💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 11:
*My one and only husband, ina roqon ka da kuma sake yi maka tini akan kaji tsoron Allah,ka sani indan kai baka ganin shi to shi yana ganin ka, ka kare mana mutuncin mu ta hanyar adana kan ka har sai ka dawo gare mu, zamu tarbe ka da tarbar da baka tab'a zato ba mijin mu, muna son ka,Allah ya dawo mana da kai lafiya..In kewa ta dame ka ka Kira d'aya daga cikin mu video call ko voice call za mu yi qoqarin taimaka Maka ta kowacce hanya da ta dace*
*Eamaaniin Alhaji shi kaɗai*
Nan take Alhaji ji ya ji gaba d'aya an zare masa lakar jikin shi,tini ya nemi sha'awar shi ya rasa, miqewa ya yi ya je ya yo alwala ya yi ta nafilfulu,kamar yanda ya ji Eamaan tana yawan faɗa yin nafila yana kawar da mugun tunani da damuwa.
Haqiqa Eamaan tayi gaskiya a maganganun ta domin kuwa Alhaji be gushe yana nafila ba face sai da ya ji wani qarfin imani na shigar shi, tsoron Allah da kunyar Allah ta kama shi, a nan ya zauna yana ta kuka yana neman gafarar Allah akan abubuwan da yayi a baya,sannan ya roqi Allah daya kare shi da zuri'ar shi daga zina,a haka ya fara gyangyadi sai kawai ya miqe ya yi shirin bacci, da asubar fari ya farka ya yi brush ya yi alwala ya yi sallah, tinani ne yazo masa na komawa gida ko kuma kiran Eamaan ta sama masa natsuwar da ta alqawarta masa, domin kuwa tinda ya tashi da safe yake jin shi wani iri.
Nasihar Eamaan ce ta yin azumin nafila ta sake fad'o masa a rai a karo na babu adadi,tinda ya iso garin Abuja a komai zai yi sai ya tuna da ita da nasihar da take yi masa,kawai sai ya d'aura niyyar zarcewa da azumi.
'Yana da kyau wanda ba ya iya riqe sha'awarsa ya dinga yin azumin nafila akai akai,kuma ya gujewa dikkan abinda zai tada masa da sha'awa idan yayi haka zai kauce fad'awa sharrin zina'
Yana gama tinawa da kalaman yarinyar sai ya saki murmushi mai kyau ya ce,
" Da dikkan alamu an sanar da yarinyar nan dalilin aure na da ita shiyasa take yi min wa'azi cikin hikima da ladabi tare da girmamawa dik da ban cancanta da hakan ba,Yah Allah ka yi mata albarka ka bani iKon sauya halaye na domin ka ko iyali na za su samu natsuwa da kwanciyar hankali da ni,"
Tabbas yana tsananin jin kunyar yarinyar da ya San zai iya haifar wanda suka girme mata ma, akwai wani lokaci da Eamaan ta taɓa ce masa,
'Haqiqa Allah shine mafi cancanta kowanne bawa ya ji kunya ya bar aikata sab'on Allah ba mutane ba, domin kuwa Allah shine yake da wuta kuma yake da aljannah, shi yayi hani da zina da shirka,ya bada umarni a tsaida sallah a bi iyaye, kaga kuwa shi ne zai sanya wanda ya kyautata a aljannah ya jefa wanda ya munana a wuta, dan haka kar ka bar aikata zunubi domin mutane ka bar aikata zunubi domin Allah kawai sai ka rabauta duniya da lahira,'
Hawaye ne suke gangara a kuncin Alhaji na tsananin tsoron Allah da yake jin yana shigar shi a lokaci ɗaya, yana cikin wannan halin wayar shi ta yi qara, yana dubawa sai yaga sunan *My Babee* na yawo a saman screen ɗin wayar,murmushi ya yi cikin hawayen da ke zuba a idanun shi ya d'aga wayar,kafin yayi sallama yaji zazzaqar muryar ta na faɗin,
"I miss u so so very much my love, na kasa zaune na kasa tsaye saboda tsananin kewar mijina,"
Dad'i ne ya kama Alhaji tinda ya zo Abuja kusan a rana sai ta kira shi sama da sau biyar, a baya kuwa tinda yake a cikin matan shi babu wadda ta damu da ta kira ta ji ma ya ya isa lafiya balle a kai ga wai ta kira shi haka nan dan jin ya yake, sai dai shi ya kira su yaji ya suke,soyayya suka sha ta waya sosai, da ya ji muryar ta na kashe masa jiki kuwa sai ya ce mata yana ɗan gabatar da wasu ayyuka ne, kamar irin bayan magrib dinnan zai kirata suyi waya, addu'a ta yi masa tare da fatan samun nasara akan ayyukan shi suka yi sallama suka kashe wayar.
![](https://img.wattpad.com/cover/332311715-288-k451043.jpg)
YOU ARE READING
BIYAYYAH
عاطفيةRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.