💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 10:
Shigar Hajiya Babba ke da wuya ta samu waje ta zauna a gefen Hajiya Qarama da ta bi hannun ta da kallo,harara Iya ta banka mata saboda dad'ewar da tayi bata zo ba, daga baya kuma sai ta gyara zama ta fara da godewa Allah da ya bawa Alhaji Abdullahi lafiya ya kuma dawo mata da shi gida lafiya, daga nan ta hau qorafe-qorafen ta na babu gaira babu dalili kafin ta bawa Alhaji Abdullah damar ya yi magana shima.
Shima ya fara ne da godewa Allah da ya bashi lafiya ya dawo cikin iyalan shi lafiya daga qarshe ya godewa matan nashi akan qoqarin su a gare shi da dikkan d'awainiya da hidimar da suka yi tayi da shi a lokacin da yana kwance a asibiti,bayan nan ne ya sanar da su zai koma Abuja ana da buqatar shi a wajen hidindimun siyasar su.
Kuɗi ya d'akko ya miqa wa kowa nashi kamar yanda ya saba, sannan ya jawa Sahabee kunne akan dad'ewar dare da yake yi.
Niko nace wai kura ce za tace da kare maye,hannun Hajiya Babba ya kalla cikin mamaki ya ce,
" Hajiya me ya samu hannun ki na ga kamar ya kumbura?"
A ɗan razane ta kalli Eamaan da ta kauda kan ta daga kallon ta ta yi kamar ma ba ta ji tambayar da akai wa Hajiya Babba ba, nan da nan zuciyar dake shawartar Hajiyan akan ta faɗi me suka yi ta taso mata,cikin sauri Eamaan tace,
" Alhaji ka gafarce ni d'azu na je gaishe ta ne na buɗe qofar shiga tana wajen ban sani ba na buge ta,"
"Subhanallahi Allah ya kiyaye gaba, ke kuma kina k'wank'wasa qofa kan ki shiga waje gudun faruwar irin hakan,"
Amsawa ta yi da zata kiyaye gaba sannan ta sake kauda kan ta daga barin kallon kowa a wajen, Sahabee da Hajiya kuwa zuciyoyin su babu dad'i dan hakan na qara sanya su a dogon nazari da jin tsoron me zai je yazo game da shirun Eamaan ɗin,muryar Alhaji suka ji yana faɗin,
" Sahabee ka kai Hajiya Babba asibiti a duban hannun nata,"
" To Yayah," yace yana wani sunne kai qasa kamar na Allah.
Daga haka sai Alhaji ya miqe ya fice zuwa ɓangaren Eamaan yana fita ba jimawa itama ta bi bayan shi, idanu suka zuba mata gaba ɗayan su har Iya, tana fita Hajiya qarama tace,
"Ni fa ina ganin wani al'amari a wajen yarinyar nan, ban sani ba ko kun kula da hakan kuma?"
Hankalin Sahabee da Hajiya Babba ne ya qara kid'ima suka faɗa tashin hankalin Allah yasa ba gano abinda suka aikata Hajiya Qarama tayi ba,cikin zumud'i Hajiya Babba tace,
"Me kike nufi da maganar ki?"
Iya ce ta karɓe maganar da cewa,
"Tana nufin Eamaanii na ɗauke da juna biyu na haihuwa,"
A zabure Hajiya Babba da Sahabee suka had'a baki wajen faɗin,
"Cikiii kuma?"
Hajiya Babba ce ta dafe qirji da hannun ta me lafiya ta kalli Iya tace,
" Iya ciki fa kika ce, yaushe ma tazo gidan har da zata yi ciki ni ina nan ina fama shekara da shekaru ban taɓa koda bari bane?to gwanda ma Hajiya Qarama ta ajiye waɗannan gajiyayyun yaran marasa jin magana, ni yanzu ina na kama babu d'a babu jika?"
"Ya ko me zaki yi banda ki zubawa sarautar Allah idanu a yi abinda kike gudu babu ke? Ke kam yanzu in ba wani ikon Allahn ba ba wata haihuwa da zaki yi nan gaba tsufa ya riga da ya riske ki, dan haka kawai ki barmu masu sauran jini a jika mu yi ta haihuwar,"
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomansaRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.