💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
RUBUTAWA:HAERMEEBRAERH
Page 6:
Saida ya biya da su supaer market ta sai kayan kwalama sosai son ranta, shi da kan shi ya qara mata bayan ta gama ɗaukan Wanda take so sannan suka dawo gida,a tsaye a bakin qofar shiga wajen Eamaan suka tadda tsohuwar a coge tana kad'a qafa, Sahabee na ta bata baki akan su koma iska nata kad'a ta amma ta qi, dan ya ga alamar ba da wuri za su dawo ba, ya juya ya fara tafiya kenan suka Jiyo qarar motar Alhaji, me gadi ya isa qofa babu b'ata lokaci ya wangale gate, gyara tsayuwarta ta sake yi ta cuno baki gaba, Hajiya A'i kuwa na tsaye tana leqen su ta window dan taga ya za a qare, itama Hajiya Qarama tana leqawa lokaci zuwa lokaci ta na jinjina masifa irin ta Iya da bata qarewa,Alhaji kuwa zagayawa ya yi gefen Eamaan ya bud'e mata qofa, bayan ya buɗe mata motar ne ta fito ya dakko mata jakar ta da ledojin suka jero su na takawa cikin nutsuwa, Alhaji se santin abincin da ya ci d'azu a gidan su yake yi mata, ita Kuma ta na ui masa dariya tare da tsokanar shi, haushin ganin su cikin nishad'i ya kama kowacce daga cikin matan Alhaji har da Iyan ma da take uwar shi, Sahabee kuwa na can ya lula wani tinani na daban a qasan ran shi,cikin masifa Iya tace musu,
" Sannu riqaqqu wato sai yanzu kuka ga damar dawowa ko? Na zaci a titi zaku kwana ai,Kun kama hanya Kun tafi Kun bar ni da yunwa,bayan kin san sarai yau girkin ki ne, tin da ki ka zo gidan nan ki ke azabtar da ni da yunwa ban san me na yi miki ba, to bari ki ji ba zan mutu ba se lokaci na ya yi, Dan haka wuce muje ki tuqan tuwon alkama miyar kub'ewa, dan nasan shi ne kawai ze raba ni da yunwar da na wuni zubur da ita,"
Mamaki ne fal cikin Eamaan, ita Iya wai ko girman Alhaji bata gani ne take yi masa irin waɗannan abubuwan, koda cewa ita ta haife shi amma ai akwai jin nauyi a tsakanin yara da iyayen su idan an kai wani minzali kuma,da ace Alhaji ya samu haihuwa da wuri da yanzu Yana da jikoki fa, Amma ba ruwan ta in ta tashi yi masa fad'a kamar ta na magana da qaramin yaron goye haka take yi kuma ko a jikin ta.
Iya kuwa sa kai ta yi gaba abun ta ta na ta sambatun fad'a,su Hajiya babba na jin haka farin ciki ya kama su dan sun san yau Eamaan sai ta ci uban aiki kan ta kwanta,yana son ya yi magana ko ya bawa Iya hakuri amma sai Eamaan ta kad'a masa kai, cike da murmushin da zai nuna masa kar ya damu zata je tayi aikin take kallon shi, kad'a mata kai ya yi alamar ta bari yaje ya bada hakuri,sai tace,
" A'a sweet ka bari kawai yanzu zan dawo ai, abinda ba zai wuce awa ɗaya ba an gama, kaga kan na dawo kaima na saka aiki, ka saka min ice cream ɗina da chocolates d'ina ga fridge, kuma kar a sha min sweet ta wuce biyu, inna dawo zan qirga abuna,"
kamo ta ya yi cike da so da qaunar halayen ta tare da tsantsan girmamawa a tsakanin su, ya sumbace ta sannan ya raka ta har side ɗin Iya sannan ya juya ya koma sashen ta, a wannan lokacin ne Sahabee dake gefe yana kallon komai ya cika ya yi fam kamar an tab'a matar shi, ganin yanda Alhaji ya sumbaci Eamaan abun ya Sosa ran shi ainun,qara lab'ewa ya yi jikin gini ya na bin bayan Eamaan da kallo har ta shige ciki.
"Shegen kaya Yaya sai kwasar dad'i yake ni ina nan na qare a hannun qadangarun bariki, ni da zan samu kamar wannan ai ba zan yi irin taka ba,da daga ranar na bar bariki,"
k'wafa ya yi sannan ya kad'a kai tare da yin murmushin da shi kaɗai ya san ma'anar shi, ya kad'a yatsa ya sa a bakin shi ya gatsa sannan ya shige ciki shima, kitchen ta tafi direct,ta fara hada-hadar hada tuwon alkamar,ba jimawa ta ɗora ruwa ya tafasa, garin niqagge ne wanda yake zuwa a tankad'e, ta d'iba tai rude, a ruden ta zuba kanwa kadan ta rufe, tukunya mai kyau ta ɗora ta kunna ɗaya bangaren na gas ɗin, ta zuba manja ta yanka albasa a ciki ta bari ya soyu, dama ta daka daddawa da kayan miya kafin ruwan tuwo ya tafasa, haɗa su tai ta zuba, suka dan fara soyuwa, sannan ta dakko tafasasshen naman da takan aje a fridge da ruwan naman,ta zuba a kan soyayyan kayan miyar nan,albasa ta yanka qanana-qanana,se ta zuba kayan qamshi da na dandano ta rufe dan ya dahu, sai da ya tafasa kamar na minti 5 sannan ta qara ruwa ta sake rufewa, nan da nan gidan ya ɗauki qamshi, Sahabee ne ya shiga kitchen ɗin yana tafiya a ranqwafe yanda ya saba,direct hanyar sink ya nufa zai ɗauki cup, a yau ya ɗauki aniyar taba qirjin ta dake tsone masa idanu ko ta halin qaqa ne, dai-dai zata juyo kenan da nufin d'akko food flask dan zuba tuwo a ciki kawai taji gaba ɗaya qirjin ta ya daki nashi.
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.