BIYAYYAH PAGE 28

44 6 3
                                    

💅🏼   BIYAYYAH    💅🏼





WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH









Page 28 :




Eamaan ta San kusan dik abinda Anwar ke so, shi ne dalilin da ya sa ta qi yadda a cika mata fuska da kwalliya, ta riga da ta San ba abinda ya fi burge Anwar sama da ya dinga kallon fuskar ta ba wata mashahuriyar kwalliya a jiki,shi a so samun shi ma kar ta shafa komai ta zauna da fuskar ta a haka ya yi ta kallo ya na Jin dad'i, yanzu ma abinda ya mantar da shi cewar a saman hanya suke kenan, ya shagala matuqa wajen kallon fuskar Eamaan Mai d'auke da sirrikan kyau.

'Ga mace har mace, amma na San wannan kunyar ta ta sai ta hana ni sakewa yau d'innan' Anwar ya ayyana hakan cikin ran shi.

A hankali ya fara kusantar da fuskar shi gare ta, idanun ta a rufe ta na sauraron bugun zuciyar shi, ba tare da sanarwa ba ta ji saukar labb'an shi masau taushi da Wani irin d'umi a saman nata, Suma ne kawai Eamaan bata yi ba a wannan yanayin da ya jefa ta, cikin rashin qwarewa Anwar ya fara sumbatar ta, murmushi ta yi a cikin bakin nashi, Wanda ya Sanya shi sake Jin kwad'ayin sumbatar ta, tura shi baya ta yi ta kalle shi ta ce,

  "Da alama ka na buqatar malama, but this is not the right place,mu je gida"

Girar shi ya had'e waje guda fuskar shi still na d'auke da murmushi da Kuma alamar tambaya.

"Malama Kuma? karatun me za a koya wa bawan Allah Anwar?"

"Idan mun je gida za ka gani"

"Ohhhh har na matsu mu Isa"

Kafin ta gama rufe bakin ta Anwar ya tada motar cike da zumud'in son sanin me za a koya masa, ko Ina na jikin shi ya na tsananin bege da qaunar kasancewa da Eamaan a daren yau, be tab'a sanin ya yi hakurin zama ba aure ba se a yau da ya gan shi ga shi ga Eamaan a matsayin matar shi ta aure Kuma halaliyar shi ,jiki na bari yake driving Allah Allah ya ke su Isa gidan, yau se ya ga gidan nasu ya Masa Wani irin nisa, murmushi ta sake yi a ranta ta na tabbatar wa Kan ta Anwar d'in ta sabo ne fill a leda ita zata b'are abunta, godiya ta yi wa Allah da bai sa ta zamo daga cikin mata masu zinace zinace ba,hamdala ta sake yi ga Allah a cikin ran ta da ya bata miji kamar Anwar.

Yau so take ta bashi mamaki kallon da yake mata na ba zai Mori soyayyar shi ba saboda  kunya zata bashi mamaki, d'an murmushi ta sake yi mai sauti, ya juyo ya kalle ta suka hada ido, ta yi saurin sunne kai, ga ni take kamar ya gane ta, a haka suka isa makeken gidan nasu, mai gadi ya bude masu gate,ya sa kai ciki,ko ina fess sai tashin qamshen tiraren wuta gidan yake, irin na sudanis dinnan na musamman Yayah ta ba wa wata qawar ta kud'i aka had'o musu tiraren wuta da humra Mai dad'in qamshi su dika ukun, sannan ta zaba mata tiraren wuta na tsinke masu dadin gaske, lumshe ido ya yi ya zagaya bangaren da take ya bud'e mata murfin qofar hannun ta ya kama ya rungume ta tsam a jikin shi suke takawa a tare,Eamaan na sane ta manne fuskar ta a cikin jikin shi take goga wa a hankali tana aika masa da saqon da ita kad'ai ta San kalar shi, bawan Allah Anwar a tunanin shi tsabar kunya ce ta Eamaan ta Sanya ta rufe fuska a jikin shi, shi dai ya San kunyar nan se ta hana shi sakewa yau.

Suna nan rungume da juna suka isa har dakin da ya ke shine a matsayin turakar shi, a bakin gado ya zaunar da ita, ya sunkuya, ya na cire mata takalmin ta, yana shafa lallen da aka zana mata mai kyau a qafar ta mara kaushi balle Faso (qafar matan novel irin Dijeena) kallon shi kawai take Ido  cikin ido, ko qiftawa bata yi, wannan kallon ya qunshi tsantsanr so da qauna,da kuma nuna masa yanda ta kwadaitu da shi itama, se da ta tabbatar kallon ya shige shi ta yi saurin saukar da Kan ta qasa ta na murmushin Jin kunya, Eamaan fa ta gama birkitawa Anwar lissafi, a hankali taga yana yo sama wajen ta, dakatar da shi tai,

" Habaa Daddyn Fateema, kamata ya yi ai mu fara gabatar da nafilar gode ma Allah ko, dan ko da ba a nafilar godiya ga Allah, ina jin mu ya Kamata mu yi a daren yau, dan Allah ya gama mana komai daya mallaka mana junan mu,"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now