JIDDO
(Gidan aurena)
By
MAMAN NABEELAASALLAMU ALAIKUM MY FAN'S KWANA BIYU KUN JINI SHIRU WLH WANI MUHIMIN UZURI YA RIƘE NI, INA FATAN ZAKU YI MIN AFFUWA.
________"Waw amma fa Big Bro ya iya zaɓe Antyn mu ina wuni! " Buduruwar ta yi maganar haɗe da gaisheni.
"Lafiya lau ya gida ya Mamey? " Na yi maganar cikin fara'a ina kallon Buduruwar.
"Lafiya lau tana gaishe ki, ni sunana Batul Autar su Yaya Abdurrashed "
"Masha'Allah ai ina ganinki naga kamanin Mamey" na kuma maganar ina dariya.
Dariya suma suka yi Batul ta fara cin abincin da aka kawo musu, hira sosai ta ɓarke tsakaninmu da Batul don itama ba baya ba gurin surutu tamkar mun wani jima da haɗowa haka muka sha hira da ita, hotona sosai ta dinga ɗaukata a wayarta ni dai ina yi ina karewa saboda babu mayafi a jikina ga kayan da na saka sun kamani sosai duk inda na saka ƙafata muna tare da Jannat wadda itama a wayata na yi mata hotona sosai.
Basu suka bar gidan ba sai kusan magriba ƙatuwar jakar da aka yi ta suna na zuba musu duk abubuwan da ake rabawa a ciki da ƙyar ranar ma Jannta ta yadda suka tafi.
Bayan fitar Motarsu ciki muka koma zuwa lokacin ƴan suna tuni duk wasu sun ta tafi waɗɗan da suka rage basu da yawa suma ƴan uwan Tahir ne na kusa-kusa wajen ƙarfe tara suma duk suka ƙarasa watsewa, Alhamdulilah anyi suna lafiya angama lafiya zane muke ɗakin Anty Maimuna muna ta shirya kayan da ta samu ita da jariri cikin drower, sosai suka samu kaya ba ɗan kaɗan ba don ko turamen atamfufi sai da muka lassafa sunyi kusan ashirin kayan jariri kuwa suma ba'a magana don wasu rigunan ma har ya fara tafiya kafin ya sakasu, haka muka jibge kayan cikin drower sannan na gyara mata ɗakin.
Fita na yi naje gurinsu Baba Ladidi na tarar harsun kwanta sai da safe na yi musu na fito na nufi ɗakin da nake cike da gajiya Bathroom na shiga na haɗa ruwa mai zafi na yi wanka dashi sannan na ɗauro alwala, ko da na fito sallar isha'i da banyi ba na yi sannan na yi shafa'i da wutiri ina idarwa a dadage na yi Addu'a sannan na faɗa gado na kwanta sosai nake jina kamar anmin duka tsabar gajiya cikin ƙanƙanin lokaci kuwa bacci ya kwasheni bani na farka ba sai asuba shima kiran sallar da ake ya tada ni Addu'a na yi kafin na tashi na shiga banɗaki, kama ruwa na yi haɗe da yin alwala, bayan na yi sallah azkar na yi sannan na jawo wayata da niyar yin karatun Al-ƙur'ani miss call na gani har uku kuma duka na A. RASHED sai saƙo guda biyu murmushi na yi ina buɗe saƙon " I miss you" shi na gani rubuce a saƙon farko buɗe na biyun na yi "Barka da asuba sahibul ƙalb ina fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya " wani irin daɗi da farin ciki ne suka kamani tare da jin ƙarin soyayyarsa a raina cike da farin cikin kalamansa bansan lokacin da hannuna nima ya fara rubuta masa saƙo ba ina gama rubutawa na tsaya ina kuma bin abinda na rubuta da kallo haɗe da turashi "Amincin Allah tare da yardarsa su tabbata a gareka My heart beat na tashi Lafiya, ina fatan kai ma ka tashi lafiya Sadauki! " Sai bayan da na tura saƙon kuma abinda na rubuta yake kuma dawo min sosai na fara jin kunya gashi saƙon ya riga ya shiga, karatun Al-ƙur'ani na fara yi sai da na yi sura biyu sannan na dakata na tashi na naɗe abun sallah na gyara ɗakin fitowa na yi na nufi ƙasa lokacin gari ya yi haske sosai ɗakin da su Baba Ladidi suke na shiga ita kaɗai na gani zaune tana jan charbi zama na yi gefenta ina murmushi "Tsohuwa mai ran ƙarfe Hajja Kakus ina kwana " na gaisheta ina murmushi."Lafiya lau Hauwa kulu kin tashi lafiya" ta amsa min bayan ta dakata daga jan charbin da take fuskarta da murmushi.
"Lafiya lau Kakus ina su Amma da Anty Hajju? " Na amsa haɗe da tambayarta .
"A'a baki gansu ba? Ai suna nan waje"
"Ban gansu amma ba na duba ko suna Kitchen " na yi maganar haɗe da tashi.
"Eh duba chan don kinsan Hajju da son yin girkin tsiya ba makawa ma suna chan bare nan taga komai waja-waja ai tana chan tana rawar kai gaban tukunya Allah dai yasa kar ta saka mana wannan abun da ta ke sakawa a gida mai warin ungulu don shine matsalar girkinta" ta yi maganar tana kyabe baki.
