BIYAYYAH PAGE 29

109 10 2
                                    

💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 29:

A babban palourn gidan su Eamaan suka yi masauki,  iyayen su Eamaan har ma da ma'aikatan su sun yi matuqar farin cikin ganin Eamaan d'in,ta  yi irin qibar nan Mai kyau ta sabbin amare ga Wani irin haske Mai ban sha'awa da ta qara, atampar da ta Sanya Mai dinkin doguwar rigan da ta sha stones ta karbe ta, gaishe da Mama suka yi tana murmushin Jin dad'in ganin masoyan da suka yi matuqar dacewa da junan su.

"Ai da na ji shirun ya yi yawa na ce wa Ammaahn ku zan je in ga ko 'yata na lafiya, ba zuwa ba waya shiru shiru, se ta ce ai lafiya ke b'uya to shi yasa baku ganni a gidan naku ba "

Kunya ce ta kama Eamaan cikin jin kunya ta ce,

"Mama muna nan lafiya qlou, kin san dake auren an yi shi cikin hanzari wasu basu sani ba se daga baya to baqi Muka dinga yi, abokan shi da 'yan uwa haka suka yi ta zuwa yau ma cewa mu ka yi bari mu fito da wuri Duk Wanda ya je ya ga bama nan ya yi hakuri se watarana"

"Eh to da wannan Dan wannan ma dama haka ne, gidan amare baya rabo da baqi"

Ammaah ce ta fito itama ta zauna aka hau gaisawa, Anwar na ganin surukar tashi  yayi saurin duqawa da kyau ya gaishe ta,a kunyace ta amsa,

" Ashe kuna tafe, to sannun ku da zuwa Allah yayi muku albarka,gashi Daddyn naku baya nan,"

"Ai muna nan se dare...ni kam Amma ina Iya ne,ban ji duriyar ta ba,"

Mama ce ta amsa ta da cewa

"Ai Iyan ki ta kafe ba za a sa ta a Wani gidan ba a aje ta anan Kuma  a nan d'in ma a bangaren masu aiki zata zauna, mun yi-mun yi ta zauna a dakin baqi amma taqi, wai tafi son can,"

"Allah sarki Iya, ai shikenan Allah dai ya qara lafiya, Kuma har yau Sahabee be zo neman ta ba ko?"

"Be zo ba, ba Wanda ya zo neman ta, uhmmm ya wajen su Hajiyan taku,"

Cikin ladabi Anwar ya amsa da,

"Suna lafiya, yanzu ma seda mu ka biya ta can suna gaida ku sosai,"

" Muna amsawa Kuma muna godiya,"

" Abu Fadheemah muje mu ga Iya kan ka tafi ko? Anjima sai ka zo ka d'auke ni,"

Tashi suka yi tsaye Eamaan ta Maida mayafin ta,suka fita  dan zagayawa ta kitchen su je wajen Iya, su na shiga kitchen d'in ya ga ba kowa sai ya kama qugun ta, da sauri ta jujjuya ta na kallon kowanne gefe kar Wani ya gan su a haka, buge hannun shi ta yi har da Wani d'an cije lebe

"In wani ya gan mu fa,"

"Sai in ce ke ki ka ce na d'auke ki kin gaji da tafiya...baby ba maganar wasa ba tin a gida nake kula da ke gaba d'aya kin sauya  kamar baki da lafiya ko kin gaji, ina jin zan zo da wuri na maida ki gida dan ki samu ki ware kan gobe tafiya, ko kina ganin mu jinkirta tafiyar sai kin huta? Abubuwa sun maki yawa ko da yaushe cikin aikace-aikace ki ke?"

Girgiza masa kai ta yi, alamar a'a, tana matuqar jin dad'in yanda yake kulawa da ita, yake son sata farin ciki a Koda yaushe.

"Kar ka damu I am ok, mu je ko?"

Suna isa qofar dakin Iya ya duqa ya cire takalmin shi, ita kuma ta shiga ciki, sanan shima ya bi bayan ta,Iya zaune take akan abin sallah, ta yi 'yar qiba abinta a cikin wata d'aya,da yake dama can ita me jikin qiba ce, to komai take so shi take ci dole kuwa ƙiba ta samu muhalli,uwa uba kuma ga kwanciyar hankali ya same ta, banda tinanin halin da Sahabee yake ciki ba abinda ke damun ta a yanzu,su Hajiya Iya se tasbihi ake yi, juyowa ta yi tare da fad'ad'a murmushin ta tana kallon Anwar da Eamaan,addu'a ta yi ta shafa, sannan suka shiga gaisawa, cikin fara'a Iya tace,

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 15, 2024 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now