*JIDDO*
*GIDAN AURE NA*
*BY*
*MAMAN NABILA**Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y
_*PAGE*_ 1️⃣1️⃣
Baccin da nayi be wani yimin daɗi ba, saboda wasu rikitatun mafarkai da na ringa yi.
Ko da na tashi farkawa cikin firgici na tashi na haɗa gumi duk na jiƙe sharkaf, inda Hussain yake na duba ina tataɓashi ganin lafiyarsa lau yana ta baci na sauke wata wawuyar ajiyar zuciya ina me yin adu'ar neman tsari daga wannan mummunan mafarki da nayi.Tashi nayi na fito tsakar gida, ina fitowa naga kamar gilmawar wani Mutum cikin suro, tsorune ya daɗa kama ni dan duk da a fizge naga shigewar Mutumin yanayin zuben sa be min kama da na Babansu Asma'u ba ko su Harisu. Amma sai na dake ina cigaba da Adu'a na nufi ɗakin da su Asma'u suke ciki, na tashesu suyi sallah.
Ko da gari yayi haske da naje wanka gurin da aka yimin aiki har sannan jini yana ɗan fitowa, bayan na fito daga wanka audiga da spirite nayi amfani da su na goge gurin da yake tsa-tsafar jinin sannan na saka kaya.
Wunin ranar gaba ɗaya banji ɗuriyar Suwiɗi ba, wanda in da sabo dama mun saba inba wata buƙatar ce ta kawo shi ba bama ganinshi.
Wani abun mamaki kuma chanjin halin da Mamansu Harisu tayi min a yau dan ko ruwan wanka safe da yamma ita ta dafa min. Hussain ma wuni guda yana bayanta sai ya tashi take bani shi yasha Nono a cewarta saboda kar a dinga jagwal-gwalashi ya kamu da wata cutar da yasha kuma zata maida shi bayanta.
Nayi farin ciki da canja warta duk da wani sashe na zuciyata na ƙin yadda da sauyawar halinta lokaci ɗaya duba da shekarun da muka kwashe, bata taɓɓa nuna mana kulawa ni da yarana irin haka ba sai dai ma tsan-tsar kishi da ƙiyayya.
Yau ma kamar jiya da Asma'u tayi mana girki sai da na zuba musu a ɗakina ma suka zauna suka ci ita da Salma kamar yadda suka saba banda santi babu abinda suke ni dai kawai murmushi nayi in karɓar Hussain daya tashi.
Da da dare bayan na gama duk abubuwan da nake nasha ruwan rubutu na' na kwanta bayan nayi adu'ar kwanciya baci.
Ban jima ba baci me nauyi ya ɗauke ni.
Cikin wani ƙasurgumin jeje me cike da duhu nake gudu, duk da ƙayoyin dake sukar min ƙafa haka nake ta faman gudu dan tsira daga wasu manyan halittu dake ta bina. Hannu na riƙe da Hussain nake gudun, gaf suke da cin mun ina gudun ban ankara ba kawai naga wani ƙaton rami me cike da duhu a gabana luuuu muka tafi zamu faɗa....
Cikin firgici na farka na jiƙe nayi sharkaf, Suwiɗi naga ni tsaye a kanmu daga shi sai gajeran wando. Murza idanuna nayi ina ja da baya duk da firgicin mafarkin da nayi da nake ciki nace“Malan lafiya? ”
Wani murmushi yayi yana lasar laɓɓanshi idanunsa kafe a kaina yace“lafiya kam ai babu har sai na samu abinda nake so” yayi maganar yana matsowa kusa dani.
“Amma da wane yare kake son na fahimtar da kai ne, na faɗa maka bani da tsarki meye amfanin mata biyune? Dan Allah kayi haƙuri yau ma kaje gurin Ummansu Harisu ni dai na yafe”
nayi maganar ina gyara rigata da rabin dukiyar fulanina ke waje ganin nan ya zubawa ido.Wani kafirin murmushi yayi yana daɗa matsoni, warin jikinshi na daɗa shigewa cikin hancina. Tamkar zanyi amai haka na keji, kaw da kaina nayi ina ƙoƙarin tashi naji ya faɗo kaina wani razananen iho na saki jin wata iriyar azaba ta ziyaci ƙwa-ƙwalwata.
Tureshi nake ƙoƙarin yi amma ya sakar min duka nauyinshi,kiciniyar tureshi na cigaba da yi saboda wata azaba da nake daɗa ji daga gurin da akayi min aiki amma sam yaƙi ɗaga ni.
Numfashi nake fizga dakyar tamkar me Asma ina cewa“dan darajar Allah Suwiɗi ka ɗagani,ko ka manta aiki aka yimin gurin ciwo yake yi min, wayyooo! Zan mutu” na ƙare maganar in fizgo numfashi na dake ƙoƙarin barin jikina.Ko mutsawa be yi ba tamkar da dutsi nake magana ban ankara ba kawai naji ya chafki........ ✍️
_To be continio....._ ✍️
*Gashi nan ba yawa* 🙏🙏🙏
_Pls share fisabililah_
*MAMAN NABEELA CE..* ✍️