JIDDO (Gidan aurena) Part 7

12 0 0
                                        

*JIDDO*
( _Gidan Aurena_ )

*Story*
_By_
*Maman Nabeela*

*Dashen Allah writers Association*

*Page;* 7️⃣

_______Tana sako kafarta kawai taga tsakar gidan malale da jini tamkar kogi,  zaro idanuwanta tayi tana yin baya.  Kanta ne ya fara juyawa ta fara  gani bibbiyu.  Take ta silale a gurin ta suma,
Kasancewar gidan babu kuwa yasa ba wanda yasan halin da take ciki.
Dama maƙota ma tuni suka dena shigowa gidan  saboda mugun halin Suwiɗi,   bare in sun shigo suga halin da take ciki su kawo a gaji!.
Sai da Salma ta dawo sannan taga halin da take ciki da sauri ta ɗebo ruwa ta zuba mata.
Firgigit ta farko tana faɗin “انه من سليمن وانه بسم
اله الر حمن الر حيمInnahumin sulaimanu wa innahu bissmillahi 
rahamanirrahim”
Ta ƙarashi tana  zaro idanu tana waigen inda take.
“Lafiya Umma?  Meye ya sameki harda suma gashi kina jawo aya? ”
Salma tayi maganar itama tana wage-waige a ɗakin dan ganin me Ummarta ke waigen gani!.

Fashewa da kuka lubabatu tayi tana faɗin “na shiga uku ni Luba,  ƴarnan ina zura ƙafata ƙofar ɗaki zan tafi gidan sunan Babar Asama'u kawai idanu na sukai tuzali da jini cike da gidan nan kamar kogi daga nan ban kuma sanin komai ba sai yanzu ashe suma nayi. Salma ta ina kika shigo? Shikenan tamu ta ƙare aljanu ko matsafa sun tsaface mana gida ya zama kogin jini” ta kai ƙarshen maganar tana daɗa fashiwa da kuka.

Salma da ta saki baki da hanci tana kallon Umman tata kamar sabuwar halitta cike da mamaki tace “Umma jini kuma a gidan nan ai ni banga komai ba dana shigo”

“La'ila ha illallahu Muhammada rasulullahi (S. W. A) Salma baki ga komai ba ki kace?shikenan ni kuma irin tawa ƙaddarar kenan, ta yiyu ta kaina zasu fara filen kan shiyasa suka fara nunan kogin jini. Salma ki ruƙa min yafiya gurin Ya gwalgwal da Innatu Allah ya haɗɗamu a darrussalam” Lubabatu tayi maganar tana daɗa rushewa da kuka.

“Umma ki nutsu ki kwantar da hankalinki, insha'Allahu babu abinda zai faru kinga anyi kiran Sallar magriba bari na zuba miki ruwa sai kiyi alwala” Salma tayi maganar tana ƙoƙarin tashi dan ita ba yarda ne da abinda Ummar tata take faɗa bata yi ba,  ta dai fi tunanin ko hawan jininta ne ya motsa har idanuwanta suka ga ba dai-dai ba.

Da kyar Salma ta samu ta lalashi Ummanta har tayi sallah itama sallar tayi bayan ta idar nan Ummar tata tace ta kunna musu karatun ƙur'ani Allah yayi musu katangar ƙarfe da koma wane ɗan file kai ne. Lol Luba tamu...😂😂😂

JIDDO washe gari masu aikin nama na tsaka da suya,  sai ga kira daga Baba tsohu na yana son ganin Jiddo da Anna harma da Momy Maimuna  ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi gidan Kawo Auwalu dake bayan layinsu.
Suna isa suka tarar da Babansu Jiddo da Yaya Ahmad ma duka suna can,  bayan sun zauna sun gaida shi ya amsa shiru gurin yayi kowanensu zuciyarsa nayi masa saƙe-saƙe, gyaran muryar da Baba tsohu yayi yasa ko wanensu maida hankalinsa gareshi.

“Abinda yasa na taraku a nan ba komai bane face a kan Hauw'u me gidanta ya kawo min ƙarar kun ɗauke matarsa bada izininsa ba bayan  cimasa mutunci da Maimuna da Amadu sukai har gidansa. Ibrahim  kai ka turasu?  Ko kuwa ke Hafsaatu ke kika turasu?” Yayi maganar yana jefawa Baba da Anna tambayar.

“A gafarce mu Baba Bamu da masaniyar hakan, abinda muka sani Maimuna taje gidan ta tarar da ita a halin ciwo batasan wake kanta ba ta ɗauketa ta kai Asibiti.
Wanda tsananin halin da take ciki yasa har sai da aka yi mata aiki. Dalilin dayasa ma bamu sanar da kai ba, saboda ganin yanayin jikinka”
Baban Jiddo yayi maganar cike da girmamawa.

