BIYAYYAH PAGE 17

37 5 0
                                    

💅🏼   BIYAYYAH   💅🏼





WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH





Page 17 :








D'aga kai suka Yi gaba d'ayan su suka kai duban su kan Eamaan da ke shiga parlourn nasu, Ammaah ce ta yi saurin goge hawayen ta ta miqe ta nufi Eamaan da sauri ta rungumeta,Eamaan cikin fara'a ta sakko mata da Fatee dake ta kuka, baya Ammaah ta ja kaɗan ta karbe ta ta rungume ta tana lallashi, gaba d'aya yarinyar ta sauya ta koma kamar wadda ruwan nono baya isar ta, ita kan ta Eamaan ɗin duk ta sauya,'yar qibar nan da tayi duk ta sauka,to damuwa tayi mata yawa kuma ga gidan miji komai ya ja baya ba kamar da ba, gaida su ta yi cikin natsuwar ta da ladabi da biyayyar ta Daddy cikin sakewa da tausayawa ya amsa mata,Ammaah kam da Mama cikin share hawaye suka amsa mata dan sun kasa b'oye damuwar su akan halin da suka ganta, itan ma idon ta ya cika da kwalla amma sai ta sanya hannunta ta share, tambayar ta suka yi mai jiki ta amsa musu da cewa,

"Da sauqi alhamdulillahi dama abin da ya kawo ni kenan akan Maganar Baban Fateen ne, muna son muje gashi wannan satin amma bamu da kud'in mota, ga kud'ad'en da ya biya na asibitin da muke zuwa sunce ya qare an kuma rubuto wasu magunguna,yanzu haka daga wajen sayar da gwalai-gwalai na dawo na sayar da nawa kud'in dana had'a naga akwai sauran cikon 20k kafin su isa na maida shi asibitin shine nace bari na zo dan Allah Dad......,"

kan ta qarasa maganar ta yayi sauri ya katse ta da faɗin

"Kar ki roqe ni dan Allah Mamana, fad'a min buqatar ki yanzu na biya maki ita in dai bai fi qarfina ba, kome kike so ni zan yi maki shi a duniyar nan, in dai bai sab'awa Allah ba,wanda na san ma ba za ki taɓa bijiro da sabon Allah wajen mu ba, dan haka taso ki karb'a ki yi sauri ki je a kai shi asibitin, Allah ya qarawa rayuwar ki albarka ya baki ladan biyayyar da kika kasance kina yi mana a koda yaushe, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka,domin babu addu'ar da zaka yiwa ɗan uwan ka musulmi data wuce ka nema masa albarka a wajen ubangiji,albarka ta qunshi komai na duniya da lahira da bawa zai samu na alkairi, Allah yayi miki albarka da zuri'ar ki baki ɗaya Mamana,"

Cikin tsananin kuka da jin dad'in kalaman mahaifin nata ta je gare shi ya miqe tsaye ya rungume ta tsam a qirjin shi tare da sumbatar  goshin ta,ya sa hannu a aljihun shi,ya zaro kuɗin da shi kan shi bai san ma iyakar su ba ya bata, Ammaah ce ta koma ɗakin ta ita da Mama suka d'akko mata kuɗi,kayan abinci da sauran su suka bata suna sanya mata albarka tare da yi mata fatan samun sassauci a rayuwar da take fuskanta, godiya tayi masu sosai ta tattare komai zata tafi, Daddy ya sa driver ya maida ita gida.

Cike da murna ta shiga sashen Iya da ta kai shi ajiya dan kar ta barshi shi kaɗai, nan ta same shi kwance a kujerar shi ya yi kashi a jikin shi yana ta kuka ,dan kuwa Iya ta kasa koda motsa qafar shi ce balle ta d'aga shi ta gyara masa,fuskar shi tayi jawur har ajiyar zuciya yake saukewa sabida kukan da yayi, da sauri ta qarasa wajen shi tana tambayar shi lafiya yake kuka haka? Tana qarasawa inda yake ta ji wari, kauda kan shi yayi gefe saboda nauyin ta da yaji ya kama shi,ita kuwa sai tayi murmushi ta sauke Fatee da ta yi bacci a wajen Iya ta tura shi suka koma sashen ta ta fara gyara masa jikin shi,sai da ta gama yi masa tsarki da wanka tass sannan ta canja masa wajen kwanciya, ta dauki kayan daya b'ata ta je ta wanke su ta shanya ta koma ta d'akko tiraren wuta ta kunna a dakin ta fesa na fesawa, daga nan ta koma ta d'akko Fatee da ke bacci ta kwantar da ita a gado ta koma ta yi wanka,cikin shirin doguwar riga ta fito ta zauna kusa da shi ta kama hannun shi tace,

"Sweet na sha gaya maka ka daina damuwa dan ka yi bayan gida,ba ga ni ba zan wanke maka ko akwai wani abu dake damun kane da baka sanar dani ba? Ko kuma dai ladan da nake samu ne baka soooo"

Ta fad'a cike da shagwab'a,hawayen shi ne ya sake sakkowa saman kuncin shi cikin maganar shi da kamar koya yake yi ya labarta mata abinda ya faru da bata nan,

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now