BIYAYYAH PAGE 3

42 7 3
                                    

💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼







  RUBUTAWA: HAERMEEBRAERH






Page 3:





Cike da ladabi Eamaan ta zube a gaban Iya sannan ta ce,

" Barka da safiya Iya,"

Cikin isa da ɗauke kai ta amsa da,

" Lafiya ! baku ban amsa ta ba ai kan a kai ga gaishe-gaishen,"

Alhaji ne ya duqar da kai cike da biyayya yace,

" Iya amarya ta ce mai suna Eamaan, jiya ban shigo gida ba sai wajen 12am, shiyasa ban kawo maku ita ba ta gaishe ku,sannan nayi zaton ko dangin ta da suka kawo ta jiya sun kawo maki ita ta gaishe ki,"

" Eh sun kai ta, amma ai a qunshe ta ke waya gan ta? Miqe ka zauna abun ka,"

Miqewa yayi ya zauna kowa ya yi shiru,amma Hajiya A'i da Hajiya Rabi sai harare-hararen juna suke yi, Ilham ce ta gaida kakar tasu, cike da fara'a ta amsa mata, sannan Sabeerah ta gaida ta itama, amsawa tai sannan tace,

"Shin yau babu mai bamu abinci ne a gidan sai mun roqa?"

Kallon kallo suka fara yi a tsakanin su domin kowaccen su tana qyashin ace ita ce zatai directing masu aiki suyi girki bayan mijin na wajen amaryar shi, Hajiya Qarama ce wato Hajiya Rabi ta miqe ta fice hanyar da zata sada mutum da kitchen ɗin gidan,ma'aikata sun yi abinci kala-kala suna jira a kitchen ɗin suna zazzaune suna jiran me zai je ya zo tinda ba a basu umarnin kaiwa ba, tsoron masifar Iya kuma ya sa sun kasa yi wa kowa magana, a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru ta iske su, dan kusan suna jiyo tashin muryar ta koda basu fahimtar komai sin san masifar take saukewa, umarnin kawo abubuwan da suka dafa ta yi masu, suka ko biyo bayan ta da abincin kala-kala suka ajiye suka yi waje, a qaton carpet d'in  da suke haɗuwa kowa yaci abincin  suka baje, dan Iya bata son hawa dining table,dan haka dole kowa nan qaa zai zube in dai tare za a ci da ita, kowa na zaune yana kwasar girki banzda Eamaan, jita take yi duk a takure,saboda bata saba da su ba,Iyace ta kalle ta a yatsine cikin masifa tace,

" Malama idan za kici abinci ki kama ki ci,kina wani sunne kai kamar ta kwarai,"

Cike da jin tsoron Iya ta fara cin abincin, Alhaji kuma sai ya ji tausayin ta ya kama shi saboda ba haka ya san jikin ta ba duk ta rame, sai ya ji kamar ya bata a baki, gaba ɗaya ya kula a tsorace take da Iyan tashi, a haka aka ci aka gama, kowa ya tashi ya nufi sashen shi masu aiki suka ɗauke komai suka gyara wajen.

A hanyar su ta komawa sashen nata ne Alhaji ya kula da damuwar da ke tattare da Eamaan din, kafin ya gama nazarin ta ya ji ta na yi masa tambaya cike da damuwa.

" Alhaji kullum a babban parlor zamu dinga cin abinci?"

" A'a na yau ne kawai dama ina so ne na haɗa ki da sauran abokan zaman ki ku ga juna, to na zata Iya zata yi mana nasiha ne, amma na ga yau faɗan ta kamar yafi na kullum zan je na ji me ke damun ta yau ɗin, sannan kuma zamu haɗu a bangaren Hajiya Babba mu yi magana zuwa Wani lokacin,"

D'aga masa kai ta yi alamar gamsuwa da bayanan shi ,dan kuwa bata fatan sake zuwa wajen wannan tsohuwa mai faɗan tsiya.

Suna shiga d'aki ta cire hijabin ta ta ninke shi ta zauna waje d'aya a gefen gadon ta, kallo ya bita da shi yaga kamar har wannan lokacin a tsorace take, jan ta ya yi jikin shi ya fara lallashin ta,yanayin yanda yake yi mata ne ya sanya ta mamakin shi, da alama dai Alhaji baya tunawa da shekarun shi idan yana wasu abubuwan, luf ta yi a jikin shi tana zubar da hawaye a hankali dan bata son ya gane kuka take yi,sai kawai ta ja baya ta gyara kwanciyar ta kamar wadda ke yin bacci, murmushi ya yi dan a zaton shi wasannin da yayi mata ne suka sa mata kasala har ta yi bacci, miqewa ya yi yaje ya yi wanka ya fito tare da sanya kaya masu kyau, sannan ya dauki key na motar shi ya fice ya bar gidan dan zuwa wajen shaqatawar shi, wanda da fari ya zaci zai iya hakuri da ci gaba da neman matan banza, amma zuwan Eamaan da lamarin da ta zo da shi na baƙon wata na mata ba zai iya jurewa har ya jira ta gama ba,tana kallon shi ya gama duk abinda zai yi amma bata motsa ba, sai da ya fita ne taje ta rufe qofar ta jingina da murfin qofar ta hau kuka da qarfi, tabbas bata qaunar bawan Allah'n nan, gaba daya ba sa'an yin rayuwar auren ta bane, a ganin ta ko da cikin tsarki take yazo mata ai ganin shi zata yi kamar Daddyn ta, babban mutum haka ya dinga sauke buqatar shi akan ta da qananun shekarun ta? kaiii akwai takura sosai da jin nauyi gaskiya.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now