💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY: HAERMERBRAERH
MUTANEN KWARAI MASU ALBARKA GA EDITING DIN TSOFAFFIN NOVELS DINA NAN ZAN DINGA KAWO MAKU A HANKALI HAR NA KAMMALA, DAGA NAN SAI MU FAD'A SABO DA YARDAR ALLAH...A KARANTA DA HANKURI.....😆
Page 1:
"Eamaan kin san ba wadda na ke so a fad'in duniyar nan da aure in ba ke ba, kema kuma na sani duk samarin da Allah ya azurta ki da su ba wanda kike so kike kulawa sai ni, to mai zai sa ki bari a raba mu?ki sani in bake ba zan iya rayuwa me dad'i ba, ba macen da zata zama madadin ki a waje na"
Cike da qunar rai Anwar ke magana ya na kallon Eamaan da ke tsiyayar da hawaye saboda baqin cikin rabuwa da babban masoyin ta,a hankali cikin natsuwa ta bud'e baki ta ce ,
" Anwar kai ma ka san maganar iyaye tana sama da ta kowa ko? ba zai yu iyayena su ce ga abinda zan aikata ba ni kuma saboda son zuciya ta na qi aikata abinda suka umarce ni akai ba, kai ne kullum kake fada min yanda zan qara kyautata tsakanin mu'amalata dasu, me yasa yanzu kake son canjawa? ina kallon yanda kake yi ma iyayen ka biyayya,na tabbata da kai ne suka umarce ka da ka rabu da ni zakai hakan, me yasa ka me so ni na qi bin umarnin iyaye na? Ina zaton mun wuce wannan lokacin dani da kai, ka riga da ka sani kai nake so, duk duniya ma ta san hakan, kuma ba zan sake son kowa ba,na gama so a rayuwa ta, na gama mallaka maka soyayya ta, ba abinda yayi saura a rayuwa ta na soyayya da zan iya yi wa wani namijin, fatana kawai Allah yasa yanda nai karatun nan kar su tauye ni wajen yin aiki, domin yana ɗaya daga burina na rayuwa anan gaba,"
Eamaan ta qarasa zancenta tana share hawayen dake zuba mata masu zafi a fuskar ta, kallon ta Anwar yayi da girmama wa, sannan yayi mata fatan alkairi ya tafi, kuka suke sosai gaba ɗayan su, a haka ta shiga gidan ta faɗa gadon ta madaidaici da yake kusa da gadon yayar ta Hafsat, gaba ɗaya rayuwar gidan su take tinani, anya ba a qwarar su ita da mahaifiyar ta kuwa? sun taso suna masu son junan su tin yarinta ita da Anwar domin kuwa maqota ne su, iyayen su abokan juna ne, mahaifin Eamaan cikakken dan boko ne, mai ra'ayin kan shi, ba wanda ya isa ko da shawara a canja mai abinda yaso aikatawa, matan shi biyu,Kareema ita ce babba yaran ta biyu mata sun aurar da babbar mai suna Fa'iza,a nan cikin garin kano ga wani hamshaqin dan siyasa, sai ta biyun wato Hafsat ita kuma tana ci gaba da karatun ta a bangaren Law, Eaman d'iyar khadija ce,itace matar Alhaji Muhammad Kabeer ta biyu,mace ce mai biyayyar aure,halayyar su ta sha banban da uwar gidan ta dan kuwa ita Kareema bata yarda a na bata umarni ba sam, sai dai in ma za a bata umarnin to fa ya zama ba zai takura ta da yaran ta ba, saba'nin Khadeeja wadda ko me za a ce tayi indai bai zama haramun ba ko zai tauye haqqin ta da na d'iyar ta tilo to fa zata yarda.
Hakane ke shirin faruwa yanzun ma a gidan na su Eamaan ,domin kuwa duk dad'ewar Anwar da Eamaan a soyayyan gashi Daddyn ta na neman raba su, sakamakon wani ra'ayin shi na son zuciya, domin kuwa wanda yake son bawa Eamaan sa'an shi ne mai shekaru kusan 55, a duniya, ita kuma ba zata wuce shekara 24 ba, a cikin wannan shekarar ta gama school of nursing ta fita a matsayin midwife, ba qaramin son aikin take yi ba, tayi wannan karatun ne dan taimakawa mata 'yan uwan ta, bata son taji labarin maza ko arna ke karb'ar haihuwa a asibiti,ranta na matuqar baci da hakan, tin a shekarar da zata gama secondary school suka yanke shawara ita da qawar ta A'ishaa zasu yi karatu a b'angaren ungozomanci, sai gashi Allah ya cika masu burin su, ita A'ishaa har ta fara aiki a wani asibiti mai zaman kan shi a unguwar da ta yi aure, kuma da taimakon mijin ta hakan ya samu, Eamaan ta taya ta murna sosai, itama taiwa kan ta fatan samun hakan, amma da dikkan alamu ba zai samu ba, na farko dai mijin da zata aura ba yaro bane, da gani zai yi ra'ayi irin na mahaifin ta, na biyu kuma dan siyasa ne shima, tasan kuwa da wahala ya barta zuwa aiki, ajiyar zuciya ta yi ta kalli sama
" Allah gare ka nake neman zaɓin alkairi ba son zuciya ta ba, na sani duk abinda ka zab'a min dai-dai ne, aslamtu nafsi ilaika ya rahman,"
Hawaye ne masu zafi ke gangara ta gefen idon ta, shigowa aka yi dakin sai tai saurin goge su ta zauna, tare da sakin murmushin yaqe
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.