💅🏼 BIYAYYAH. 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 24:
Anwar ya isa kano bayan azahar, direct unguwar su ya nufa cike da d'oki, sai dai bai san me yasa gaban shi ke ta fad'uwa ba, addu'a ya fara yi akan Allah ya kare shi daga dikkan abun qi ya tabbatar musu da alkhairi, ta gaban gidan su Eamaan ya wuce, aran shi yana ayyana nan da yan kwanaki za a daura auren su da Eamaan din shi anan, Wani qayataccen murmushi ya saki, ya tarar da mai gadin gidan nasu a qofar gate din gidan tare da abokan shi ya na ta hira,hango motar Anwar ne ya Sanya shi sheqawa a guje dan bud'e gate d'in, sallama ya wa abokan Mai gadin nasu sannan ya danna hancin motar shi compound din gidan su Mai d'auke da motoci kala-kala,daga inda yayi parking d'in motar shi ya na iya hango mahaifiyar shi dake cikin lambun gidan tana ta kaiwa da komowa hannayen ta hard'e a bayan ta cike da isa,da dikkan alama tana cikin wani yanayi ne na damuwa, fuskar ta sam babu walwala a cikin ta kamar kullum, tayi nisa sosai a cikin tinanin da ta ke yi shi yasa bata San shigar Anwar d'in gidan ba ma.
Bude motar shi ya yi sannan ya fita tare da zagayawa ya bude bayan motar ya ɗauki ledojin da ya tsaya a hanya ya yo tsaraba ya fara takawa zuwa ga mahaifiyar shi da suke Kira da Hajiyah, yana isa ta d'ago kan ta ta kalle shi tare da murmusawa kaɗan,sannan ta ce,
" Sannu da zuwa mutanen bauchi qaya baku san na gida ba,"
Murmushi Shima ya mayar mata sannan ya ce,
" Barka da hutawa Hajiya ta,akwai abinda ke damun ki ne? Na ga kin yi nisa cikin tinanin da kike yi har na shigo baki sani ba,"
Kama hannun shi ta yi suka fara takawa cikin gidan,
" Muje ciki kai wanka ka ci abinci ka huta zamu yi magana mai mahimmanci da kai,"
'Daga mata kai ya yi alamar to, amma zuciyar shi sai bugawa take da dikkan alamu abinda za su yi magana akai Mai mahimmanci ne, tinda Hajiyah ta gama nuna hakan a fuskar shi, bayan sun shiga ne ya kammala komai, ya kwanta da niyyar ya dan samu bacci, amma inaaa baccin nan ba zai samu ba, tabbas sai yaji me ke damun Hajiyan shi haka? Tashi yai ya saka qananan kaya marasa nauyi ya fesa tirare ya saka takalmin shi ya fita.
A daki ya same ta tana kwance kamar mai bacci amma idon ta biyu, sallama ya yi ta tashi zaune tare da amsa masa sallamar shi, nuna masa kusa da ita ta yi alamar ya zauna, zama ya yi yana fuskantar ta, ta shafa kan shi tare da murmusawa tace,
"Anwar in baka yi wasa ba zaka zama babban tuzuru a layin nan, rashin auren ka na damun mu matiqa ni da Abban ku,shin wai yaushe ne za ka yi aure? Ka sani kai d'aya ne Wanda muke da shi, ga shi girma ya fara kama mu ba kai aure ba balle mu sa ran samun zuri' daga wajen ka,bama ka da niyyar aure Anwar why? Yarinyar da ka kwallafawa rai ta yi aure mijin ya mutu,zawarci take yi yanzu, kaga ba sa'ar auren ka bace ita sai ka nemi wata, amma Anwar 8inaa ka qi sam, ko an nemo maka sai ka ce basu yi maka ba, ya kake8 so na yi ne Anwar,"
Ta qarasa maganar ta cikin damuwa sosai, Anwar ya fita shiga damuwa musamman da yaji tana neman condaming auren na su tin kafin ya fad'i me ya kawo shi, zufa kawai yake yi,a hankali ya saka hannu ya share, kallon shi ta yi cikin kulawa ta ce,
" Son me ke faruwa ne na ga ka shiga halin damuwa? Ko na faɗi wani abu daya d'aga maka hankali ne haka,"
" Kwarai kuwa Hajiya ta,domin kuwa yanzu haka har mun daidaita da Eamaan akan maganar auren mu,kuma ta amince da ni nima na amince da ita, yayun ta dika sun yarda na faɗa wa magabatan na wato na fada maku a nemar min auren Eamaan, Hajiya na rasa ta a baya ba....."
"Haka wannan karon ma zaka sake rasa ta, wai Kai Anwar wanne irin yaro ne Kai mai kafiya da naci? Ba ka ganin yanda mahaifiyar ta ta mallake mahaifin ta se abinda ta ce, so ka ke Ina zaune wata ta zo ta dinga juya ka se yanda ta yi da Kai ni na sha wahalar banza kenan? Ba zai Yu ba to! can gidan ma da ta bari Ina da labari har mijin ya rasu ita ke juya gidan,me ka ke tunanin zai faru anan gidan in ka aure ta?"
![](https://img.wattpad.com/cover/332311715-288-k451043.jpg)
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.