💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 18:
Umartar ta ya yi da ta bishi office din shi yana son magana da ita, suna isa ya mata nuni da wajen zama, ta zauna hankalin ta gaba daya a tashe yake, kallon shi take ko qiftawa bata yi, gyaran murya ya yi yace,
" Hajiya a gaskiya Alhaji yana cikin matsala sosai, domin kuwa ada mun samu ci gaba sosai, yanzu komai ya koma mana baya, na sha fada maki kuna qoqarta kauda shi daga abinda zai b'ata ran shi, amma yanzu ki duba ki gani yanda gaba d'aya komai ya koma mana baya, a gaskiya banji dad'i ba sam, kuma a yanzu kam sai dai na baku shawarar akan ku fidda shi waje, domin a samu ya samu sauqi da wuri, in ba haka ba a gaskiya ina jiye maku tsoro sosai,"
kukan ta ne ya qaru sosai, a hankali ta share hawayen ta ta yi masa godiya sannan ta fita, direct gidan su ta tafi, ta je ta samu Iya da Sahabee a palour suna tattauna wa akan Eamaan, yana qara fada mata qarya da gaskiya akan abinda ya faru, Sallama yi ta musu ta shiga, a tare suka daga kai suka kalle ta, Sahabee kuwa a matuqar razane ya kalle ta, Iya ta kula da hakan nan take ranta ya qara ɓaci, wato har Eamaan na da wannan effect din akan d'an nata
" Meya kawo ki nan kuma?"
Kallon Iyan ta yi da tsantsar tsana tace,
"A da na zaci zan kyautata maki har Allah ya ganar da ke ki so ni, na jure duk qunci da wahalar ki, na kasance ban taba kwana da abinda kika yi min a raina ba,a lokacin da kika batamin rai a lokacin nake mantawa kuma na yafe maki, dan haka yanzu ina son gaya maki ni ban riqe ki da komai ba na yafe maki dik abinda kika yi min ko da baki nemi yafiyata ba, amma ku sani wannann gidan akwai mai shi, kuma mai shi d'in nada buqatar gidan shi, kamar yanda baku damu da shi da lfiyar shi ba haka nima ba zan damu wajen sanar daku daga yau zuwa ko wanne lokaci gidannan da abinda ke cikin shi zai zama mallakin wani ba, ruwan ku ne ku samu wani wajen fakewar kuma ruwan ku ne ku zauna har masu siyan gidan su zo su fidda ku,"
Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice, gaba d'ayan su baki suka buɗe suna kallon ta har ta b'ace wa ganin su,nan take wani irin fargaba da tsoro suka shige su yanzu ina za su je? lallai lamarin Eamaan a bin tsoro da firgitarwa ne, to yanzu ya zasu yi?shin me ma ya sake samun d'an nata, sai a yanzu wannann tinanin ya zo mata,cikin hanzari kuwa ta yinqura ta tashi tana dingisa qafar ta da ta ke ciwo zata fita,Sahabee ne ya kalle ta yace,
" Iya ina zaki je kuma bayan ta gama fad'a mana saqon rashin mutuncin data ga dama ta tafi?"
"Kai da Allah ja can, daga dikkan alama Audu bai da lafiya sosai, shine dalilin da yasa za ta saida gidan a yi masa magani da kud'in ,ko kuma so take yi ta cinye kud'in gidan dan taga bai da lafiya bai san ina kan shi yake ba,"
Tana fita ta tarar da Eamaan da wasu mutane tsaye suna magana har da drivern Alhaji,shi kan shi drivern haushin su Iya ya ke ji, yana ganin Iyar ya d'auke kai gefe ya haɗe rai sosai, buɗe sauran bangaren su Hajiya Babba da Qarama su Eamaan ke yi, komai na nan kamar yanda suka bar shi, sai da suka bud'e ne ma suka ga akwai sarqoqi da wasu abubuwan masu amfani har da kuɗi a sashen Hajiya Qarama, d'iba Eamaan ta yi ta damqa a hannun drivern tace yaje ya siyar ya dawo, duk da ta San ta yi a kasada amma gwanda shi ya nuna damuwar shi akan mijin ta sama da mahaifiyar shi da ɗan uwan shi da ya wahaltawa a rayuwa.
Masu siyan gidan sun shiga ko ina sun gani, gida yayi musu fiye ma da yanda suke so kuma yayi musu za su siya, sun tsaida magana akan za su fara bayarda rabin kud'in zuwa wata uku masu zuwa su cike sauran,Eamaan kuwa ta yi na'am da hakan, dan haka Kiran lauyan Alhaji ta yi aka yi komai a gaban shi.
Driver kuwa direct wajen saida gwala-gwalai ya nufa ya siyar ya dawo mata da kud'ad'en ta cass ko sisi bai rage ba,ko da ta duba sai taga ta samu kimanin million biyu da rabi, nan take ta wari dubu d'ari ta baiwa driver, qin karb'a ya yi ya na hawaye yace mata a qara a maganin Alhaji baida komai da zai taimaka da shi dan haka ba zai karb'i ko sisi ba,cikin kukan tausayin su ta yi masa godiya amma ta bashi 20k ta matsa masa dole ya karba.
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.