💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 13:
"Me ya shigo da kai har cikin bedroom ɗin mu Sahabee?"
" Ah Yayah dama kana nan, ai na yi ta sallama a can parlour na ji shiru kuma da fari na ji kamar hayaniya sanda na shigo ana daga muryoyi,to da nai ta sallama na ji shiru shi ne yasa na zaci ko wani abu ne ya faru kawai na shigo kai tsaye,"
wani irin kallon ka raina min hankali Alhaji ya yi masa sannan yace,
"Babu komai to je ka kawai,"
Hajiya Babba ce ta fito daure da towel, tana ganin Sahabee ta daburce bakin ta ya hau rawa tana son tayi magana ta kasa, nan da nan Alhaji ya sak'awani zargi cikin zuciyar shi game da abinda ya faru,shin me ya sanya qanin nashi shigowa kai tsaye ba tare da neman izini ba? Me yasa Hajiya rikicewa daga ganin Sahabeen a d'akin tin kafin ta san dalilin zuwan shi? Ɗauke kallon shi ya yi daga na ta, ya yada jikin shi kan gadon ya rufe idon shi yana tinani, a gaggauce ta saka riga ta fita waje, a farfajiyar gidan ta ga Sahabeen ya na ta Kai wa da komowa, cikin faɗa Hajiya tace masa,
" kai wanne irin soko ne Sahabee, me ya kai ka zuwa yanzu?"
"Ina zaune a d'aki ne kika fad'o min a rai sai na ji ina buqatar ki ko na minti gomane,to da yake d'azu na ga shigar shi wajen waccan yarinyar na san zai dad'e, Iya na can ta sani a gaba da zance bana ma gane ina ta dosa,to shine yanzu da ta shiga ciki ta kwanta dan ta huta kawai na yo nan, ban zaci ya dawo ba,"
Hararar shi ta yi,Sannan ta ce,
" kai wane irin shiriritacce ne, amma dai kasan a qa'ida in yana nan baka zuwa ko so kake yi asirin mu ya tonu ne,"
Sosa qeyya ya yi ya sunkuyar da kai ,ita kuwa sai ta buga tsaki ta juya ta yi ciki, Alhaji duk yana kallon su ta window yana ayyana abubuwa da dama akan su, tana shiga sashen nata ya koma ya kwanta, duk da baya jin hirar su saboda tazarar dake tsakani,kallo ɗaya zaka yi musu ka gano akwai wani abu dake wakana a tsakanin su, Idon shi ya rufe kamar yanda ta bar shi, ta koma ta ɗauki mai ta fara shafawa a jikin ta da ya bushe.
Hajiya Qarama ce kwance a gado tayi ruf da ciki tana waya cike da Jin dad'i kamar wata budurwar da ke yin hira da saurayin ta.
" Yanzu kana ganin za ka kai wani satin a gari ne?"
" A'a gaskiya ina jin jibi ma zan koma, akwai matsala ne, ko kina son ganina ne?"
" kwarai da gaske ina son ganin ka, dan akwai magana mai matuqar mahimmanci da za mu yi da kai,"
"To shikenan sai ki samu lokaci ki fito mu gana ko,"
Sai da suka taba zantukan su na lalacewa kafin daga baya su yi sallama da juna, cike da fargabar me zai je ya zo ta yanke shawarar yanda za ta fita, ita zata karbi girki da dare dan haka ran ta kwal tana ta murna zata samu damar tambayar fita unguwa, Alhaji kuwa fatan shi bai wuce ace tayi wanka ta yi brush kafin dare, ga mace har mace amma ba gyara, dan gaskiya Hajiya Qarama bata da muni ga jikin ta mai kyau sai baqar qazanta da wari.
A haka lokacin komawa sashen ta yayi sai ya tattara ya dawo bangaren ta, ba laifi tayi wanka tayi brush harda su sabon kitso,amma fa gaba ɗaya bata qamshi gata nan ne dai kawai a lallab'a auren zamani,a wannan karon Alhaji ya sha karairaya da gata dai-dai iyawar ta, har suka yi shirin kwaciya bacci,sai da komai ya gama kan kama ana soyayya warin hammatar ta duk ya cika masa ciki saboda sai ya zamana kamar tana aikin qarfi ne tana haɗa zufa warin na fitowa, cikin fada ya fara yi mata magana,
"Wai ke sau nawa zan yi maki magana ne akan kina amfani da turaruka a jikin ki ne ? Ga su nan da yawa har ban san iya adadin su ba saboda naki ma na musamman nake siyo maki amma ke sam baki san meye amfani da tirare ba ko saka abun da zai ɗauke warin hammatar ki kamar Alimun ko lemon tsami, sai dai ki zauna kina wari malam meye hakan?"
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.