JIDDO
(Gidan aurena)
By
MAMAN NABEELADASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION
Tafiya Tahir ya shirya min tare da drivernsa sakamakon shi yanayin aiki bazai samu damar kaini ba.
Ko da na iso Kano sosai na tarar gidan basa cikin kwanciyar hankali, Jidda na kwance babu lafiya saboda yadda ta saka batun auren a ranta.
Hankalina naji ya ƙara tashi ganin yadda Jidda ta rame ta lalace sosai take kuka tun zuwana tana faɗin'ita bata sonshi idan ta aureshi mutuwa zata yi.
Hankalina naji ya kuma tashi nan na tasa ta a gaba ina tambayar wanene?
Amma ta kasa faɗa min sai kuka da take, Anna da ranta ya gama ɓaci saboda abinda Jidda take yi tun daga lokacin da aka yi maganar faɗa ta fara yi tana ce wa“Wai ni Jidda a kanki aka fara irin wannan auren ne da zaki tasa mu a gaba ki hana mana kwanciyar hankali? Ko kuma don kinga duk muna nuna damuwa a lamarin ki shi yasa ki ke neman saka mana ciwo to wallahi in zaki kwantar da hankalinki ma gwanda ki kwantar don kinsan ko mutuwa za kiyi ki dawo Baba babu abinda zai sauya daga abinda ya faɗa haba ko a kanki aka fara yankewa mutum karatu cha nake ga Ƴar'uwaki nan haka aka tsigeta itama aka yi mata auren! In Allah ya yi zaki ci gaba ai ko kina ɗakinki zaki iya cigaba” Anna ta ƙare maganar da sau-sauta murya cike da lallashi.Tambayar wanda zata aura na fara yiwa Anna nan ta ke sheda min Suwiɗi Ɗan gurin Malam Barau ta ke na fara tunanin waye ma Siwiɗi yayin da Jidda ita kuma ta daɗa rushewa da kuka sai da Anna ta kuma kwatanta min shi sannan na gane shi.
Tashin hankalin da na shiga har yafi na baya saboda jin wanda zata aura tabbas in baiyi sa'a da Babanmu ba to kuwa zai yi sa'a da Kawo Auwalu Mutumin da a lokacin Matansa biyu amma za'a ɗauki Jidda a sakata a cikinsu kamar an gaji da ita! Na yi maganar cikin raina cike da tashin hankali amma ganin yadda Jidda ta zuba ido taji mai zan ce yasa na ƙirƙiri murmushi ina faɗin “Jidda ki kwantar da hankalinki in sha'Allahu zai riƙe ki da amana kuma ya barki ki cigaba da makaranta kiyi biyayya karda sanadin wannan abun ran Iyayenmu ya baci saboda ke kinji in sha'Allahu zaki ga ribar biyayya”
na yi maganar cike da tausayinta a raina kuma ina shirya tunkarar Baba Tsohu kan lamarin.Sosai muka haɗo ni da Anna harma da Yaya Ahmad daya dawo bayan zuwa na mukai ta lallashinta da kyar muka samu ta kwantar da hankalinta har ta ci abinci.
Da yamma liƙis na ce wa Anna bana leƙa na gaida su Baba Tsohu da Anty Hajjo, fatan dawo wa lafiya ta yi min na kama hanya ni da Yaya Ahmad da yake ƙofar gida muka nufi gidan muna hira inda nan nake faɗa masa inaso idan munje mu haɗo ni da shi mu ruƙe Baba Tsohu ya ruƙa mana Suwiɗin ko bayan aurene Jidda ta cigaba da karatu” sosai shima ya yi na'am yana ce wa shima dama yana ta wannan tunanin amma ya rasa ta yadda zai tunkari Baba Tsohu.
Cike da farin ciki muka ci gaba da hira har muka ƙarasa gidan, da sallama muka shiga inda nan muka tarar Kawo Auwalu zai fita gaisawa muka yi dashi sannan muka ƙarasa ciki gaisawa muka yi da Anty Hajjo take tambayata yaushe na zo na ce mata ɗazo karasawa ciki sashen Inno kakarmu muka yi nan muka baje muna kwasar hira nan nake tambayarta Baba tsohu ta ce ya ɗan fita amma bata tura yara suyi masa magana yana ƙofar Masallaci.
Kafin Yaron da ta aika ya dawo ta dama mana fura muka fara sha Muna ta hira tana riƙe da Haidar.
Ba'a jima ba sai ga Baba tsohu ya shigo da sallama gaisawa muka yi cike da farin cikin ganinmu ya zauna yana karɓar Haidar daga hannun Inno hira muka ɗan taɓa dashi kafin Yaya Ahmad ya fara faɗa masa abinda ke tafe damu, duk da yadda muka ga fuskarsa ta sauya bai sa Yaya Ahmad ya dakata ba sai da ya kai ƙarshe, nima na ɗora da tawa maganar cike da ruƙo.
