*MAMAN NABEELA CE* ✍️
*JIDDO*
( _Gidan Aurena_ )
_BY_
*MAMAN NABEELA**Dashen Allah writers Association*
*Alhamdulilah, Alhamdulilah* _ina miƙa saƙon gaisuwa a gareku masoya na amana, na irin adu'o'in da kuka ringa yi bisa aikin da aka yiwa Ƴata Alhamdulilahi an sallamemu daga Asibiti jiki yayi sauƙi._
_Insha'Allahu yanzu zan dawo typing, bazan yi muku alƙawarin kullum zan ringa posting ba amma insha'Allahu zan dinga ƙoƙartawa ina yi._
_Nagode sosai masu kirana da masu turamin saƙo Allah ya bar ƙauna._ 🥰🥰🥰*Page;* 5️⃣
______Lubabatu dake shan Ruwa kusan ƙwarewa tayi, saurin janye kofin tayi tana faɗin" mun shiga uku Malan!, Salma da gaske Amadun Jiddo yana ƙofar gida? Da ƴan sanda yazo ko da sojoji?"
Lubabatu tayi maganar tana zaro idano waje.
"Ummarmu daɗina dake tsuro wanne irin yazo da ƴan sanda ko sojoji kuma, Ammeyn Asama'u fa akaiwa tiyata toh ƴaƴa biyu aka ciro ɗaya ya mutu shine fa muka tahu dashi, ya tahu da wanda ya mutun ya kawo wa Baba Malan!"
Wata wawuyar ajiyar zuciya Lubabatu ta saki dan tayi zaton ko kamasu yazo yi.
"Kaji zanchan banza wato gawa ya kawo min? Hala bazasu iya kaishi ƙabari ba sai sun kawo min? " Suwiɗi yayi maganar cike da masifa.
"Haba Malan kaine fa Mahaifinsa, kai ya dace ka binne Yaronka da kanka. Dan Allah kaje karmu ƙara wani laifin a gurin Basamuden nan"
Lubabatu ce tayi maganar tana kallonshi.Suwiɗi da kusan tsurone ya hanashi fita ba tare da ya ce komai ba ya yi hanyar soru yana riƙe da kwan-kwaso yana ɗingisa ƙafa.
Yaya Ahmad duk yanda ya kai da ƙoƙarin ranshi kar ya kuma ɓaci zuciyarsa dake kusa sai da ta kuma dugunzuma da ɓacin ran Suwiɗi.
Ganin bashi da niyar fitowa ga magariba na ƙoƙarin yi yasa ya shiga sorun hannunsa riƙe da kwalin da gawar Jinjirin ke ciki.
A ƙofar shiga cikin gidan suka kusa cin karo da Suwiɗi, ba tare da yayi masa magana ba ya miƙa masa gawar jinjirin yana maka masa wani mugun kallo.
"Meye nan ɗin? " Suwiɗi yayi maganar yana yin baya.
Cikin fushi Ahmad yace "Gawar ɗanka" Ya dire masa kwalin a gabansa, ganin bashi da niyar karɓa.
"Kamar ya? Gawar ɗana, toh yasin bazan yarda ba kun kaita an kashe min yaro yanzu ka ɗauko ka kawo min.... "
"Baƙin halinka dai da rashin imaninka yasa ɗanka ya mutu, da kake wannan maganar ma gwara kayi shiru. Dan wannan karon da yardar Allah babu abinda ya isa ya hanani maka ka kotu baƙin mamagunci" Yaya Ahmad yayi maganar yana katse wa Suwiɗi maganar da yake cikin faɗa.
Suwiɗi kicin-kicin yayi da fuska gabansa na faɗowa yake faɗin" kajima baka kaini kotu ba, daka kawo min gawa hala baka san inda ake kai gawa ba yadda kuka je kuka kashe min yaro ai sai ku binneshi da kanku".
"Au! Haka kace Dan Allah ka barshi a kwalin har ya ruɓe karka binneshi, idan kai baka da abin yi ni ina dashi kuma ka saurari sammaci! " Yaya Ahmad yayi maganar yana ficewa daga sorun.
