BIYAYYAH PAGE 5

36 5 1
                                    

💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼







   

   RUBUTAWA:HAERMEEBRAERH







Page 5:





"A'udhubillahi minasshaid'anirrajeem,waye kai? Meye haka zaka shigo ba ko sallama, ko an faɗa maka nan ɗin gidan arna ne, dalla malami fita daga nan,Kuma  koma waye kai baka da d'a'a, FITA MANA NACE NA SUTURCE JIKI NA"

Da fari Ido ya zuba mata ya na Jin sautin muryar ta kamar busar sarewa a kunnuwan shi,tinda yake tsalle-tsallen shi daga gida Nigeria har waje be tab'a gamo da mace kamar Eamaan ba, a zaton shi ko baquwa amaryar sashen ta yi kyakkyawa haka, dan be tab'a ganin makamanciyar shigar qananan kaya a jikin kowacce mace a gidan ba sai yau,tsawar ta ta qarshe ce ta bashi tsoro ya dawo cikin hayyacin shi,kallon idanun ta ya yi ya tabbatar da wannan fuskar ba alamar wasa a cikin ta, fita ya yi salalo-salalo da dogon wuya ya koma bangaren Iya,yana shiga ya zauna dabar yana dogon nazari, Iya kuwa bin shi kawai ta yi da ido, tinani ya hau yi shin wai wannan 'yar yarinyar ce ta daka mai tsawa kuma ya bi umarnin ta kamar Wani soko? Lallai sai ya koya mata hankali ko ita wacece, sai ya nuna mata bariki fa sune iyayen ta, dan ta yi shigar 'yan bariki take zaton ita wata ce? Lallai rashin sani ya fi dare duhu in ji bahaushe, kwafa ya yi ya janyo jug ɗin da ke cike da juice ya tsiyaya ya sha,wani gard'i ne ya buge masa kunne sai ya d'aga glass cup ɗin yana kallo, duk abinda yake Iya na kallon shi sai kawai tayi murmushi tace,

" Labartan abinda ya faru daga fitar ka zuwa dawowar ka yanzu,"

kwafa ya sake yi a karo na ba adadi tin shigar shi parlourn sannan ya zayyana mata haɗuwar shi da budurwar sashen amarya, ya qara da cewa,

"Har ni zata kora da kakkausar murya, wai  na bar mata waje ta suturce jikin ta? Ni wanne kalar jiki ne ban gani ba kuma ban taɓa ba,daga na turawa har larabawa zuwa baqaqen fata namu na nan,ni zata faɗawa jikin ta?"

"Dole ta faɗa maka jikin ta mana d'anneman lalatacce( ita take lalata shi kenan tin da ga sunan da ta faɗa masa wai lalatacce)kai da ko kunyar faɗin kai mazinaci ne ba ka yi, a gabana kakr faɗan wacce kalar mace ce baka taɓa ba ko?,saboda ka gawurta, na rasa me yake damun ku Kai da d'an uwan ka, kamar Waɗanda na tsugunna na haife su a gidan magajiya,mtsss maza d'auki abinci kaci soko kawai,Kuma ka sani wannan yarinyar da ka ke magana akai matar Yayan ka ce,dan haka ka kula"

Tashi ta yi ta na ta surutai har ta shige d'akin ta.

Abincin shi ya ɗauka ya na ci siffar Eamaan da surar jikin ta da ya gani a kashingid'e a kujera nayi masa yawo a kwanya da zuciyar shi, ba wai tsananin kyau ne da ita ba, ah ah kyau ne wanda yake da ɗaukar hankali, sura ce da ita ta daban me ban mamaki ,da tinanin ta ya kammala cin abincin shi da yake Jin dad'in shi har tsakiyar Kan shi.

Eamaan kuwa bayan fitar shi ne ta tashi ta sako doguwar riga akan kayan,ta yafa dankwalin rigar ta d'akko wayar ta ta duba lokaci ta ga lokacin da ta saba yin Chatting da qawar ta ne saboda yanayin aikin ta bata so tana shiga lokacin aikin ta tafi so sai ta tashi daga aiki su sha hirar su a nutse,cikin sa'a kuwa ta ga Aishan online sai kawai suka hau hira.

Eamaan :'Assalamu alaikum Babe y kk'

Aisha :'Gud..sarkin qa'ida tin dazu nake jiran ki hawo online mu sha hira sai in ga time din hawan ki be ba, ni ki na bani mamaki fa sosai Eamaan, a wannan zamanin wa ya damu da wani amfani da lokaci irin haka? Ko ni da nake aikin ma na ce miki ki dinga hawa online zaki same ni a kowanne lokaci amma se ki qi kice sai na taso aiki,',

Eamaan : 'Hmmmm Ayshaa kenan, kiyaye lokaci kuwa na da matuqar mahimmanci a wajen d'an Adam, a kalla ko ba ka zama me tsananin kula da lokaci ba ka zama ka San me ka yi da lokacin ka, kar ya zo ya wuce a banza baka mora ba ba a more ka ba, sannan in bama kula da shi sai ajalin mu ya riske mu bamu tab'uka komai ba, bamu Samar wa kammu mazauni me kyau ba a aljannah,ke ni raina ne ma a b'ace'

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now