Dariya sosai na kwashe da ita haɗe da juyowa don har na kai bakin ƙofa "Hajja Kakus menene kuma mai warin ungulu da ake sakawa a girki?" Na yi maganar cikin dariya.
"Au dariya na baki ai da gaske warin ungulu yake ni me naji tana kiransa koriya ko kur menene ma oho"
Tun bata kai ƙarshen maganar ba na fahimci me take nufi bansan lokacin da na kuma kwashewa da dariya ba sai da na yi dariya son raina idanuna har na tara ƙwalla ganin ta saki baki haɗe da riƙe haɓa tana yi min wani kallo yasa na dakata ina goge ƙwallar da ta taru a idanuna na ce"Hajja Kaku Allah yaja kwana yanzu curry ɗin ne yake warin ungulu! Shifa gyara girki yake da ƙara masa armashi "
"Ah lalai Hauwa'u mai ki ke nufi yanzu da girmana na yi ƙarya kenan! Yoh in ba warin ungulu ba me yake? , Oh ni Aminatu yau ga Ibarahima ya haifi Ƴar da take ƙaryata ni da girmana" ta yi maganar fuskarta kicin-kicin tamakar zata fashe da kuka.
Idano na zaro jin maganar da ta ke na ce "Allah ya huci zuciyar Hajja Kakus ɗin mu ina ni ina ce wa kinyi ƙarya wallahi ba haka na ke nufi ba, haba Uwar gida kuma amaryar Baba Tsohunmu mai zamani wane ni Jidda da wannan batun" na yi maganar cikin lallashi don kaɗan daga aikin Baba Ladidi ne ta fara zubu mana rikici da sanyin safiyar nan, kuma wuni za'ayi in ba'ayi wasa ba tana mita.
"To bazan haƙura ba sai dai in kinje kinyi min haɗin zogale mai daɗi da yasha ƙoli da albasa da tomatur shine zan haƙura" ta yi maganar tana gyara ɗaurin ɗankwalinta ta turoshi gaba haɗe da ɓantarar guro tana tauna.
Dariyar da ke tasu min na danne ina ce wa "karki samu damuwa yanzu kuwa zanje na haɗa miki Hajja Kakus" na yi maganar ina nufa ƙofa na yi saurin fita sannan dariyar da nake riƙewa na saketa, kitchen ɗin na nufa jiyo kamar motsinsu har sannan fuskata da dariya.
"Assalamu alaikum sannunku da aiki ashe kuna nan na shiga ɗakin chan mu gaisa tsohuwar nan take neman rataya min jakar tsaba" na yi maganar ina dariya haɗe da ƙarasa shiga cikin kitchen ɗin.
"Amin wa alaikumussalam yauwa Maijidda, ai tsakaninku da Baba mukam sai dai musha dariya idan ƴan rikici sun motsa" Anty Hajjo ta yi maganar tana dariya.
"Ƴar nema ta yiyu ma ke kika tsokano ta fa " Amma ta yi maganar haɗe da dungure min kai.
"Ouch wayyo! Amma wallahi a kan Anty Hajjo ne fa...."
"Kai Jidda kiji tsorun Allah wace Hajjo ɗin kuma nida nake a nan muna tare da Yaya? " Anty Hajjo ta yi saurin tarar maganar da nake.
"Wallahi Anty da gaske nake akan fa curryn da kike sawa a girki ne................." nan na kwashe duk yadda muka yi da ita na basu labari, ai tun ban kai ƙarshe ba suke dariya.
"To ai zama bai ganki ba Maijidda yanzu kayan kwaɗon zogale zaki fara nema kar taji shiru wani sabon rikicin ya tashi" Anty Hajjo ta yi maganar cikin dariya.
"Allah dai yasa Maimuna tana da zogalen! " Amma ta yi maganar itama har sannan fuskarta da murmushi.
"Ba na duba ko Anty Maimuna ta yi shaura lokacin da tayiwa Yaya Tahir" na yi maganar ina nufar frige ɗinta na fara dubawa cikin ikon Allah ina tsaka da dubawa sai gata ta shigo tambaya ta ta yi mai nake nema nan na faɗa mata haɗe da bata labarin rikicin mu da Baba Ladidi, dariya sosai itama ta yi kafin ta ce "Allah ya temakeke jiya Tahir ya shigo da wani zogalen don yanzu ma shi zan haɗa masa kinga sai ki haɗa kawai duka kowa ma sai yaci" Anty Maimuna ta yi maganar tana nufar ɗayan frige ɗin.
Bayan ta ɗauko haɗe da kayan da za'a haɗashi gaba ɗayansa na wanke da ruwan ɗumi sannan na fara haɗashi sosai haɗin zogalen ya yi kyau haɗe da daɗi Anty Maimuna ce ta ɗibarwa Yaya Tahir nashi haɗe da Breakfast ɗinshi ta fita kai masa, nima ɗiban na Hajja Kaka na yi da abin karinta na nufi ɗakin da ta ke.
"To Kaka ga zogalen naki har da ma abin kari duka na haɗo miki"na yi maganar ina ajiye tire ɗin abincin a gabanta haɗe da dariya.
"To sannunki Allah dai yasa ya yi daɗi" ta yi maganar haɗe da washe baki lokacin da ta buɗe kwanon da zogalen yake.
"Ai kawai ki ci kiji Hajja Kakarmu" na yi maganar ina dariya ganin har ta fara gyara baki.
MAMAN NABEELA CE