💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 21:
Anwar ne zaune a kujera a parlour yana hutawa,tunani yake yi mai zurfi kafin daga baya ya d'akko wayar shi da ke saman qaramin table ya hau danna digits d'in abokin shi, ringing biyu tayi ya ɗauka , cikin shaqiyanci irin na abokai ya ke tsokanar Anwar,
" Yahhhh ustaz ya ne....Ya Bauchin kuma? ina fatan dai by now Ustaz ya samo mana ustaziya acan da zamu sha biki, kasan fa 'yan bauchi ustazai ne."
"To kanya sarkin zuba, ai kama jira in amsa maka gaisuwar taka ko? dama na kira ka ne akan labarin da ka bani game da Eamaan kwanaki ,tin da ka fada min nake ta tunanin anya gaskiya ne kuwa?"
" Man da gaske ne mana, yanzu haka tana garin Bauchi a gidan yayar ta Hafsat,saboda jiya an wangale gate d'in gidan na hango ta tana ta kuka tana masifa ma wani Alhaji, ina nan zaune ina mamaki akan abinda na gani, saboda gaba ɗaya Eamaan ta sauya akan yanda muka santa,na kai minti biyar a wajen bayan Alhajin nan ya tafi,dake qofar buɗe aka barta shi ya bani damar ganin ana saka musu kaya a bayan mota,ana gama loda kayan ne suka yi sallama da mutanen gida suka shige mota driver ya ja suka bar gidan, tafiyar su da mintuna na zauna a qofar gidan su,to dake ka san baba me gadi mutumin mu ne, a wajen shi nake samun labarin dik abinda na fad'a Maka kwanaki har ya min qarin bayanin ai jihar Bauchi suka nufa zata je Bauchin gidan Hafsat dan ta huta da hayaniyar da keta faruwa."
Ajiyar zuciya Anwar yayi cikin zuciyar shi yace,
'Lallai wannan babbar dama ce a gare ni ta dawo da soyayya ta sabuwa dal a zuciyar Eamaan.'
Abokin shi ne yace,
"Man yaa dai na ji ka yi shiru? Lafiya dai ko?"
"Lafiya qalaou kayi min qoqari na gode sosai Allah ya qara mana zumunci, sai mun yi waya, Assalamu alaikum,"
Sallamar abokin na shi ya amsa suka kashe wayar, murmushi ne kwance a fuskar shi, da kuma addu'ar da ta zama sirrin shi,domin kuwa dik tsawon waɗannan shekarun bai taɓa mantawa da ita ba, soyayyar ta kuma bata taɓa gushewa daga zuciyar shi ba.
Girki take a kitchen su kuma suna zaune a plour da Fatee sai sa su dariya take yi, Kamal ne yace da dan qarfi yanda Eamaan dake kitchen zata iya jiyo shi,
" Eamaan ko zaki d'akko takardun ki ne a nema maki aiki ki fara, nema maki aiki ba zai min wuya ba in Allah ya yarda, akwai Wani cousin d'ina da ya bud'e Wani asibiti ko anan se na nema maki,zuwa aikin shima zai taimaka maki wajen rage maki kad'aici ko baby?"
"Kwarai da gaske wannan m shawara ce mai kyau."
Inji Hafsat,Eamaan kuwa sai da ta kammala abunda take yi,sannan ta dakko abincin ta fito parlour ta same su, kunun acca ne Hafsat ke so ta yi mata da alala, da rana su kuma tayi masu rice and stew da salad da pepper meat mai cike da veges a ciki,gefe ɗaya kuma Apple drink ta hada masu domin tafi son haɗin gida akan lemon kwali ko na roba,a tsakiyar su ta aje sai kowa ya ja plate suka fara ci,bin ta ya yi da kallo, dan har lokacin bata bashi amsa ba,a hankali ta furta,
" Yayah ka d'an bari ba yan zu ba, sai naje gidan Yayah Babba na gama mata hutun ta na dawo, saboda kaga ba lallai bane na ci gaba da zama anan dindindin, wataqila zan koma kano,"
kallon ta ya yi da harar wasa sannan yace,
" kina nufin ba zaki zauna a wajen mu ba har Allah yasa ki samu d'an bauchi ki aura kin ga shikenan Hafsat ta samu 'yar uwa a kusa."
murmushi suka yi,
"Ohhhh ashe son kai ne abuunn, shi yasa ake son na samu aiki a bauchi ko, to naqi wayon kano ma Mama da Amma na jirana,sannan Hafsat bata da Wani dangi da ya wuce Kai da 'yan uwan ka, mu haka aka koyar da mu a gidan mu, dangin mijin mu su ma 'yan uwammu ne in bamu d'auke su 'yan uwa ba wahala zaman zai yi mana Ina fatan ka gane"
![](https://img.wattpad.com/cover/332311715-288-k451043.jpg)
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.