💅🏼 BIYAYYAH 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 9:
Ga yawan kasala, tafukan hannayen shi da qafa sai su kumbura, fuskar shi ma ta dan hau, sai yawan jin qaiqayi da yake a jikin shi,wasu quraje na fito Masa qanana,in ya je fitsari da kyar yake Iya yi, rabon shi da Kashi kuwa ya kwana biyu, abubuwa dai sun taru sun mai yawa.
Randa zasu asibitin, ya kama ranar girkin Hajiya Babba ne, ta sha kwalliyar ta kamar yanda ta saba, suka shiga mota ita da Alhaji, a baya, Sahabee da driver a gaba, suna zuwa aka bashi gado, likita ya rubuta Masa sun gwaje2n da ya Kamata a Masa, Dan akwai ciwon da yake zargi duba da ciwukan da ya ke tattare da su, gwajin farko kuwa suka gano gaba daya qodar shi sun samu matsala, d'aya ce kawai me sauqi sauqi,ita akwai yuwar in ya sha magunguna aka wanke Masa ita zai iya samun sauqi, hankalin iyalin na shi ba qaramin tashi ya yi ba,da jin wannan labarin, kowa ya shiga damuwa, a haka likitan ya bashi duk wata kulawa da ya Kamata a bawa Mai irin ciwon.
Iyalan Alhaji Abdullahi su na iya bakin qoqarin su dan bashi magani akan lokaci da bashi kulawar da likita ya umarta, duk da sun so matuqa a fita waje da shi, likitan ya musu alqawarin za su bashi kulawa kamar ya na qasar waje,abokan shi na siyasa sun shiga damuwa Suma duba cewa kusan shi ne jigon jam'iyyar tasu, gashi mutane na son shi da girmama shi, addu'a suke da fatan Allah ya tashi kafad'un shi.
Matan Alhaji kuwa shifting din zama a wajen su suka fara yi kamar ma'aikatan gwamnati, in girkin wannan ya fita wannan ta zo, duk ran girkin Eamaan ranar sahabee fa ba shi a zuwa asibiti, dan tinda abunnan ya faru yake toshe duk wata kafa da zata had'a su waje guda.
Wata rana Iya ta kira Eamaan, duk da cewar washe gari ne zata karbi girki, kimtsawa ta yi ta saka hijab din ta, ta fita wajen Iya, tana zuwa ta tadda ta da himilin rake a gaban ta,Eamaan zama ta yi ta tankwashe qafa,ta gaida Iya,
" Ba gaishe2 ne ya sa na kira ki ba ni, ammmm kina jina ko, wannan raken nake son ki samu ki markaden shi ki tacen ruwan, kamar yanda najiki a waya rannan kina gayawa wata,jarababbiya kamar ki wai har kin san hada maganin mata da rake, to ni na lafiya zaki hadawa dana, kina jina ko,ki markad'e shi kar ki sa mai wani kayan qamshi da madara, kawai zallan ruwan nake so , a saka a jug a kai masa ya shanye, naji ance yana wanke qoda shi ruwan raken,"
kanta a qasa cike da takaicin abubuwan da Iya ke mata, ita ake mora amma ita ce sharar zubarwa, fuskar ta cike da murmushi da annuri ta dago,
" wai ke bakya fushi ne?"
" Iya dawa zan fushin? Da ke? Allah ya sawaqa Allah kuma kar ya nuna min ranar, domin kuwa ke uwa ce a wajena, d'an kirki kuwa baya fushi da iyayen sa sai ya zama marar rabo duniya da lahira, kuma ni na tabbata ba wai so na ne baki yi ba, wataqila wasu daga halaye na ne baki so, inshaa Allah zan qoqarin gyarawa na zama d'iya ta gari me neman albarkar ki a koda yaushe, in kuma abubuwan da kike man dan kawai ki baqanta min ne, kina son ganin fushina, Hmmmmmm Iya kar Allah ya nuna maki fushina,"
Ta qarashe maganar ta cikin wani murmushin da ya sa Iya Shan Jin jikin ta, ka kawai ta ji yarinyar ta mata kwarjini matuqa, kalamanta akwai hikima, kuma a kwai tsantsar gaskiyar abinda ke ran ta, had'iye yawu Iya ta yi makwattt, ta jingina da jikin kujera, tabi bayan Eamaan da ke cike da mazaunai da kallo, tana karantar wasu abubuwa daga halittar ta,kauda tinanin ta yi ta miqe ta shige daki.
Eamaan na gama had'a ruwan raken a jug ,ta yi sallama d'akin Iya ta fada mata, Iya kuwa cewa ta yi ta ba Sahabee ya kai asibitin, ta amsa ta fita, a yanzu jikin Iya a sanyaye yake da Eamaan, shakkar mata rashin mutunci direct kamar yanda ta saba take, dan kuwa da dane sai ta yada mata da baqar magana, fita ta yi farfajiyar gidan riqe da jug a hannu, wanda ta saka cikin wata leda babba mai kauri, tana leqa wurare ta na neman Sahabee, tinda bata gan shi a dakin shi ba ko da ta duba shi can,hanyar backyard ta yi dan da damar lokuta yana zama wajen, daidai bangaren Hajiya Babba, ta ji nishi,irin na nishad'i, mamaki ne ya kama ta,dan tasan dai Alhaji na asibiti,amma kusan muryar shi ta ji, sannan wannan daya muryar tabbas ta hajiya Babba ce, meke faruwa? Qara matsawa ta yi sosai, ta jikin window ta ji magana,
YOU ARE READING
BIYAYYAH
RomanceRabuwa da masoyi babban ciwo ne Wanda maganin shi...shine hakuri da sadaukarwa...sadaukarwa da BIYAYYAH ita ce tushen faruwar komai a rayuwar Eamaan.