da wuri.......husna da wata qawarta rahma suka rakoni bakin get muna tafe muna fira,rahma tace"kin san khairat DR MK fa yana ciki,don wallahi ydda nakejin labarinsa wajen wad'anda suka fita abu babu sauk'i,baida kirki ko kad'an kuma ga tsanani wajen test ko exam,amman abun mamakin shine yau da ya kama mu muna noise nai zaton walh korar mu zai sai naga baice mana komiba."
Jaki naja nace"shine kuma yace maki rahma inason khairat."
Husna dai dariya take ba tace komi ba,
"Ni bance yace haka ba,Amman kina dai gani yadda muke addabarsa da surutu class bacin ko ranar da yafara zuwa yayi mana kashedin cewar babu abunda yatsana sama da makara da noise,kuma duk wnda yshiga cse dashi yabani."
Girgiza kai nayi nacewa husna"wannan qawartaki bata da kan gado pls kina ringa kwatanta mata pls."
Me husna zatai ba dariya ba,rahma ranta ya b'aci rakiyar da batai ma kairat kenan ba.......munata dariyar tare nace"haba wlh kina fama da kwashe kwashen abokai marasa kan gado,shiyasa fa ni kinganni nan ban wata qawa data wuce ke,kema don naga kin zo daidai dani ne,inbacin iskanci ko ya akai tasan haka."
Husna na dariya tace"kika sani tashiga zuciyarsa ta gano."
Tsaki naja daidai munzo bakin get nace''ki koma yamma tayi sosai.......motar dake shigowace ta katseni.
Duk makarantar babu mai irin motar in bashi ba,motace ta gani ta fad'a kowa santinta yake school din.
D'auke kaina nayi nayiwa husna sallama na nufi fita,driver baizo ba kuma banzo da mota ba,daman yah jahid ne ya kawoni.......tracking nakeyi ina dub hanya kozan samu taxi,don hanyar ana wuyar abun hawa,duk yadda naso inje gida kan mangruba da alama hakan zai wuya........ban gama tunani naba motar nan tayi parking gabana.
Tsoro naji ni dafarko kafin ya sauke glass din tagar gefen shi.....
"Shigo mine in kika tsaya jiran taxi zakiyi dare."
Fuskarshi bbu alamun wasa ban iya musu da malamina ba shiyasa kurun nashiga,shima kuma don nasan yasan gidanmu nasan bazai cutar dani ba,don Abokin yah Areef ne sosai.
Shiga nai kurun ya cigaba da tafiya saida muka hau titi sosai yace"ina motar ne yau"
Ina danna wayata nace"banzo da itaba daman Yah jahid ne ya kawoni."
"Oky,Amman ya kamata abaki mota saboda irin haka,idan kuma Abbu yana ganin kinyi k'aranta yabarki ki dawo hostel inaga hakan zaifi,don irin haka akwai risk gaki mace."
Shiru nayi ina sauraren sa,hakika yana da zak'in murya sosai ga natsuwa komi cikin natsuwa yake har maganarsa.
"Nace insha Allah zan masa magana."
Daga haka bamu sake cewa komi ba har mukaje gida........ban yarda yashiga ciki ba nace yasaukeni nan ma bakin get is oky.
Fitowa nayi nace" thank u sir."
Gajeran smile yayi yace"ur welcome, kigaida Maah."
Nada"zataji."
Sauri sauri nake don kar wanda ya ganni nashige ina ajiyar zuciya,don bansan yazance ba idan aka ganni ya saukeni,duk da ansashi cikin gida hakan bazai hana su tabayeniba.B'angaren Annie na wuce in tajin dadin babu wanda na gamu dashi,yah meenah na ta gyara kayanta na wadrop tayi guga nashiga dakin,
" sannu dr kairat."
Murmushi nayi nace"me akayi da maza yah meenah kofa first semister bamu gama bah."
Kaya nahau cirewa tace"kamar gobene insha Allah."
"To Allah ya Nuna mana lokacin lafiya,bari nayi wanka inyi sallah zaki rakani wajen boss."
Dariya tayi tana tambayata waye boss,
Inacewa idan nafito zakiji.
Ban wani d'auki lokaci ba nafito shaf shaf nayi shafa nazura kaya,Allah yayini ba gwanar kwalliya bace,don ni sometimes ko powder bana sawa in zan fita school,amman i wonder nake ganin yadda wasu ke daukar heavy make up suna shiga school.......Saida na gaido Annie sannan nafita cikin gida wajen maah,Falo na sameta itada mai aiki suna hira,na zauna ina gaidata.
"Ashe kin dawo,ya test d'in."
Na yamutsa fuska"to da sauk'i dai kiyitayi man Addua kar nasamu fail,saboda wlh yau nayi ma lecturan laifi."
Fada tayi man kamar zata dakeni,har nai nadamar sanar da ita.
Hakuri nabata take cewa idan nayi wasa wallahi karatun zan aje ayiman aure.
Wata irin zabura nayi ina kallonta,nace"maah aure fa kikace me yakawo wannan maganar."
