BIYAYYAH PAGE 12

48 6 1
                                    

💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼



WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



Page 12:

Gaba ɗaya hankalin Alhaji ya kasa kwanciya da matan nashi da ya kamata ace a wajen su ya sauka, dan haka a  wajen Eamaan ya kwana ranar ,dik da cewa Iya tayi-tayi dashi ya tafi gida ya huta amma qi, baya son ya tafi ya bar ta a nan daga ita se Iya dan a ganin shi akwai abinda dole shi zai yi mata Iya baza ta iya ba.

Har suka yi kwana uku a asibitin babu wanda yazo duba Eamaan ding a cikin mutanen gidan Alhajin kama daga kan Hajiya Babba har zuwa Hajiya Qaramar balle kuma Sahabee dake a cikin damuwa, qarshe dai dole Alhaji ya yi waya gidan su Eamaan ya Sanar da su halin da Eamaan ke ciki, Hafsat aka umarta data zo ta zauna da ita har ta samu k'warin jikin ta tinda ita ta yi graduating yanzu haka tana aiki a camber din ta na kanta ne, sannan an kawo kuɗin auren ta har an saka ranar auren da wani abokin aikin ta mai suna Kamal, Iya da cewa ta yi a bar ta ba sai tazo ba tinda ga masu aikin gidan cikin su an samu mai zuwa ta zauna da ita, amma Eamaan ta ce a mata alfarmar barin yayar ta tazo wajen ta in zai samu, kan Iya tace komai Alhaji yace ba komai zai je da kan shi ya d'akko mata Hafsar,ita kanta Hafsar ta ji dad'in hakan dan tana son baiwa wa qanwar ta ta kulawa ta musamman.

Ammaah da Mama sun tausaya ma Eamaan dan sun tabbatar aiki take shaqa har hakan ta faru da ita, amma babu yanda za suyi da ya wuce suyi mata addu'ar samun sassauci,dama kowacce mace da qaddarar gidan auren ta,Daddy ma ranshi ya baci da jin cewa wai zata yi b'ari saboda yawan aiki da stress amma sai ya danne saboda baya son ya karya wa d'iyar shi mai BIYAYYAH qwarin guiwar ci gaba da yin BIYAYYAH a gidan mijin ta, sai kawai ya bi ta da addu'a da fatan alkhairi shima.

Wani irin haɗin kai ne yake wanzuwa a tsakanin matan na Alhaji da Sahabee wanda kai da ka gani kasan ba na Allah da Annabi bane akwai wata a qasa,dan kuwa kowa na nan na jin haushin 'yar uwar ta a qasan ran ta.

Tin bayan da aka kwantar da Eamaan sukan haɗu a sashen junan su suyi ta tattaunawa akan matsalar da suke ganin tana tunkaro su a gidan, dan haka yau ma zaune suke a sashen Hajiya Babba suna hira, cike da b'acin rai Hajiyan ta nisa tace,

" Hmmm wai baku san cewar an tabbatar da Eamaan na ɗauke da cikin watanni 3 zuwa 4 ba? Meye plan din mu akan hakan ne dan dai gaba d'ayan mu yanzu mu masu laifi ne a wajen Alhaji da ya san me muke aikatawa a bayan idanun shi kashin mu ya bushe,  Qarama kin dai san baki da gadon yaran nan a gidannan dan ko in Alhaji ya fad'i ya mutu ni ko Sahabee ba bari zamu yi a raba da shegu ba tin da mun san komai,"

Wani mugun kallo Hajiya Qarama tai wa Hajiya Babba, sannan tace,

" Yo me zamu yi banda mu qoqarta zubda cikin tin kan yazo duniya? Ko dake na kula ku tsoron ta kuke ji har yanzu,"

Sahabee ne yayi mata kallon baki da hankali,

" ke kan ki tsoron ta kike yi balle mu,akan me ba zamu ji tsoron mace kamar Eamaan ba, macen da ta san me take yi, tasan ta kan tafi da abokin gaba ba tare da tada jijiyoyin wuya ba ko hargowa,tasan yanda zata saka duk wani wanda basa shiri da ita cikin fargaba da tashin hankali, dan haka ni ina ganin kar wadda ta yi yunqurin taba abinda ke cikin ta,koma dai menene Yayah dan uwana ne, dan haka zan so ace yau ko da d'a d'aya ne ya ga jinin shi shima a duniya ,dan haka ku kiyaye kar na ji labarin wani abu ya sami cikin nan,"

shiru suka yi, kowacce da abinda take saqawa,Hajiya Qarama ce ta buɗe baki tayi magana cikin fargaba da tsoro tace,

"Ni yanzu ku ban shawara dan Allah, ya zan yi na sanar da Alhaji Saminu ina ɗauke da yaran shi guda biyu ba tare da ya qi karb'ar su ba?"

" Kar kiji tsoron komai ki sanar da shi komai a wannan dawowar da zai yi in ya sani shikenan fargabar ki ta qare,idan yaso kina faɗa masa ki bashi sharuda biyu, na farko dai ko ya Karb'a cewa yara nashi ne ko ki masa barazanar tona maku asiri, ki nuna mai ke baki damu ba dan wani ya sani shi kike jiyewa,"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now