*JIDDO*
*GIDAN AURE NA*
*BY*
*MAMAN NABEELA**Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y
_Chat me on_ :07042808467
*Page* 1️⃣5️⃣
________“Dan Allah da gaske Tantirin nan ya tafi Jiddo? ”Lubabatu tayi maganar tana waige-waige bakinta yayi kaca-kaca da jini ga uban kumburin da yayi wanda da kyar take iya magana.Kallonta nayi ganin yadda lokaci ɗaya kamaninta suka sauya ina cewa“Ummasu Harisu kinga yanda kuwa kika koma, irin abinda nake gudar miki kenan kan yaɓawa Jazuli duk maganar da tazo bakinki. Wallahi banda nayi saurin zuwa ƙofar gida nayi kiran yaransa da bamu san me zai aikata miki ba inya karya ƙofar ɗakinki dan zaftareriyar wuƙar da ya zaro daga jikinsa tunda uwata ta haifeni ban taɓɓa katarin ganin irinta ba a zahiri sai a film. Dan Allah ki dinga faɗan alkairi ko kiyi shiru, ita ƙaddarar Ubangiji dan ta samu wani babu kyau ka ringa nuna kamar shiya ɗorawa kansa kana faɗa masa maganganu marasa daɗi adu'a ya kamata ki tayashi Allah ya shiryeshi bawai ki dinga yaɓa masa magana ba babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara da jarrabawar Ubangiji.
Ba fata nake miki ba wannan abun da kike yi masa wallahi tsaf Allah kema sai ya jarrabeki ta ɓangaren Ƴaƴa ko jikokinki” nayi maganar ina tsogunnawa dan ɗaura alwala.
Lubabatu kai kawai take gyaɗawa kamar ƙadangaruwa ta nufi butarta ta zuba ruwa ta fara wanke jinin da yake zuba daga bakinta, tana zuba ruwa a bakinta haƙurinta ɗaya ya biyo ruwan ya faɗo kasa hawayen bakin ciki ne suka fara biyo fuskarta a ranta kuwa ta tsinewa Jazuli ya kai cikin kwando tana kuma aiyana bafa zata yarda ba da irin wannan cin mutunci da Jazuli ya yi mata harda cire haƙuri.
Ko da na gama alwala nan na barta bayan nayi mata sannu na shiga ɗakina kwalbar maganin shafawa na me Nasara na miƙo mata nace “gashi ki shafa ko zai rage miki zogi”karɓa tayi ni kuma na koma ɗaki na ta da sallah.
Ko da yara suka dawo daga islamiya ganin Lubabatu da facemack yasa suka fara tambaya“Umma lafiya na ganki da facemack? Ko bakin coroner ne zasu kawowa gidanmu ziyar? ”
Salma tayi maganar tana zama kusa da ita.“Ba naji ance Yaya Jazuu ne yazo ya fasa mata baki ba” Abdull da ya shigo daga ƙarshe yayi maganar.
Kai da muka dawo daga islamiya da kai yanzu wa ya faɗa maka? ”
“Anty Salma yanzu Lukuman ɗin gidan Hantsi yake faɗa min wai har sai da Ammeyn mu tasa aka fita dashi saboda yace zai kashe Ummanku.”
“Lailaha ilallahu Muhammadurrasululahi (S. A. W) Abdull ban raba ka da yaron nan ba inba tsabar gulma ba har aka tare ka ana faɗa maka toh, wuce ka cire yuniform ɗin jikinka kar kuma na kuma jin ka tsaya da wannan yaron. Oh! Ni Jidda wato kasa kunne suka yi suka ji me yake faruwa har aka fara yama ɗi-ɗi da zancan toh Allah ya shiryesu su dena gulma da sa ido”
Ɗaki duk suka shiga dan su canza kayansu.
Lubabatu jin abinda Abdull ya faɗa ta kuma cika tayi fam tana kuma ayyana baza ta yarda ba.“Umma da gaske Yaya Jazuli ne ya fasa miki baki? Toh me kika yi masa? ” Salma tayi maganar tana kallon ta.
“Salma shene kawai dan nace masa me shaye-shaye shikenan sai ya jefu min dutse, Salma temaka ki samo min paracitamol da amoxcilin nasha k zanji daɗi gaba ɗaya shigen yarun nan yasa da kyar nake iya magana yanzu ma ji nake kamar zazzaɓi zai kamani” Lubabatu tayi maganar a hankali sabida yadda gurin ke mata zafi.
“Kin gani ko ni dama na san da abinda kika yi masa tunda ba zaki iya shiru ba idan yazo ki bishi da ido ai gashi nan ya fara fasa miki baki, nasha faɗa miki ki fita harkarsa su Yaya Harisu ma sun faɗa miki, Ammeyn Asma'u a ta faɗa miki amma kin ƙi ji toh Allah dai yasa iya abinda zai yi kenan”
Salma tayi maganar tana tashi ta shiga ɗakin Umman tasu.
