JIDDO(Gidan aurena) Part 8

12 0 0
                                        

*JIDDO*
_(Gidan Aurena)_

_By_
*Maman Nabeela*

*Dashen Allah writers association*

*Page;* 8️⃣

Suna shiga haɗaɗɗen shoping mall ɗin ɓangaren kayan abinci su kayi,  Momy Maimuna lodar kayan abinci masu yawa tayi danginsu shinkafa, taliya, makaroni, kuskus, semoviter, garin alkama, mai, da maggi,  sannan suka wuce gurin biya credit card ɗinta ta bayar suka cira sanna aka fitar da kayan.

Suna fitowa me taxi suka tara aka lode komai sannan suka nufi gida.

Tun basu ƙarasa gidan ba Azima da haƙurinta ya gaza tace“Anty Moon wai wa kika lodarwa wannan jibgin kayan abincin?”

“Na Jidda ne” tayi maganar tana ƙoƙarin ciro wayarta da ake kira a jaka.

“Anty Jidda kuma! ba kunce ba zata koma yanzu ba? ” Azima ta kuma jefa mata tambayar.

“Oh! Auta ki bari mu koma gida zaki ji komai”

Momy Maimuna tayi maganar tana ɗaga kiran da ya kuma shiguwa wayarta  bayan na farko ya katse.

Azima gyaɗa kanta tayi tana cewa “toh” ta maida hankalinta kan game ɗin da take a wayarta.

Suna isa gida ma Anna da idar da sallarta ke nan ta magriba,   jin ana shigowa da kaya yasa ta fitowa tana haskawa da tochlight ɗinta kusan tare ita da Babansu suke tambayar “ waɗɗan nan kayan daga ina?”

Azima da ta shigo ce tace “mu muka siyo fa ”

“Ina Maimunar? ” Anna tayi maganar tana kallon Azima.

“Taje POS cirar kuɗi yanzu zata shigo” Azima ta bata amsa.

Anna komawa ɗaki tayi Azima kuma ɗakin Jiddo ta shiga tana zuba fara'a zama tayi gefen Jiddo dake bawa Hussain Nono tana  amsa sallamar da tayi haɗi da cewa “A'a Autar Anna kun dawo? "

“Eh' Anty Jidda yanzu muka dawo”

“Ƙaramar uwa wai ina kuka je da magriba sakaliya haka? ” Asma'u da idar da sallarta kenan tayi maganar tana dariya.

“Wani guri na raka Anty Maimuna” Azima ta bata amsa.

“Uhm ya naji ana faɗin Maimuna hala gulmata ake? ” Momy Maimuna da shigowarta kenan ta ajiye jakarta tana maganar tana murmushi.

“Wane mu! Muyi gulmarki Momyna ta kaina” Asma'u tayi maganar tana dariya.

“Uhm!  Kaga masu Momy  manja” Azima tayi maganar tana yiwa Asma'u hararar wasa.

Jiddo dake kallonsu ita da Momy Maimuna dariya suka yi, kafin daga baya Momy Maimuna ta shiga banɗaki yin alwala.

Tun a daran Momy Maimuna ta shedawa Babansu da Anna,  wannan kayan abincin gudunmawarta ne na komawar Jiddo gidanta.

Sunyi farin ciki sosai inda su kayi ta sanya mata albarka. Jiddo ma tana samun labari bayan Anna ta kirata suka faɗa mata har kukan farin ciki sai da tayi, tana kuma yiwa Ƴar uwarta adu'a da fatan gamawa lafiya.

Washe gari!  Anna da kanta ita da Momy Maimuna su kaje gidan Umar Sani fagge suka kuma karɓowa Jiddo tufin da ta fara sha tun a Asibiti.

Bayan sun dawo nasiha sosai Anna ta zaunar da Jiddo tayi mata tare da bata littafin Hisnul-muslim tace ta ringa yin azkar. Sannan tace ta kuma ringa ya waita yin sallar dare Allah zai kawo mata ɗauki.

“Maijidda ki ƙara haƙuri sannan kiyiwa mijinki biyaya karkiga baya sauke haƙinku kice zaki ƙi masa biyaya, wannan shi da Allah. Allah yayi muku Albarka, idan Azima taje kasuwa zuwa jibi zata siyu miki kayan   sana'ar ta kawo miki”

“Toh Anna, na gode Allah ya ƙara arziƙi ya ƙara muku lafiya da nisan kwana. ”

“Ameen”

Taxi aka samu aka lode kayan Jiddo gaba ɗaya a ciki, Momy Maimuna da tasha gargaɗi gurin Anna kan karta sake taji ta yiwa Suwiɗi ko kallon banzane, dan da farko hana ta zuwa tayi sai da tayi ta magiya da saka bakin Jiddo sannan ta barta bayan tayi  mata alƙawarin babu ruwanta dashi. Sai Azima da Asma'u, Abdull da Zainab sai kuma ita Jiddo shiga Motar su kayi suka nufi gidan Jiddo.

Suna isa shiga cikin gidan Jiddo tayi tun daga soru taga ɗakin dake sorun a rufe ta san Baba Malan baya nan cikin gidan ta shiga tana sallama, Salma dake...... ✍️

_Hmmm, yanzu za'a fara wasan fan's ina kuke ga jiddo fa ta koma gidan Suweɗi yaya zata kasance.....?_

*Gefe guda ga gamun da Lubabatu ta fara yi a gidan shin ita kadai ta gani babu me kuma gani ko za'a samu wanda idanunsa zasu kuma ganin abinda ta ganiiii....?*

_Ku biyo alƙalamin Maman Nabeela domin jin ya zata kaya._

*MAMAN NABEELA CE* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now