BIYAYYAH PAGE 25

55 7 0
                                        

💅🏼    BIYAYYAH.   💅🏼




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH



Page 25:



Kukan murna Eamaan ta yi sosai kan ta ɗago da idanun ta da suka sauya kala daga farare tas zuwa launin ja, haqoran ta farare wanda suke a jere ɗauke da siririyar hushirya sai haskawa suke, Hafsat da ta matsa kusa da ita tana shafa bayan ta da sigar lallashi ta kalla, itama murmushin ta sakar mata Fatee kuwa na ta kallon ta da mamakin dalilin kukan nata, Eamaan ce ta ce,

" Yah kamal me kake so a matsayin goron albishir d'in da ka min yanzu?"

" Ba abinda nake so illa kafin nan kafin ki tafi ki koya ma Hafsat duk girke-girke  da kike yi mana masu dad'i, sannan kuma a bar mana Fatee har tsawon lokacin da kuka gama cin amarcin ku sannan ku karɓe ta, ke in ma Anwar ba zai d'auke ta ba ni nayi tayin riqe Fateema har abada a matsayin ta ƴata"

Farin ciki ne ya qara sanya ta kuka sosai mai cike da murmushi, lallai Yah Kamal na son Hafsat sosai, dan ta kula yana taya Hafsat son duk abin da take so, ko baya son abun nan indai ta na so to fa Shima abun nan ya zama abin son shi,lokuta da dama shi da Eamaan sukan zauna su yi ta gulmar Hafsat d'in, su Kan yi magana da Eamaan akan shi fa baya son kaza a da amma tinda ya kula Hafsat na so ya ji ya fara son abun.

" Yah Kamal kome kake so zan yi maka,kai daga yau ma zan fara inshaa Allah, game da Fatee kuma shi fa Anwar cewa ya yi da ita za mu tare duk sanda Allah ya sa muka yi aure, amma dole zan lallab'a shi mu barta ko wata biyu muka yi an maida ta yanda dai ya amince,"

Kamal ne ya kalli Hafsat da farin ciki ya bayyana a fuskar ta ya matsa jikin ta ya dora kan ta a gefen jikin shi dan itan tana zaune a hannun kujera ne kusa da Eamaan da ke kukan farin ciki sannan yayi kissing goshin ta, a tare suka yiwa Eamaan godiya tare da fatan Allah yasa Anwar ya bar musu Fateema su riƙe ta na tsawon lokaci.

**************************
Anwar na qara murmurewa ya sa aka je gidan shi sabo aka gyara shi fes, dan ba abinda bai zuba ba na more rayuwa dai-dai qarfin shi, komai yayi masa yanda yake son shi, gidan na ɗauke da d'aki hud'u ne sai palour biyu, dinning area ɗaya, kowanne d'aki da toilet ɗin shi, sai Kuma toilet guda d'aya a harabar gidan, gidan ya na da  farfajiya mai girman da zata Iya d'aukan a qalla mota uku, a can bayan gidan Kuma ya yi dan garden me d'auke da kayan wasa na yara wanda manya ma zasu iya hawa lillunan wajen, gidan yayi matuƙar haɗuwa gwanin sha'awa,yana tafe ya na kallon  yanda aka tsara gidan ne ya ji qarar saqo a wayar shi, daya duba sai yaga No Kamal ne ta turo mai wata Number waya a qasa an  rubuta *Ur sweetheart No* wani dad'i ne ya kama shi, dan dama yana son ya aika kuɗi yace kamal ya sai mata waya mai kyau amma da alama Kamal d'in ya riga shi, shi kuwa me zai yi ya biya Kamal kyautatawar da yake yi masa, saving ya yi da 'My one' ai ko yana gamawa ya shiga ɗaya daga cikin palourn ya qame a kujera ya danna kiran layin na ta, Eamaan na can na ta faman koyawa Hafsat girki ta ji wayar ta na ringing wanke hannun ta tayi ta d'aga tare da yin sallama a zuciyar ta tana mamakin waye wannan da ya samu No ta sabuwa haka? Iya sanin ta ba kowa ne yasan tana da waya ba.

Ajiyar zuciyar da ya sauke ne da ƙarfi ya sanya ta dafe jikin cabinet na kitchen ɗin ta jingina dashi tana murmushi mai sauti, Hafsat na ganin haka ta daki kafadar ta ta ce,

"Sarakan soyayya bari na kwab'a na yau na tara  a gaba, na San yanzu ko wuqa zan caka maki ba ji Zaki yi ba,"

Fita ta yi ma daga kitchen d'in kwatakwata ta tafi d'aki ta kwanta a gado ta mimmiqe ta na sauraron muryar Anwar d'in da ke ratsa dik wata kafa ta jikin ta.

"Kin san me?"

" A'a sai ka fada"

" Ina gidan mu yanzu haka,inda zamu zauna ni da ke da Fateema nake nufi,ina kan doguwar kujera a kwance nace bari na kira ki naji muryar ki,yanzu iwar haka inshaa Allah wani satin kina gefe na a kwance muna hira ko?"

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now