“Kun gama? Na ce kun gama? To duk naji abinda kuka faɗa bari na tambayeku shi ilimin Bokon dolene da har kuka sani a gaba akan sai ta ci gaba?” Ya yi maganar cikin faɗa yana kallonmu, babu wanda ya iya bashi amasa cikin ni da Yaya Ahmad sai tsantar maganarsa muka kuma yi cikin ƙara fusata yana faɗin
“To ku sani babu fashi wannan auren mudin ina raye kuma batun karatu ko mutuwa zata yi bazan tambayi Suwiɗi ya barta ta yi ba waɗɗan da aka aurar na baya finsu gata ta yi? Indai kunsan wannan maganar ta kawo ku ku tashi ku barmin gida” Baba tsohu ya ƙare maganar cikin faɗa da saita musu hanya.Duk yanda Inno taso ya yi haƙuri abi komai a sannu rayuwa ta sauya yanzu ilimi ya zama shine ja gaba a rayuwa na Addini dana Boko yinsu duka na da amfani.... Ai bai bari ta gama ba faɗan ya koma kanta na ko ita ta sasu saboda son jikokinta na tsaya, ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba.
Ko sallama bamu samu yiwa Anty Hajjo ba muka bar gidan kowa rai ɓace ko da muka dawo gida bamu yadda mun faɗawa ko Anna abinda ya faro b.
Kwana na biyu da zuwa ganin Jidda ta ɗan saki ranta ta fara warwarewa ga Tahir nata kirana kan yaushe zan dawo Anna ta tarkatani na koma bayan sun gyara wayarsu da ta lalace.Kamar yadda ake saka ko wanne aure na zuri'armu haka aka saka na Jidda cikin ƙanƙanin lokaci akayi bikin aka gama aka miƙata ɗakin Mijinta tana gursheƙin kuka kamar ranta zai fita, kwana biyuda kaita muka kai kayan garar da aka yi mata abin mamaki kamar ba Jidda dake ƙin auren ba da Suwiɗi ya shigo mu gaisa har rawar jiki take gurin karɓar ledar piowatern da ya shigobda ita tana tsugunnawa har ƙasa, ta zama wata shiru-shiru ta kwantar da hankalinta babu wannan koke-koken.
Ni dai mamaki bai barni ba da muka dawo gida nake bawa Anna labari sai take nuna min ai Addu'a ce tayi tasirin da tasa haka, haka na fara shirin komawa Kaduna nima amma da ta faɗo min a rai sai naji zuciyata taƙi yadda da sauyawarta lokaci ɗaya don sai bayan auren wata da muka haɗo da ita take cemin ai ana zargen shi yayi sanadin mutuwar Matarsa ta farko ko wata guda ba'a yi ba, haka na tarkata na koma kaduna zuciyata cike da tunanuka ina ta Addu'ar Allah dai yasa ba haka bane kawai sharin mutanene tunda aikin gama ya riga yagama Jidda ta riga ta aureshi.........Nan ta cigaba da bawa Mame labarin auren Jiddo har kawo rabuwarsu....
duk ƙarfin zuciya irin na Mame sai da labarin ya sakata zubar da hawaye ita babban mamakinta dama har yanzu ana auren dole?Mame hawayen dake idonta ta share tana ce wa “Maimuna amma dai an kama wannan azzalumin ko?”
Murmushin da yafi kuka cewo Anty Maimuna ta yi sannan ta ce“Ba kamashin da aka yi Mame a yanzu haka ma labarin da na samu a kansa wai takarar gwamna ya tsaya a kano”
Jinjina kai Mame ta yi tana ƙara jin son Jidda da tausayinta har cikin ranta tare da burin taimakawa rayuwarta don tana jinta tamkar su Bintu da Batul a cikin ranta......★★★★★★★★★★★
A. RASHID
Ɓangaren A. RASHED Mame da Maimuna suna barin falon abinci sosai ya ci don ya yi mugun yi masa daɗi kafatanin kunun ayar da aka kawo sai da ya kusa shanyeshi.
“ T don Allah wa yayi wannan kunun ayar? ” Ya yi maganar yana ajiye kufin da yasha.Tahir mai zai yi banda dariya sosai yake dariya jin tsabar santi har tambayar wa yayi ya ke?
Ɓata fuska ya yi yana wurgawa Tahir dake ta dariya har sannan harara“Oh! Oh! Oh! Karfa kayi tunanin santi nake da har kake min dariya, kawai dai na tambaya ne ba don wani abu ba ” ya yi maganar yana wani taɓe baki.
Dariya Tahir ya kuma kashewa da ita yana faɗin “na nawa kuma Malam ai waigine kawai ban saka maka ba” ya yi maganar cikin dariyar da yake.
A. RASHED bai kuma tanka shi ba ganin yadda yake yi masa dariya, shi kansa yau cike yake da mamakin kansa na yadda ya ke abubuwa ba yadda ya saba ba, zuciyarsa da idanunsa sosai suke muradin sake tozali da ita, saboda yadda lokaci ɗaya soyayyarta ta shige shi daurewa kawai yake kar ya bayyana wannan ɗan rainin hankalin ya tasa shi gaba da tsokana.
A ƙoƙarin da yake na son ya kau da abun daga ranshi nan ya fara yiwa Tahir magana akan aikin sabon reshen kamfaninsa dake lagos wanda za'ayi a Abuja wanda shi Tahir kusan duk shine a kan kula masa da su don shine mataimakinsa musaman ma ta ɓangaren kamfanuni sosai suke tattaunawa inda Tahir ke nunnu na masa wasu abubuwan ta cikin Tap ɗin dake hannunsa yana yi masa bayani........
MAMAN NABEELA CE
