BIYAYYAH PAGE 20

81 6 0
                                    

💅🏼    BIYAYYAH  💅🏼




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



Page 20:


Wani abu ne da ba zata Iya tantance mene ne ba ya ke taso mata a wuya, maqaqin da take ji baya yi mata dad'i, after all he put them through he have the nerve to show his stupid face a gidan su? lallai yau za a yi ta kenan dan kuwa sai ta nuna masa itama 'yar zamani ce.

Wata zuciyar ce ta taushe ta har taji a ranta tana son barin wajen tin kafin ta kasa riqe kanta, tashi tayi tsam daga sama kujerar robar da take kai zata shiga gida ɗauke da Fatee a hannun ta,tana zuwa gefen da yake zata zagaye shi ya sha gaban ta ya tsaida ita,wani kallo ta d'ago ta watsa masa da idanun ta da suka rine suka yi jawur kamar jan yadi,nan take jikin shi yayi sanyi izzar shi ta fara raguwa saboda kallon ya shige shi, sai dai taurin kai irin nashi ya hana shi ya kauce ya bata waje ta samu ta bar wajen,cikin muryar shi mai nuna isa da taqama yace,

" Hajiya Eamaan barka da war haka, ya qarin hakurin mu kuma?to Allah ya jiqan Alhaji yayi masa gafara,"

Haka ya gama gaishe-gaishen shi ba tare da ta ce masa kanzil ba, burin ta kawai ya matsa ya bata waje ta wuce, Hafsat na ganin yanayin da Eamaan ke ciki ta miqe ta isa gaban ta, hannun ta sai wata iriyar rawa yake yi,hannu ta sanya ta amshe Fatee daga wajen Eamaan ɗin ta tsaya a gefen qanwar tata.

" Uhum ina jin ka sai me ya kawo ka bayan fake concern din da ka gama nunawa yanzu? In ba ka da abin fad'a ka wuce ka tafi, kafin raina ya yi matuqar baci naka ran yafi nawa baci yanzun nan,"

" Eamaan na zo ne da magana mai mahimmanci, wanda ina ganin bai kamata muyi ta a tsaye ba,"

" Dakata min malam, kai har kana da magana mai amfani da zaka zauna ka yi min ne har na saurare ka? Waye kai? me kake taqama da shi da har zaka manta komai da ka aikata dan baka da kunya kazo min ta'aziyya? kayi kaɗan ka ce zaka yi amai ka lashe akaina, ka kama hanya tin bamu shiga wani hali na rashin mutunci da kai ba,"

" Ina son ki Eamaan kuma auren ki nake so nayi wannan shine muhimmin abinda ya kawo ni wajen ki, ina sane da kin gama......"

Wani shahararren mari ta ɗauke tsohon mutane da shi, ta qara yanka masa wani marin, haka ta dinga kifa masa mari tana kuka,  Yayah ce ta iso gare ta da gudu ta riqe ta tace,

" Ke Eamaan baki da hankali ne kike marin babban mutum kamar wannan, me yake damun ki ne, kalmar so tana jawo qiyayya ne?"

Cikin qara da tsawa ta furta

" Eh Yayah ! kalmar so na jawo gaba ma ba qiyayya ba, Yayah wannan ne Alhaji Saminu, da ya shiga cikin taswirar rayuwar mu ya b'ata ta, ya nakasa min miji ta zahiri da bad'ini, sannan a qarshe ya yi sanadiyyar mutuwar shi,waya baka damar zuwa min da shirmen kalmar so waje na? hhhhh idan ka amince zaka aure ni to zan aure ka, amma se dai in ni ce zan zama ajalin ka,shin ka yarda?"

Tinda mutanen gidan su suke da Eamaan ba su tab'a ganin ta yi faɗa da kowa ba balle har duka ya shiga tsakani irin haka sai yau, ko da ace bata tab'a son Alhaji Abdullah ba tabbas ya na da Wani babban matsayi a zuciyar ta Wanda ba zai gogu ba, Alhaji Mutum ne da ya so ta sama da yanda take ganin Anwar ma zai so ta, ya kula da ita sama da yanda ta ke tinanin Anwar zai kula da ita, Alhaji Mutum ne da baya son damuwar ta, ya tsare mata dikkan Wani haqqi na aure nata da ke Kan shi, ta ya ba zata ji mutuwar shi ba?shi ne fa uban 'yar ta tilo,

Cike da qunci da d'acin zuciya take bin shi da mugun kallo idanun ta na kwarar da hawayen baqin cikin da zuciyar ta ke ciki, 'yan uwan ta da masu aikin gidan har ma da iyayen ta da suka fito kowa sai mamakin yanayin da  Eamaan mai sanyin hali da kunya tare da kawaici ta koma a cikin kankanin lokaci, yau har ta kai ga itace ke ikirarin kashe wani,cikin tsawa ta sake furta,

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now