💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 22:
Direct bakeryn ya koma, yana shiga masu gadi da ma'aikatan wajen suka yi ta gaida shi da fara'a a fuskar su, dan suna matuqar son Anwar sosai,Anwar akwai mutunci ga kamala, da kyautata wa, yana yawan zuwa wajen siyan abincin shi da na Mai gadin gidan shi da Mai masa share share, in ya zo su na Shan hira kala-kala kan ya tafi,hirar siyasa ne ta ilimi ne da kuma hira akan yanda samari da 'yammata ke gudanar da soyayya a wannan zamanin saboda kasancewar wajen wajen saida kayan kwalam suna ganin abubuwa kala-kala dake faruwa.
Tin da yake zuwa wajen basu tab'a ganin ya je da budurwa ba, ko Kuma su ga ya tsayar da budurwa a wajen, dik da cewa waje ne da matasa maza da mata ke zuwa siyan snacks da sauran su.
Kwatsam sai su ka ji ya na musu tambayar da ta sa su kallon juna fuskokin su dauke da fara'a da alama bana Anwar ya samu wadda ta sace zuciyar shi, shi ma d'an murmushi ya yi ya gyara tsayiwar shi sannan yace,
"Tabbas akwai abinda baku sani ba game da rayuwa ta, wannan da kuka ji ina tambaya itace rayuwata,itace firsr love d'ina, wadda nake sa ran ta zama last, dan in ba ita na aura ba ba zan tab'a samun kwanciyar hankali ba ko soyayyar gaskiya,nan na ga ta shigo d'azu da safe kafin na wuce asibiti, ta na sanye da hijabi kalar pink dogo har qasa, fara ce me matsakaicin tsaho, ta na da kyau Mai d'aukan hankalin me kallon ta,tana da siririyar murya Mai sanyi da zaqin sauraro, girar ta na da cika sannan..."
Cikin tausasawa murya d'aya daga cikin securities na wajen yace,
"Ranka ya dade ina roqon Allah daya mallaka maka ita Allah ya sa rabon ka ce, ba sai ka qarasa kwatancen ta ba ma na gane ta, tabbas na ga shigar baiwar Allahn Kuma na ga sanda ta b'uya a can wajen cike da tsoro, da Wani irin yanayi a tattare da ita, sanda ka shigo Ina gaishe ka baka ji ni ba ai, se na ga kana dube dube ka fita cikin damuwa, tafiyar ka ke da wuya baiwar Allahn ta fito ta sai bread ta tafi cikin hanzari, ranka ya dad'e gaskiya ban mata sani na musamman ba amman yan da ka kwatanta ta dai tabbas sun tab'a zuwa nan sau biyu su biyu mata da Kuma namiji d'aya sai qaramar yarinya sun siyi pizza ranar Sunday da ta gabata,inaga yanda za a yi yanzu shine tinda Ina da lambar ka da na ga sunzo zan faɗa maka sai ka zo ka riske ta"
Cikin rawar hannu Anwar ya miqa masa hannu suka qara gaisawa, ya shiga godiya kamar har ma an had'a shi da Eamaan d'in shi,ya yi masu alherin da ya saba ya tafi gida cike da addu'ar Allah ya sa a kira shi da wuri idan an ganta, zuwa ya yi gida ya yi wanka ya wuce masallacin Juma'a aka yi sallah da shi,ya na dawowa gida sai ya ja qur'anin shi ya karanta suratul Kahfi bayan ya idar ya hau yiwa Annabi salati ,yana cikin yi ne bacci ya dauke shi.
'Baby pls ka bari, ni bana soooo'
'kina mana so Sweety,to tsaya idan baki son wancan bari na maki wannan'
Sai ya fara tickling d'in ta ita Kuma ta na ta dariya, d'an tsaya wa ya yi kad'an ita kuma ta rungume shi,zata kai bakin ta nashi kenan ya ji an jijjiga shi, cike da jin haushi ya miqe tare da addu'ar tashi a bacci.
" Kai dalla can galahore kawai, meye haka zaka zo ka tada ni ina bacci na me dad'i,"
Dariya abokin shi Jamal ya yi yana kallon yanda Anwar yake fushin da bai san shi da shi ba, kwata kwata fushin ma be dace da shi ba tinda ba halin shi bane.
" Haba namijin duniya,meye zai d'aga hankalin ka a mafarki haka? To koma mene ne alkhairi ne da yardar Allah success is urs man, Allah zai kare ka daga dikkan Sharrin da mafarkin ya qunsa ya kuma haɗa ka da alkhairin shi, dan haka ka miqe lokacin fara addu'o'i ya yi, tin da ka san dai ba wai mun san sa'ar da aka ce in mutum ya dace da ita a ranar juma'a ya yi addu'a Allah zai amsa bane lalube muke a duhu, Allah ya datar da mu"
![](https://img.wattpad.com/cover/332311715-288-k451043.jpg)
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.