BIYAYYAH PAGE 26

53 7 0
                                        

💅🏼      BIYAYYAH   💅🏼


WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

Page 26:

A hankali Amarya ta maida Sahabee tamkar wani bawan ta, domin kuwa dik wani aiki da ya kamata a ce itace take yin shi sai ta mayar masa da shi aikin shi,shine shara, wanke-wanke,girki, d'iban ruwa da wankin kayan su,a dik sanda yayi girki taci taji bai yi mata daɗi ba yanda take so sai ta sa shi ya siyo a waje.

Yana matuƙar wahala wata yazo ya wuce bata je biki ba, babban abinda yafi ƙayatar da ita a zuwa biki shine ɗinka anko,wannan shine babban dalilin da yasa ta ƙware wajen yawan roqon kud'i,abinda dik ya bata da shi zata sayi anko tayi ɗinki idan ya ragu ta kaiwa bokan ta ya qara kafe mata shi ta yanda sai abinda tace yayi kawai zai yi, dik kuma abinda bata so to fa bai isa ya aikata shi ba.

Wajen shaye-shayen magungunan mata kuwa an bata lambar yabo dan kuwa ƙwararriya ce a wannan fannin tinda ta gama gano lagon sa,indai  zai samu biyan buƙatarsa to fa komai zata yi masa baya gani,kan kuce me Sahabee ya tashi daga d'an gaye ya koma Wani iri da shi kamar d'an aikin gidan dama can shi ba me kaurin jiki bane se ya sake jemewa ya rame sai uban tsawo kamar igiya,gaba ɗaya ya zama wani abin tausayi da shi.

Tsakanin uwa da ɗa sai Allah,ganin halin da ya shiga ne ya sanya ciwon Iya yake yawan tashi, Sahabee bai ma san tana yi ba balle ya sai mata magani, watarana har kasa tashi take yi ta fita koda yin alwala ne.

Idan abun ya yawaita ne yaga be ga gilmawar ta ba na kwanaki sai ya ɗaga labule daga bakin ƙofa zai yi mata sannu sannan ya kama gaban shi ya shiga sabgogin shi kamar bai ga halin da take ciki ba,matar shi kuwa sai suyi kwanaki bata leqa ta ba balle ta duba ya jikin ta yake, lokacin da ta ga damar gaishe ta kuwa to daga bakin qofa take d'age dan buhun labulen itama ta ce mata sannu ta yi gaba abunta,a cewar ta ai uwar miji ba uwar ta bace.

Babban abinda yafi baƙantawa Iya rai bai wuce yanda matar nan zata kalli idanun Iya ta dinga kiran ta da ƙazama wadda bata share ɗakin ta balle tayi wanka taji dad'in jikin ta,Iya ta yi nadamar abubuwan data dinga yiwa Eamaan a baya, gefe ɗaya kuma ta yi nadamar yanda ta dinga yiwa Alhaji Abdullah da yake tsananin tausaya mata da taimaka mata tare da yi mata ladabi da BIYAYYAH,a kullum ba shi da burin da ya wuce na ya ganta cikin walwala da farin ciki, duk dan kar ran ta ya baci da girman shi haka zata sa shi a gaba da fad'a kamar yaro qarami, ga masu aiki wajen uku ya zuba mata ita kaɗai a sashen ta dan su kula da dikkan buƙatun ta, amma dik da haka ta takurawa matar shi mai tsananin BIYAYYAH dik da cewa ba auren soyayya suka yi ba, idan tace masu abu fari ne komai baqin shi basa yi mata musa haka zasu yarda da abinda tace ɗin.kuka shine ya dawo abincin Iya Kuma ya zamto abin Shanta.

Idan ana girki a gidan haka hayaƙin zai shiga ta ɗan ƙaramin windown nata tai ta tari tana neman iskar shaƙa mai kyau, dik randa tayi gigin fita dan ta shaƙi iska amaryar sahabee sai ta nuna mata bariki ta hau taɓa shi a gaban idanun ta shi kuwa yana biye mata,tsananin da Iya ke ciki yayi tsanani har ya kai ga yanzu bata gani sosai saboda hawan jini da yayi mata yawa da kuma hayaƙi dake addabar ta kullum.

Muryar Amaryar Sahabee ke tashi kamar wata gardi a cikin gidan cikin ɓacin rai take magana.

" Yanzu honey kana nufin bashin da na ciwo saboda ankon bikin qawata ba za ka samu biya ba? kai fa ka yi min alqawari kafin auren mu ba zan tab'a neman abu na rasa ba kace min babu ni babu wahala aikin gida da komai ba nawa bane naka ne, sannan ka jaddada min kar na damu da maganar kud'i ko nawa ne baka da matsala akan su zaka dinga bani,ni ba ma abinda ya fi min ciwo ma sama da alqawarin zama a qaton gida bayan d'aura mana aure sai na ga an kawo ni nan, hakuri kawai na yi na rufa Maka asiri wajen dangi na da qawaye na muke zaune a wannan akurkin, domin rufin asirin ka shine nawa,se yanzu na gane duk Kalaman ka a gare ni qanzon kurege ne,tin yanzu gashi ka fara karya alƙawarin ka na bani kud'in anko a duk sanda na buƙata,to ka buɗe kunnen ka da kyau kaji ni,wannan ankon da na ciyo bashi se ka biya ba zaka sa na ji kunya ba,dubun nan talatin da bakwai cassss se ka kawo su,sannan ga kudin ɗinki dubu biyar da aka yo min,dole ne ka biya kud'in takalmi da jaka da mayafi da na sa qanina ya amso bashi a shagon abokin shi, ba zaka sa na ji kunyar qanne na ba a dinga raina ni ana zagin miji na ana kiran ka talaka,sarqa da dan kunne da abun hannu da zan yi amfani dasu Kuma ka siya daga baya kafin ranar bikin tazo.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now