BIYAYYAH PAGE 2

60 8 1
                                    

💅🏼  BIYAYYAH  💅🏼




WRITTEN BY: HAERMEEBRAERH



page 2:

Hidimar biki ta kankama ka'in da na'in,komai da ya Kamata a sai wa amarya Kuma a Yi wa amarya an Yi wa Eamaan, tasha gyara wajen Amman ta sosai, gyara kuma bana wasa ba, duk wanda ya kalle ta sai ya qara,Amma  ta yi iya yin ta Dan Eamaan ta dawo da jikin ta amma abun ya faskara, dik da kuwa  samata abincin da  take a gaba ta tsare ta sai ta  cinye, all in vain Eamaan na nan a rame saboda damuwa,ita dai  ga ta nan ne dai kawai, 'yan uwa da abokan arziqi sun hallara, domin gudanar da shagulgulan bikin da aka tanadar, wasu da suka san ta da Anwar sun matuqar tausaya mata, amma ba mai jajan tawa saboda yanda kullum take cikin kuka, a fuska da ka kalle ta kamar mai shirin fasa ihu, haka take a Koda yaushe  cikin quncin zuciya, Hafsat kullum sai ta taushi zuciyar ta amma bata samun wani sauqi, se dai ta na samu ta kwanta a jikin Hafsat d'in da Amman ta ta Yi ta kuka a jikin su.

Daga lefen da aka kawo kowa yasan gidan da za a kaita ba na wasa bane, wasu a unguwa cewa suke Daddy ya saida ita ne ga dan siyasa, wasu suce kwadayi ne irin na masu kudin yanzu suna da shi sai sun qara, ba wadatar zuci, masu fahimta ne suka san qaddara ce ta sauka akan ta, kuma sukai mata fatan wanyewa lfy,( ko ina ruwan masu cece kuce din oho). An daura auren Eamaan da Alhaji Abdullahi, taron daurin auren da ya qunshi manyan mutanen qasar mu Nigeria, motoci a layin har rasa wajen tsaiwa suke, Daddy kam bakin shi yaqi rufuwa, dan murna yake da aurar da diyar shi ma  dan siyasa a karo na biyu.

Yan kai amarya na gano baki sake suna kallon gidan da aka kai Eamaan kowa sai san barka yake, qawayen Hafsat ne ke mata tsiya,

" babe yanzu da kin yarda da tini muna zuwa ganin wannan makeken gidan, muci arziqi mu bar shi inda yake,"

" hmm baku da hankali, itama fatan Allah ya kubutar da ita daga sharrin dake tattare da wannan gidan nake,"

A haka kowa ya dinga watsewa ana ma amarya fatan alkairi, bangaren ta ya rage ba kowa sai ita kadai, kafin su tafi saida suka qara gyare mata gidan tass ko ina sai daukan ido yake, komai na gidan pink ne da ratsin fari, gidan ya mata kyau sosai,rufe idon ta tai wasu hawaye suka zubo mata, wannan rana sun dad'e suna tsara ta ita da Anwar, gashi zata yi ta a wani gidan, gidan da bata tab'a mafarkin aure a cikin shi ba,

" Ya Allah na roqe ka dan kyawawan sunayen ka tsarkaka,Allah ka ciren damuwar komai a raina, ka bani iko da juriyar yiwa mijina biyayya da mahaifiyar shi, Allah ka bamu zaman lfy da abokan zamana, sharrin dake tattare da cikin gidan nan Allah ka kare ni da shi, ka hada ni da alkairin dake cikin gidannan ya raheem,"

Fashewa ta yi da kukan da ya taso mata, na kadaici, ji take duk duniyar ita daya ce, ta rasa kowa nata, Anwar shine kowa nata, tabbas rabuwa da masoyi akwai ciwo akwai azaba, gashi tana d'and'anar hakan, gani tai har sha daya bai shigo ba ta miqe taje tai wanka, tai brush, ta gyare gashin ta, ta fito, tana fashin sallah, zuwa tai ta tofe qofar shigowar da addu'a ta dawo tai addu'ar bacci ta shafe jikin ta ta ja abun rufa, ta kwanta, bata jima da kwanciya ba ko bacci ya dauke ta mai dadi, mai cike da mafarkai barkatai wanda ba zata iya tantance su ba, cikin baccin taji ana shafa ta, firgigit ta miqe tana tsilla idanu, Alhaji ta gani, cikin qananan kaya, tsufannan ya boye,sai sheqin angonci yake, komawa tai ta ja abun rufan ganin sai kallon ta yake yana hadiye yawu, duqawa tai da Kan ta ta gaida shi ya amsa, kanta a qasa bata qara cewa komai ba, tana jiran taji daga gare shi, ledar dake hannun shi ya miqa mata yace taci kan ta kwanta, dan ya ga alamar bacci take ji,ya hakura sai Wani lokacin kuma.

Sanar da ita ya Yi cewar sun yi magana da sauran matan a babban parlorn gidan za a taru in safiya ta Yi, parlourn ya na ta can bangaren mahaifiyar shi ne,dann haka itama ta shirya tare za su je in safiya ta Yi,daga masa kai tayi sannan ta furta,

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now