************
*BAYAN KWANA BIYU*
Cikin amincin Allah kwana biyun da Jiddo tayi cikin kulawar ƙwararun likitoci ga kuma kulawar ahalinta ta war-ware kamar ba ita aka yiwa tiyata ba.
Farar fatarta ta ƙara yin shar kyaunta ya ƙara fitowa kamar a taɓɓata jini ya fito tsabar kulawar da take samu, damuwarta ɗaya Zainab da Abdul da tun dawowarta hayyacinta bata sanyasu a idanonta ba.
Zaune take tayi nisa cikin tunanin Rayuwar gidan aurenta da yadda ta suma........?
Tunda aka tura akace Baba tsuhu mahaifin Babansu na kiran mahaifinsu ko wanensu ya dakata da abinda yake yana tsumayin dawowarshi, Jiddo da tafi kowa damuwa zama tayi tana rafka tagumi.
Tasan zaiyi wuya ace ba maganarta tasa Baba tsohu kiran mahaifinsu ba.
Shin mene lefinta dan ta nuna bata ra'ayin wannan Mutumin, ita tun ganin farko da tayi masa gaba ɗaya taji be mata ba duk da irin shigar mutanen kirkin da yayi kowa. Dafata Anna mahaifiyarsu tayi tana cewa"Maijiddah banaso naga kinyi tagumin nan adu'a ya kamata ki dage da ita, bana fatan ace maganar wannan mutumin Baba tsohu zai wa Babanku, dan ni kaina be kwanta min a rai ba dan haka adu'ah zamuyi Allah yasa kan wani abun daban ya kirashi"Jiddo kanta ta ɗora saman cinyar Anna tana cewa"Annarmu ina jin tsuro! gabana yana faɗowa tunda Hassanar Kawo Auwalu tace taga yaje gurin Baba tsohu hankalina yaƙi kwanciya"
Jiddo tayi maganar idanunta na cikowa da ƙwalla.Sallamar Babansu tasa Anna duban ƙofa zuciyoyinsu cike da fargabar abinda zasu ji daga bakinsa.
Tashi Jiddo tayi zata tafi ɗakinsu bayan tayiwa Baban nasu barka da dawowa, dakatar da ita yayi yana zama fuskarsa ɗauke da damuwa yake sheda musu abinda Baba tsohu ya sanar dashi na bayar da aurenta nan da sati huɗu masu zuwa. Tamkar ruwa ya cinyesu haka sukayi tsit,saboda tashin hankali.Baba tsohu mahaifin Babansu ya kasance baya neman zaɓin Ƴaƴa ko jikokinsa a wajen bada aurensu yanke hukunci kawai yake yace ya bawa wane wance ko da suna son juna ko basa so kuma haka zasu bi.
Cike da damuwa Anna tayi ƙarfin halin tambayar dawa ya haɗasu?
"Da wannan yaron Suwiɗi na wajen Malan Barau".
Baba yayi maganar cike da damuwa."Babansu yanzu ya za'ayi da batun makarantarta kaga ta kusa gamawa? "
Anna ta kuma yin maganar cike da damuwa."Hafsatu kinsan halin Baba shi dama ba'a san ranshi ake karatun bokon nan ba, kamar dai yadda ya faru kan na baya ne itama bazai bari ta gama ba..... "
Tun kafin ya kai ƙarshen maganar da ya fara Jiddo ta tashi tayi hanyar ɗakinsu kanta na juyawa....
Wannan shene masumin ita kuma tata ƙaddarar.
Taɓɓata da akayi yasa ta dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi!.
"Lafiya? Jidda shiru inata magana kin lula duniyar tunani ga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarki?" Momy Maimuna da shigowarta kenan ta karɓo magani daga parmacy na Asibitin tayi maganar tana zama gefenta haɗe da ajiye ledar maganin.
"Au! tunanin take kuma yi? " Anna da ta fito daga banɗakin dake cikin ɗakin tayi maganar tana ƙarasuwa gurin gadon.
Sharrr wani hawayen ya kuma zubowa daga idanun Jiddo..... ✍️
Pls
Share & share & share🙏*MAMAN NABEELA CE...* ✍️
