💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 27:
Yayun amarya da qawar ta Aysha sun gama shirin su tsaf dan dawowa da amarya garin kano ta dabo tumbin giwa,tafiyar awanni hud'u da minti arba'in ne ta iso da su har qofar gidan su Eamaan d'in, Wanda ta kula da shige da ficen mutane a gidan nasu,har abun ya tuna mata da lokacin auren ta na fari, a wancan lokacin ma haka aka yi taron mutane sosai a gidan nasu, wannan karon bata zaci zata ga kowa ba duba da yanda auren nata ya zo da Kuma cewar ita fa yanzu bazawara ce ba budurwa ba, wanne taron mutane Kuma za a yi?
Anwar bai san da dawowar su ba, da ace ya sani to fa ba makawa ta San cewa zai shi ze dakko su,direct d'akin su suka yada zango dan huce gajiyar da suka kwaso sanin cewa suna tafe ne ya sa aka tanadar masu abinci da abin sha, Hafsat da ke Jin yunwa ce ta zuba masu ita da Fatee suka fara ci, a can tsakar gidan kuwa cike yake da 'yan biki mata, gaba d'ayan su mamakin taruwar mutane da yawa suka dinga yi, Yaya ce ta katse masu tinanin su ta hanyar cewa,
"Kun San yanzu fa aure ne za a yi na soyayya, aure ne za a yi Wanda tin fil azal dangi shi suka zaci zai faru, duba da cewar kowa ya San soyayyar dake tsakanin Eamaan da Anwar d'in to kuma qaddara ta riga fata, dole kuwa yanzu ku ga dangi ko ta Ina"
Su Kan su su Amma da Maman sun yi mamakin cikar dangin nasu, saboda ba su yi gayyata ba, sun dai Sanar da daurin auren Eamaan da Anwar d'in, saboda dangi su sani, se Kuma suka basu mamaki da zuwa, 'yan uwan Mama sun ce dole ne a yi yinin biki, ba ruwan su da Wani auren bazawara ne, mijin ta ai saurayi ne.
Shagalin biki kuwa ya kankama, Eamaan ta yi mamakin ganin uban lefen da aka kawo Daga gidan su Anwar, se Daga baya ta yi murmushi ta tabbata Anwar be tab'a cire ran zai aure ta ba, maqota da abokan arziqi an tsattsaya ganin lefen da ya ba wa kowa mamaki, akwati seti d'aya da rabi kowanne kalar shi daban, Goggon Anwar ce ke musu bayani, seti d'aya ango ne ya yi abun shi tin da jimawa ya aje, Rabin setin kuwa uwar ango ce ta yi shi, kowa ka kalla fuskar shi d'auke take da annashuwa da annuri.
Bayan su Eamaan sun huce gajiyar su ne su Kai shiri da yamma dan zuwa gidan Iya,Eamaan Hafsat Yayah da Fatee ne zaune a mota Yayah na tuqa su, sai da suka tsaya a Wani shago Eamaan ta yi musu tsaraba, duk Wani abu da Iya ke so se da ta siya mata daidai misali, sannan ta qara da d'an abubuwan ci da sha suka ci gaba da tafiya,da kwatance da tambaya aka kaisu har gidan Iya, tana kwance jikin nata ya motsa, maganin ta na hawan jini ya qare jiya, ga ba kud'in siya ko da da kud'in ma wa zai siyo mata? ta yi kashi da fitsari a inda take kwancen a tsakar gidan duk jikin ta ya yamushe ta rame kamar ba ita ba, cikin ta sai qara yake saboda yunwa Dake addabar ta,bata san ina kan ta yake ba.
Ko da suka yi ta doka sallama suka ji shiru sun so su juya, a tinanin su ko wrong address ne,wata yarinya ce da ta musu gidan ta basu tabbacin nan ne gidan, tsohuwar gidan na ciki yau kwata kwata basu ga ta fito bara ba.
"Bara Kuma? Wanne irin bara, Iyan ce ke bara Kuma Ina Sahabeen?"
"Ai 'yan sanda sun kama shege, ya ishi kowa a unguwar nan da neman matan tsiya, matar shi kuwa bata da mutunci kwata kwata bata raga wa kowa, to qarshe ma na ji ana cewa ta gudu ta bar shi, shi Kuma 'yan sanda sun tafi da shi shekaran jiya"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,"
Tini hawaye ya fara zarya da rige rige a kuncin Eamaan a hanzarce ta afka gidan, ganin Iya a yashe a qasa cikin Wani mawuyacin hali ne ya Sanya ta qarasawa a guje ta tallabi Kan Iyar ta Dora a cinyar ta ta na kuka ta na Kiran sunan ta, Iya da ke kwance magashiyan bata San wake Kan ta ba, sai qoqarin bude ido take amma ta kasa, haka dai Yayah da Eamaan suka d'agata ta daga qasan, Eamaan tana kuka sosai ta ke gyara mata jikin ta, jallabiyar ta data dora akan atampar ta ta cire ta nade Iya a ciki, ta ce ma Hafsar ta taimaka ta siyo mata pure water ,domin kuwa Eamaan ta kula farkon abinda ya Kamata su fara yi wa Iyar maganin shi a wannan lokacin shi ne yunwa, dan yanda cikin ta ke kukan yunwa abun ya ba su matuqar tausayi,yau ko me Sahabee ya yi a ganin Eamaan ya Kamata 'yan sandan da suka kama shi su tausaya musu, Hafsat na tsaye ta na jinjina irin tausayi na Eamaan.
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.