BIYAYYAH PAGE 23

46 10 0
                                    

💅🏼  BIYAYYAH.  💅🏼




WRITTEN  BY HAERMEEBRAERH


Page 23:


Da sassafe ya shirya dan  zuwa kano, ya matsu ya ga manyan shi dan su shiga maganar auren su da Eamaan, a bari ya huce shi ke kawo rabon Wani in ji bahaushe, sanyin jiki da Jan jikin shi na daga abinda ya ja masa rasa Eamaan a baya,wannan karon kuwa ba zai yi qasa a guiwa ba wajen gabatar da Kan shi da wuri.

Bayan ya gama shirin tafiyar shine tsaf, ya dakko jakar shi da zai tafiya da ita ya saka a mota, ya na so ya fara biya wa ta asibiti ya duba marasa lafiyan da ya yi wa aiki shekaran jiya ka fin ya wuce,asibitin shi na da kwararrun likitocin da ko baya nan za su kula da komai magana  ya yi ma Baba mai gadi da mai share share akan su kula da gida, ya musu  sallama tare da damqa masu kud'i a hannun su ko da zasu buqaci Wani abun baya nan, Anwar mutum ne Mai tausayi da kyautayi, ba ruwan shi da Yana biyan su albashi kullum cikin kulawa da su yake baya gajiya.

Direct gidan su Hafsat yaje ya tsaya a waje ya yi ma Kamal waya,ya sanar da shi abinda yake shirin yi, Kamal kuwa sai ya bashi goyon baya d'ari bisa d'ari,tare da qarfafa masa guiwa, sannan yace ya shigo su gaisa da Eamaan mana kafin ya wuce, shiga cikin gidan yayi ya jira Kamal ya bud'e masa qofar parlour ya shiga da sallama.

Hafsat ce ta fito sanye da babban Hijab, dan cikin ta ya fara girma ba laifi, gaisawa suka yi ta wuce dakin Eamaan dan Kiran ta, karo suka yi a hanya ta miqe hannayen ta ta na miqa, dan ta gama sakankancewa Kamal ya fita tinda takwas ta gota, Anwar dake hango Eamaan da ke miqa wani yawu ya hadiya ya kyafta kyafta idanu, da  saurin  ya dauke idon shi saboda rashin ganin dacewar qura mata Ido da ya yi, a zuciyar shi ya hau istighfar, can shaid'an ya sake bijiro masa da kyawun surar ta, numfashi ya ja ya na tunanin wa zai ga wannan yace ta taba aure ballantana ma a ce har ta Kai ga haihu? Allah mai halitta kenan ,hannu ta d'aga ta daure gashin ta tana kallon Hafsat dake Jan hannun ta dan su koma ciki, ja ta yi ta tsaya sannan ta ce,

"ke malama, kamal bai tafi ba fa har yanzu, yau ya makara kin dai gane ai, kuma Anwar ma na palour ya na jiran ki, Allah ya taimake ki kamal na d'aki be gan ki ba, amma dai wataqila Anwar ya ga amaryar shi cikin night wear kafin aureeee"

Turo baki ta yi cike da shagwab'a tace,

"Me yasa ba ki faɗan duk waɗannan bayanan ba ki na hango ni se da na gama dik Wani shirme ya ganni, sannan shi mijin naki  me ya hana shi tafiya Office da wuri yau,  kuma shi Anwar d'in me ya kawo shi da wuri qarfe takwas gidan mutane?"

Dariya sosai Hafsat ta yi ta tura Eamaan toilet dan bata da lokacin amsa tambayoyin ta dika, ta dakko mata kayan da zata saka kan ta fito,Jiranta ta yi dan ta taya ta shiryawa da hanzari, nan tana fitowa kuwa ta saka kayan ta Hafsat ta gyara mata gashin ta tayi kyau sosai, sai tashin sassanyan qamshi take in ba ka matsa kusa sosai da ita oba ba zaka ji ba,( Saboda har yanzu shi din ba muharramin ta bane, dan haka ba zata sake ta saka tirare mai qamshi sosai da zai ja masu fitina ba, musamman yanda suke son juna tirare zai Iya kunna masu wutar fitina a tsakanin su, gare ku mata masu zuwa zance wajen masoya a ci turare Eamaan na magana) yana ganin ta a zuciyar shi yace,

' Yah Allah she is so beuatiful, ko wace shiga ta yi kyau take yi mata'

Sai da ta sake maimaita sallamar ta  da qarfi tare da dan dukan table ɗin gaban shi sannan ya dawo daga kallon ta, ɗan murguda baki ta yi kaɗan ta ce,

" kallon fa?" Shi Kuma ya ce,

" kyawun fa?"

Dariya suka yi a tare, sannan ya zama  serious ya ce,

"Da gaske nake  kyawun ki ne ya sa na kasa sanin kin iso gare ni har na shagala da kallon ki,"

kunya ce ta kama ta, ta dan yi murmushi ta ce,

BIYAYYAHWhere stories live. Discover now