BIYAYYAH PAGE 8

73 7 3
                                        

💅🏼  BIYAYYAH   💅🏼







WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH







Page 8:



Qafa ta saka masa ya kife a qasa, cikin zafin nama ya yunqura zai tashi ta fesa masa turaren  da ta d'akko a fuskar shi, sannan ta sa bayan hannunta ta buga masa a baya, gwangwanin turaren ta d'aga sama ta kwad'a masa a kafad'a da qarfi, yana son ya yi ihu dan azabar da yake sha hannun Eamaan amma babu dama,saboda baya son asirin shi ya tonu, da lalibe ta kunna fitilar d'akin,Sahabee ya bayyana duqe a gaban ta, haɗe hannayen shi d'aya cikin d'aya yayi yana zubda hawaye a idanun shi ya hau bata hakuri, mamakin ganin wai Sahabee ne ashe ya ke wannan iskancin a cikin wannan daren me ya zo yi to a d'akin nata Sata Ko fyad'e?

Sahabee ya gama cika mata ciki wannan karon dan haka haushin shi take bala'in ji, ta tabbata ba shi da cikakkiyar tarbiyya ko kaɗan, d'aga hannunta ta yi da nufin yin magana sai dai kalma d'aya ta kasa fita daga bakin ta,takaicin shi ya tokare mata kowacce kafa da amon sauti zai fita a wuyan ta,cije leb'en ta na qasa ta yi cike da takaici,yawo ta fara yi a d'akin ta kai ta dawo ta Kai ta dawo a gaban shi,qoqarin tashi ya yi zai gudu,Eamaan na ganin haka kuwa ta yunqura itama cike da wani irin zafin nama da bata san ta na da shi bama ta fizge shi ya yi baya, hannunta ta d'aga ta wanke shi da Mari sannan tace masa,

"Guduwa za ka yi? Ai ba inda zaka je se ka Sanar da ni me ya kawo ka sashe na a wannan Daren har da kashe min fitila, kashe ni za ka yi ko me?"

Sahabee ya tabbata in ya Sanar da ita gaskiyar abinda ya je yi a sashen ta har maganar ta Kai wajen Yayan shi kashin shi ya bushe,ya san dikkan wasu sirrikan shi manya da qanana za su bayyana, dan haka cikin kuka irin na 'yan bariki ya zube a gaban Eamaan ya na bata hakuri, tare da fad'in  tsautsayi ne ya kawo shi,amma ba shi da wani qudiri mummuna a ran shi.

Yanda yake bata hakuri ya fara karyar da zuciyarta ta yarda ba shi da wata manufa da ya je, dan haka cikin dakewa ta ce Masa

"Zan rufa maka asiri dan kuwa wannan abun kunya ne ace wai qanin miji na ke bibiya ta,sannan dan rashin lafiyar Iya bazan so maganar nan ta fita ba,sannan ba zan so b'ata zumuntar dake tsakanin ka da ɗan uwan ka ba, amma ka sani duk sanda ganganci ya sa ka qara kallona ka bari muka haɗa ido da kai a cikin gidannan ma, Hmmmmm,"

Wata dariyar da ta matuqar tsorata shi Eamaan ta saki, dariyar da ya kasa gane ma'anar ta,wai yau shi da yake bariki me lasisi a qasar masu kwale shi ake yiwa haka,shi ɗin uban bariki reshe ya juye da mujiya.

A yau ya gane ashe barikin ma suna ta tara, lallai yau ya tabbatar da cewa mace sai ta so duk wani iskanci zai wakana tsakanin ta da namiji,murmushi kaɗai ya isa ya ja ragamar afkawa zina balle har a kai ga yin magana da juna.

Yau ya gane cewar ashe ba kowacce mace bace yar iska,Sahabee kuka yake yi sosai na baqin cikin ganin shi qasqance gaban yarinya qarama kamar Eamaan ta na yanka masa gargad'i bayan ya yi masa duka,qasan ran shi kuma yana kukan takaicin rasa babbar damar kashe qishin ruwan shi akan Eamaan, gefen idon shi ya yi jawur inda turaren yayi nasarar shiga ciki, umartar shi ta yi daya fice maya daga waje kafin ta sake sanya masa turaren a idanun shi,ai kuwa da gudu-gudu ya miqe zai fice daga sashen nata, Eamaan ta daka masa tsawa ya dakata tace,

"Wannann jakar taka da takalmin ka d'aya da ka bar min anan uban wa zai ɗaukar maka,"

"Bbbaaaabaaa kowwaaa, niiii zannnn d'auuuke abu na"

Wurga masa ta yi ya ɗebe su da hanzari ita Kuma  ta danna qofar ta rufe da makulli, kuka ta zauna a wajen tana yi sosai,zuciyarta ta yi mata kunci, wannan shine babban misalin in kayi zina da 'yar wani ko matar wani ko qanwar wani ko mahaifiyar wani kaima za a yi da naka,ficewar motar Alhaji da taji ne ya sanya ta je ta dakko Ice cream ta sha ko ranta zai yi sanyi amma ina bata samu abinda take so ba, nan take taje ta dauki qur'aninta ta fara karantawa ko zai ɗauke mata damuwar dake ran ta, ta fara kenan ta ji shigowar mutum ashe qanin mijin ta ne,ajiyar zuciya ta yi ta goge hancin ta dake d'igar da hawaye da majina,ta tabbata Alhajin na su sai gobe a ganshi tinda ya tafi wajen matan banzan shi, kuka ta ci gaba da yi sosai zuciyar ta kamar ta fito waje dan qunci, wannan wace irin rayuwa ce,Allah ya sani a rayuwar ta bata tab'a hango ta zaune da kishiya ba ita da Anwar d'in ta sai gata a gidan me mata biyu ya qara masu da wasu matan banzan a waje lallai bahaushe ya yi gaskiya da yace qaddara ta riga fata,a yanzu Allah kaɗai yasan iya adadin matan da Alhaji ke bi da wanda ya lalata ba tare da amincewar su ba, cikin kukan da take yi ta kalli sama tace,

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now