JIDDO
(Gidan aurena)
BY
MAMAN NABEELADASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION
AFFUWAN KWANA BIYU KUN JINI SHIRU SAKAMAKON RASHIN LAFIYAR DA TA SAMENI NE, AMMA YANZU ALHAMDULILAH
Faisal tamkar wani status haka ya tsaya yana kallonta jin maganar da suka faɗa masa, ba wai ya yarda bane da abinda ita da Buduruwar dake Mota suka faɗa masa ba don baya jin ko da da gaske Matar auren ce zai iya haƙura da ita.
Zabura ya yi tamkar wanda ya farko daga bacci ya nufi Motarsa cikin gudu-gudu don dole ne ma yau ya bibiyeta yaga gidan da take, yana ƙoƙarin bin bayansu ganin Motarsu ta fara tafiya wata Mota ta shiga gabansa tamakar zai fasa stiarin Motar haka ya kai masa duka haɗe da danne horn, lokacin da Motar ta matsa daga gaban Motarsa har Motarsu ta ɓace ɓat cike da takaici da baƙin ciki ya fito yana dannawa mai Motar zage tamkar zai zabga masa mari kamar taɓaɓe nan take rigima ta kacame wadda ta haɗa harda jami'an tsaro.
Mai Motar da yake zage wanda kana kallonsa kasan shima ba ƙaramin Mutum bane take yasa aka yi ram dashi bai dena lailayo zagi yana antayawa Mutumin nana ba har jami'an tsaro suka turashi Mota.
Sosai ran Mutumin ya kuma ɓaci take ya kira mataimakin kwamishinan Ƴan sanda na Kaduna wanda ya kasance amininsa ne ya bashi bayani da kuma irin hakuncin da yake so ayiwa Faisal.Har suka wuce police station yana ta zuba tijara, “wallahi tunda kuka kamani duk sai kun rasa aikinku kunsan ko ni waye kuwa ?” Ya yi maganar yana naushe wanda ya riƙe masa hannu.
Babu wanda ya kulashi cikin jami'an tsaron har suka isa police station.
Suna isa police station aka wuce dashi cikin sell take wanda aka bawa umarnin da an kawo shi suyi masa hukunci suka fara kirɓarsa kamar Allah ya aiko su, sosai suka yi masa dukan tsaya wanda yasa kan kace meye wannan fuskarsa duk ta kumbura bakin tijara tuni ya mutu.
Haisam da wani abokinsa dake tsaye lokacin da aka kamashi ya kirashi yake faɗa masa cike da tashin hankali ya nufi gidansu Faisal ya sanar da Mahaifiyarsa Hajiya Hindatu cikin ƙanƙanin lokaci suka gane police station ɗin da aka kaishi, ko da suka je juyin duniya su bari su ganshi suka hana duk cin hancin da tabasu fir suka ƙi amsa, duk yadda tasu tayi maganin matsalar ba tare da ta sako wani ba abin ya gagara don jami'an sun murzawa idanunsu toka sun ma ƙi saurarenta.
Wayar ta ta ɗauka ta lalubo lambar wayar mijinta Tijjani ta sanar masa abinda ke faruwa, sosai ransa ya ɓaci ya kuwa fara zazaga mata faɗa ta cikin waya ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba “yanzu da kika kirani mai kikeso na yi muku bayan ke kika ɗaure masa ƙogu yake abinda yaga dama? ” Tijjani ya yi maganar cikin takaice.
“Haba Alhaji yanzu fisabililahi idan baka tsaya masa ba wa zai tsaya masa sun mafa hana mu ko ganinsa kuma waya sani ma ko babu laifin da ya yi musu suka kamashi! Ni dai don Allah ka saka baki a sake shi kar ya kwana gurnan” ta yi maganar cikin danne nata fushin har sai bayan an sako mata Yaronta ɗaya tilo.
“To idan ya kwana ma ai shi ya jawa kansa kuma su jami'an tsaro ai ba mahaukata bane da zasu kamashi babu dalili, kinga kiyi Addu'a kawai na samu wayar Abdurrashid don nasan shine kawai zai yi musu magana su sakeshi” ya yi maganar yana katse kiran haɗe da jan tsaki.
Wayar ɗan ɗan uwansa da suke Ƴan uba ya fara nema cikin ikon Allah ya samu ta shiga tana gab da katsewa aka ɗaga.
“Assalamu alaikum Uncle barka da rana” A.RASHED da ya ɗaga wayar haɗe da maganar cike da girmamawa.
“Amin wa alaikumussalam barkanka dai Abdurrashid ya aiki? Allah yasa ban katse maka aiki ba! ” Tijjani ya yi maganar cike da ƙaunar ɗan Yayan nasa.
“A'a no Uncle lafiya laubAlhamdulilah” ya bashi amsa haɗe da mai da hankalinsa ga wayar.
“Abdurrashid ƙanin nan dai naka ne Faisal da baya jin magana yanzu Mahaifiyarsa ta kira take faɗa min jami'an tsaro sun kamashi kuma sun hana kowa ganinsa sun kuma ƙi sakinsa don Allah shine nake so ka saka baki idan laifin ba mai tsanani bane su sakeshi” Alhaji Tijjani ya yi maganar cikin ruƙo.
