BIYAYYAH PAGE 16

35 6 0
                                    

💅🏼     BIYAYYAH   💅🏼









WRITTEN BY HAERMEEBRAERH









Page 16:



Ganin hukumar EFCC a gidan Alhaji ba qaramin tada wa kowa hankali yayi ba, jikin shi har rawa yake yi a lokacin da ya koma ya zauna,suna shiga suka samu waje suka zauna suma kamar gidan su tare da gabatar da kawunan su da kuma abinda ya kawo su,babu b'ata lokaci suka fara binciken Alhaji daga fatari har fataari, duk wata dukiyar shi sai da aka karɓe da sunan za a yi bincike akai idan haqqin shi ce za a dawo masa da ita, idan kuma ta gwamnati ce to fa gwamnatin zata karɓe wataqila har hukunci ma ya biyo baya,ganin yanda suke yi masa abubuwa cikin cin zarafi da wulaqanci ne ya koma tunanin  anya wannan hukumar EFCC ne ma kuwa?

Amshe dikkan kadarorin shi da hukumar tayi ne ya sanya jikin Alhaji ɗaukan rawar sanyi, Eamaan kam ta dad'e da fara kuka saboda matsanancin tausayin mijin nata da ya kama ta,abubuwan da suke samun shi akai-akai na musibu sun yi yawa.

Eamaan da Iya sai kuka suke zabgawa babu mai lallashin wani a cikin su,Alhaji kuwa yana zaune shiru banda karkarwa babu abinda jikin shi ke yi, ma'aikatan hukumar da kansu suka dinga shiga lungu da saqon gidan suna ɗaukan takardu da dik abinda yayi musu, Hajiya Babba kuwa takaicin kwashe mata sarqoqin zinaren ta dik shi yafi damun ta har ya sanya ta kasa yin kukan ma, shi kuwa Sahabee baqin cikin yanda aka k'wace komai ba tare da ya samu wani abu daga wajen yayan nashi ba shi ya sanya shi zabga tagumi yana bin kowa da kallo,daga gidan da suke ciki sai motoci biyu kawai aka bar musu.

Suna cikin wannan halin na jimami aka sake k'wank'wasa qofar parlourn Iya,nan take Alhaji yaji k'wank'wasawar har cikin tsokar zuciyar shi,gani yake yi kamar wata musibar ce ta sake tinkaro shi da iyalan shi,babu wanda yayi jarumtar amsawa mai k'wank'wasawar daga qarshe dai da kan shi ya buɗe ya shiga parlourn cike da isa da taqama, Alhaji Saminu ne yake ta zabga murmushin da yafi dacewa a kira shi da sassanyar dariyar samun nasara kafin yace,

" Alhaji Abdullahi kenan a zaton ka zaka samu kuɗin gwamnati ka sace ka killace dan ka mora kai da iyalan ka ba tare da gwamnati ta k'wace abinta ba? to bari kaji wani sabon albishir da zan yi maka dan na kula baka kalli news ba jiya kana nan kana shanawa da wannan kyakkyawar matar taka ko? Albishir ɗin shine majalisa ta sauke ka daga muqaminka yanzu haka ana can ana jefa quri'ar samun madadin ka,kai kuma kana nan a nade wajen mata,"

Ya na gama faɗin maganganun nashi dake kama da shaqiyanci ya kwashe da dariyar mugunta harda tafa hannayen shi,a harzuqe Alhaji yayi kan shi da niyyar yi masa dukan tsiya,kafin ya qarasa gaban Alhaji Saminu ya yanke jiki ya fad'i a qasa yana ta wani abu kamar mai bugun iska.

Ihu Eamaan ta sanya ta ajiye Fatee ta nufe shi tana jijjigawa, Iya kuwa jinin ta ya jima da hayewa ganin ta gaba ɗaya yayi rauni jinta take yi kamar ba zata kai gobe ba saboda tsananin ciwon kai da bugawa da zuciyar ta keyi dan haka ko yunqurin zuwa wajen Alhaji bata yi ba,dan kuwa ta riga ta san da ta miqe se dai a yi biyu,sunan Allah kawai take ambata dan shine mafitar ta a wannan halin da suke ciki.

Eamaan kuka take tayi sosai ta na yima Sahabee magana akan ya rabu da Alhaji Saminu daya dunqunqunewa wuya ya zo akai Alhaji asibiti,amma ya qi sai naushin Alhaji Saminu yake yi yana zagin shi, shi kuma yana dariya kamar ba jikin shi ake duka ba.

Jikin Alhaji Abdullah ne ya saki ya daina motsi Eamaan kuwa sai ta fasa ihu da qarfi wanda ya ja hankulan Hajiya Babba da Sahabee,Waje Sahabee yaje ya hau kiran masu gadi da driver akan su zo su taimaka masa, suna zuwa kuwa suka hau ciccibar Alhajin suka fita dashi suka sanya shi a mota .

Asibiti suka kai Alhaji nan da nan likitoci suka duqufa akan shi dan duba lafiyar shi, ba shi ya farfado ba kuwa sai da asubar washegarin ranar da suka kaishi asibitin, Eamaan ta ci kuka ta gode Allah har ta hakura ta barwa Allah komai, Fatee kuwa sai kallo take bin kowa da shi,lokacin da likitoci suka sanar da iyalan Alhaji samun cutar barin jikin da ya yi ba qaramin shiga cikin damuwa suka yi ba, likitocin kansu sai da suka tausaya ma su saboda sun san shi farin sani ma kuwa yana daga cikin masu kuɗin dake taimakawa asibitin nasu, ga Alhaji nan kwance samb'al babu imm ba umm umm sai ido,yawu ma baya iya hadiye shi gaba ɗaya sai wani ya zubo,Eaamaan kamar zata haukace haka take jin kan ta, saboda shiga damuwa da tashin hankali,tashiga wani irin yanayi na tsantsan tausaya ma mijin nata,nan take ta hau yi masa addu'ar Allah yasa ta hanyar jinyar nan da ta same shi ya samu gafarar Allah,Allah ya yafe masa dukkan abinda ya aikata.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now