“Toh! 'toh da aka sallameta me yasa kuka ƙi mayar da ita gidan mijinta? Duk nasan abinda ke faruwa a gidan aurenta amma yin bure da da tada  jijiyar wuya bashi zai sa a samu masalaha ba, dan haka ba tare da ɓata lokaci ba ku maida masa matarsa yadda kuka ɗaukota dan ya fiku iko da ita a halin yanzu tunda mijinta ne shi. Sannan zan daɗa ja muku kunne kai Amadu da ke Maimuna muddin kunsan tashin hankali zai kaiku gidan ba ziyarar Ƴar uwarko ba toh karda ma naji kunje gidan. Adu'a ita take buƙata kuma muna taya ta Allah be manta da ita ba zai kawo mata ɗauki” Baba tsohu ya ƙare maganar cike da gargaɗi yana dubansu.

Yaya Ahmad da tunda Baba tsohu ya fara maganar komawar Jiddo gidan Suwiɗi ya kasa hakuri yace
“Amma Baba........ “ dakatar dashi Baba tsohu yayi yana cewa “kawai kuyi abinda nace”

Jiddo tunda Baba tsohu ya fara maganar komawarta take hawaye aranta take faɗin anya Baba tsohu yana ƙaunarta kuwa? Tana kokwantun hakan.

Momy Maimuna ma hawayen take na tausayin ƴar uwarta, tabbas Baba tsohu ba abokin wasansu bane ko abun raina warsu. Da wanine yake wannan maganar bashi ba tabbas da tuni ta wanke shi tasss da soso da sabulu amma Baba tsohu ne mahaifin Babansu,  ko ba komai yana da matsayi Babba a rayuwarsu da bazasu iya ja'inja dashi ba bare musayar yawu.

“Baba kayi haƙuri insha'Allahu zata koma ” Anna tayi maganar da raunananiyar muryarta da take cike da tausayin Ƴar tata.

Bayan sun tashi dakatar da Jiddo yayi ya kama hannunta ya zaunar da ita kusa dashi, yana yi mata magana can ƙasa da nima me ɗaukan rahotu bana jin me yake faɗa mata, murmushi naga ta fara sannan ya ɗauko wata leda me girma ya bata.

Yaya Ahmad dake cike famm kamar zai fashi ba wanda ya yiwa sallama ya wuce ya koma gurin neman kuɗin shi.

Suna komawa gida har an gama suyar naman Ragon da Babansu shi ya siyeshi aka yanka Asma'u da Azima har sun gyara gidan fess Azima dake ƙoƙarin shiga banɗaki ce taga shigowarsu, sannu da zuwa tayi musu tana bin fuskokinsu da kallo ganin damu ƙuru-ƙuru a fukarsu ga fuskar Anty Jiddo jawur alamun tayi kuka yasa ta dakata.

“Me yake faruwa? ” Ta kwato tambayar da kyar daga maƙoshinta.

Babu wanda ya samu damar amsa mata suka wuce suna shigewa ciki.

Bin bayansu tayi tana kuma tambayar “Lafiya? ”

“Auta ba wanka zaki shiga bane?  Babu komai fa maza kiyi wankan ki fito” Jiddo tayi maganar tana ƙaƙalo murmushi.

Bandan ta yarda ba komai ɗin bane ta wuce ta shiga wankan.

Asma'u ma da tagama saka kaya ta fito sannu da zuwa tayi musu  ganin yanayin fuskokinsu yasa ta fara tambayar meke faruwa?

“kije ki fara haɗɗawa Ammeynku kayanta zuwa gobe zaku kuma gida” Anna tayi maganar tana dubanta.

Tashi tayi ta shiga ɗakin da kayan Ammeynsu suke, zama tayi gefen katifa tana tsirawa bango idano. Me za tayi farin ciki ko baƙin ciki.
Tabbas tana tana baƙin cikin abinda Babansu kewa Ammeynsu amma duk da haka baza tasu wani abu ya gitta ta tsakaninsu yayi sandin rabuwarsu ba komai lalacewarsa mahaifinsu ne.  Tausayin halin da mahaifiyarsu dasu kansu zasu kuma shiga in sun kuma gidan ya kuma bijiru mata. “Allah ka shiryi mahaifinmu ka dawo dashi hanayar dai-dai.” tayi maganar a fili tana goge ƙwallar da ta zubu mata.

JIDDO

Anna da Momy Maimuna zama suka yi sukai ta kwantar mata da hankali har ta sake, kafin daga baya Momy Maimuna tace Azima data gama shiryawa bayan ta fito daga wanka tazu ta rakata.

“Maimuna ki rage yawan fitar nan fa kinsan yanzu kiwon mutum ake bana dabba ba,  yanzu gaf da magribar nan ina zaki je ma? ” Anna tayi maganar tana duban Maimuna.

“Anna ba wani guri me nisa zani ba yanzu zamu dawo, saƙo zan karɓo fa”

“Toh sai kun dawo”

Suna fita wani Shoping mall suka nufa...

To be continio.....✍️


*MAMAN NABEELA CE...* ✍️

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now