Sallamar mai aikin tayi tace idan zan kwanta in sameta d'akinta,nace to kurun tatashi tabar falon.Abbu bainan shiyasa banma je inda yake ba,maganarta tayi man tsaye ga makoshi "Aure,ni za,awa auren,tabdijam."
Tashi nayi nawuce d'akinmu salma bata nan nasan tanacan ta kasa ta tsare.
Tsaki naja nace"Allah yarabani da wanan wahalallar soyayyar."
Kaya na fara had'awa cikin trolley,tun kan in tabbatar da anyarje man ko akasin haka harna hada kayana,inaba zuciyata tabbacin ai yama yarda yagama,saida na had'a akwati uku harda jakunkuna takalma dadai sauran abunda zan buk'ata.Nafito na wuce wajen yah meenah nace tataso muje,tayi dani inzo muci abinci nace sai mundawo banda natsuwa harsai na samu abunda nakeso.
Fita mukai Annie nacewa Allah yabada sa,a muna dariya mukace ameen.
Tunda muka doshi b'angaren nasu zuciyata take bugawa kamar zata fito waje,na rik'e hannun yah meenah gagam har tana cewa"zaki karyani fah."
Banmasan nayi ba bansan dalilin dayasa nake masifar tsoran saba,nidai banson had'uwa dashi harcikin zuciyata kuma haka yake,nidai yanzu ko kad'an banajin wani sonsa saboda yariga ya koya man tsoransa ya cireman duk wani feelings akanshi,amman ina mamakin abunda naji shekaranjiya........wanda har yau inajin abun idan natuna da ranar......tura k'ofar falon yah meenah tayi nayi saurin b'oyewa natoge nakasa shiga,da alamun suduka suna nan,inajinma harda salma jinai yah jahid yace"waye nan."
Yah meenah tace"yah mune."
"To kushigo mana kuke lab'ewa."
Jana take ina togewa don har jikina ya fara rawa,saboda tsananin tsoro........dole tashige tabarni ina rawar sanyi.
"Ina kairat d'in."
Cewar yah jahid
"Gata can bakin k'ofa ta k'i shigowa."
Murmushi yayi ya kalli Areef dake kwance kan three seater yalumshe idonshi,ga salma zaune gabanshi da alama fad'a sukai.
Muryarsa yadaga yace"kishigo my dear bacci ma dodon naki yake."
Aikuwa nai zuf nashiga na rakub'e bakin kujerar farko ta wajen k'ofa.
Duk nai tsuru tsuru me zasuyi ba dariya ba,har salma dariya take can kasa kasa.......hawaye suka silaloman natashi nayi hanyar fita naji muryarsa irin ta marasa lafiya yace"zo nan."
Kasa fitar nayi najuyo ya kalli yah meenah yace"kubarnan."
Kankace me taruga salma tatsaya nuk'u nuk'u yadallah mata harara sannan tatashi tafita,yah jahid yaketa jana nakasa biye mashi don jina nake kamar saman gajimare ina lilo.
Lumshe idonsa yayi bai sake kulani ba,saida naji zaman ya isheni nace"yah."
Jahid murmushi kurun yake yanason wannan dramer tasu,
Jin yaki ansawa nasake cewa" *YAH AREEEF*"
Tsintar kwayar idonsa nayi cikin tawa,sai bakina yayi nauyi na kasa cigaba da maganar.........sadda kaina nayi ina sharar kwallah,nidai narasa gane kaina,dan danan idan ina gabanshi sai kuka.........."idan kuka zakiyi man get out."
Jinai kukan ya kucceman nadunkule waje guda kaina cikin guyawuna,yi kawai nake ina sauke ajiyar zuciya.
Yah jahid da tasowa yayi zai lallasheta sai yayi wani tunani kurun sai yafita yabarsu.
Tashi yayi zaune yanajin kanshi yana tsananta ciwo,daker ya fizgo maganar yace"zonan."
Kasa motsawa nayi jikina rawa kurun yake kamar anjonaman wuta......dafe kanshi yayi da duk hannunsa,cikin tsawar dabaisan ma zai iyayintaba tace"I said come here."
Ina makerketa na isa wajenshi,rawa kurun jikina keyi hawaye kau kamar anbude famfo.......hannunsa yasa guda d'aya ya rikoni yana kallona da jajayen idonsa dasuka rine.
"Menene,mekike so."
Muryata na rawa ina shashsheka nace"dama........dam.....a..cewa za......nyi.......ka....barni na koma hostel."
Tsaki yaja kafin ya saki hannuna yace"is that All"
D'aga kai kurun nayi yace"waye ya kawoki d'azun."
Ai jinai fitsari zai kucceman girgiza kai nayi inaja baya.....fincikoni yayi ya zaunar yana kallona "I said waye yayi dropping naki d'azun."
Fashewa zanyi da kuka ya tashi ya shiga d'aki belt ya d'auko yace"answer my question."
Saboda tsananin firgitar danake ciki yasa bansan sadda idona yayi looooooo nazube k'asa bah...........Love u All my fans
Mom muhseen✍🏻

YOU ARE READING
ABIN CIKIN RUHINA
Fanfictionlabarin soyayyar khairat da yayanta wanda ta daukesa matsayin yayanta ciki guda