BIYAYYAH PAGE 19

51 10 1
                                    

💅🏼    BIYAYYAH   💅🏼








WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







Page 19:







Sahabee ne da Iya zaune suke ta zabga kukan rashin Alhaji Abdullahi da aka yi, gaba d'aya parlourn kallon su kawai ake yi babu wanda ya tausaya masu sai ma haushin su da kowa ke ji a wajen, amma saboda karamci irin na su Ammaah ko a fuska ba su nuna masu ba, daga Daddy har mama kowa ya gaishe da Iya yayi mata ta'aziyyar rashin ɗan ta da tayi,Eamaan na ganin su wani tuquqin baqin ciki ya taso mata, kawai sai ta nemi waje ta zauna tana bin su da kallo, dan kuwa ita gani take yi ta sanadin abinda Sahabee yayi ne ta rasa mijin ta,Iya kawai ta gaida saboda kasancewar ta mahaifiya ga Alhajin ba dan haka ba ko kallo bata ishe ta ba,

" Ina wuni,"

Ta furta tare da komawa gefe ta zauna a kujera idon ta rufe dan ko ganin su ba ta son yi, amsawa Iya ta yi tana ta zuba tana fad'an a inda suka ji rasuwar,shiru wajen ya ɗauka babu wanda ya ce mata ci kan ki,kalma ɗaya kowa ke amsa masu da Ameeen idan suka furta Allah ya jiqan Alhaji.

Eamaan kam ma ko kula su bata yi ba balle ta amsa Ameen ɗin ,tana kyautata wa Allah zato ya gafarta wa Alhaji kuma zai yi masa rahama da yalwatacciyar rahamar shi,suna nan zaune banda maganganu da kukan Iya dake tashi baka jin komai a haka aka kawo Fatee tana ta kuka, Eamaan ce ta karɓe ta tana ta jijjiga ta a hankali ta samu ta yi shiru, Ammaah ce ta kawo mata abinci ta ɗauke ta tana bata, can a cikin surutan Sahabee  su ka ji yana fad'in

" Allah ya jiqan Yayah, tin da abubuwa sun zo a haka kuma Fatee ita kad'ai ta rage mana a dangi da zamu kalla muji dad'i, sai a had'a mana kayan ta mu tafi da ita,"

Cikin sauri Ammaah ta ajiye Fateema a cinyar Mama ta yi kan  Eamaan ta riqe ta tana yi mata magana cikin sanyin murya,Ammaah ta tsorata da yanayin da taga 'yarta ta ta shiga cikin qanqanin lokaci, yanayi ne da tinda ta haife ta bata taɓa gani a tattare da ita ba, jikin ta sai rawa yake yi, idonta kuwa ya yi jawur kamar jan yadi, tashi tayi tsaye Ammaah na riqe da ita ta fara takawa tana bin Sahabee da wannan deadly look din nata, cikin sauri Sahabee ya ja gefe kusa da Iyaa yana zaro idanu, bata ce wa kowa komai ba ta shiga ɗakin ta, Ammaah ce ta basu hakuri tana qoqarin bin bayan Eamaan ɗin sai gata ta fito ɗauke da leda a hannun ta ta wurga ta a fuskar Sahabee, abinda ke cikin ledar ne ya leqo,nan fa sahabee yayi arba da kuɗi sai ya hau zare ido yana washe baki,

" ku tashi ku fita da ragowar abinda ya yi saura na ɗan uwan ku a wajena, na yafe gadon shi bana so ku haɗe ku cinye dika dan shine dama ya fiye maku ɗan ku, d'iyata in ta girma kun bata nata a hannun ta in kuma kun cinye kun bata a lahira,ni ba zan karb'i gadon ta ba ba kuma za ku bar shi  a hannun dangina ba, marasa hankali da imani kawai, kutashi ku fice nace !!!!"

Cike da wata gigitacciyar tsawar da ko iyayen ta basu taba jin ta yi irin ta ba ta qarasa maganar ta,ai kuwa tayi matuqar kid'ima kowa a wajen, ba shiri Sahabee ya tattare kud'ad'en ya mayar ledar ya kama Iya suka bar gidan hankalin su a tashe, daf zasu fita ne ya juyo yace,

"ko ba jima ko ba dad'e sai Fatee ta dawo hannun mu,"

"Naga dan iskan da zai ɗaukar min yarinya ya kaita gidan tsohuwar da bata san ya zata baiwa kanta tarbiyya ba balle yaran ta su tashi cikin son junan su ɗaya bai yi sanadin rasuwar ɗaya ba, har ta samu damar yi wa jikar ta tarbiyya ta zama yarinyar kirki bata sanya ta zama karuwa ba kamar yaran ta,"

A kunyace Iya ta sa kai tsakar gida ta ja hannun Sahabee dan su bar gidan,shiru gidan ya ɗauka dan kuwa babu mai bakin magana Eamaan ta baiwa iyayen ta da suka haife ta suka raine ta mamaki ma balle kuma wanda suka same ta da girman ta, shi yasa bahaushe ke cewa a kiyayi fushin mai hakuri.

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now