JIDDO(Gidan aurena) part 32

26 2 0
                                        

    JIDDO
(Gidan aurena)
   STORY BY
MAMAN NABEELA

DASHEN ALLAH WRITERS ASSOCIATION

__________Murmushi A.RASHED  ya yi yana jin jina kai, Mame da Ihsan, Anty Maimuna  harma da Ammar da ya yi kamar baya falon dariya abun na Jannat ya basu saboda saurin karɓe zancan da ta yi haɗe da bada amsa kamar za'a rigata.

“To Akku sarkin katsalandan ki bar wadda aka tambaya mana ta bada amsa chai-chai kin fara zuba kamar ke aka tambaya” Ammar ya yi maganar yana murmushi haɗe da miƙewa tsaye don yasan yau kam ya taro wa kansa March.

Ilai kuwa tun bai gama magana ba ta zaburo zata yi kansa cike da faɗa A.RASHID ya yi saurin  riƙeta cikin muryar lallashi ya ce“Oh! Sweetheart mai yasa ki ke da rigima ne? Yayanki ne fa! Bana son yawan faɗan nan kinji! ” ya ƙare maganar yana jawota jikinshi yana bubuga bayanta alamar lallashi.

“Dady....”

“Shiiiii”ya yi saurin katse ta yana ɗora hanunsa a kan bakinta alamun ta yi shiru.

„Kina son ki shiga Aljanna? ” ya yi maganar yana ɗagota daga jikinshi.

“Eh Dady”

“To ki daina faɗa da rashin haƙuri kinji!”

“Dady idan na daina zan shiga Aljannar?” Ta yi maganar idanunta har sun fara tara hawaye.

“Eh! In sha'Allahu kuwa” ya yi maganar yana buga bayanta cike da lallashi.

“Dady to na daina amma shima ka ce ya dena sa min baki  in ina magana”
Ta yi maganar cike da shagwaɓa.

“To Mamana angama, kai Ammar karka kuma yiwa Mamana haka!” Ya yi maganar shima da kwaykwayon yadda ta yi maganar yana kallon Ammar.

Dariya dukansu suka kuma kwashewa da ita wanda ya sake tunzura Jannat ta kuwa fashe musu da kuka wiwi. 
Lallashinta Dadynta ya ci gaba dayi da ƙyar ta yi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Abincin dake gabansa ya fara ɗiba yana saka mata a baki tana ci nan da nan ta ware kamar ba ita ta gama rigima ba.
Ihsan ce ta miƙe zata koma gaiding ai kuwa Jannat na ganin ta nufi ƙofa ta ce“Dady na ƙoshi' Anty Ihsan tsaya ni”
ta yi maganar tana tashi daga Jikin Dadyta ta nufi Ihsan, ranƙwashe kan Ammar da ya dawo kusa da A.Rashid ta yi  sannan ta zura da gudu tana dariya ta fice daga falon.

Murmushi kawai A.Rashid ya yi yana girgiza kai shi ya rasa a ina Jannat ta kwasu wannan faɗan sam ba tada haƙuri duk abinda aka yi mata sai ta rama Addu'ar shiriya ya yi mata sannan ya fara cin abinci tamakar baya so.

Anty Maimuna da suke ta hira da Mame tashi suka yi suka bar musu falon don sufi sakewa su kuma suka hau sama. Falon da yake sama suka zauna Mame da bakinta ke ɗauke da magana ce ta fara ce wa “Maimuna nifa akwai maganar da nake so dama muyi da ke!” Ta yi maganar fuskarta da murmushi.

“To Mamen ina saurarenki” ta yi maganar tana ƙara mai da hankalinta gurinta tana murmushi.

“A kan ƙanwar nan taki ne shin tana da aure? ” Mame ta yi maganar cike da fargabar amsar da zata fito daga bakin Anty Maimuna.

“Mame ba tada aure yanzu tana zawarci ne”ta yi maganar cike da tunanuka iri-iri dan gane da tambayar Mamen.

Ajiyar zuciya Mame ta saki tana godiya ga Allah da wannan furucin na Maimuna “Maimuna nasan za kiyi mamakin tambayar da na yi miki to ba komai yasa ba sai son da nake mu ƙara ƙarfin alaƙarmu da ku ta hanyar Ƴar'uwaki. Tun ganinta da na yi yanzu naji ta kwanta min saboda nutsuwarta da hankalinta in ba damuwa zanso ki ɗan bani labarinta ko ba yawa don banaso abin yaja lokaci kuma ina fatan wani bai rigamu ba!” Mame ta yi maganar fuskarta da murmushi tana duban Anty Maimuna.

“Alhamdulilah Mame a sanina dai babu wanda ya rigaku don tana gidan nan ma ta fita daga idda, labarinta kuma zan baki labarinta don na yarda dake Mame ke ɗin tamkar Mahaifiya nake kallonki”Anty Maimuna ta yi maganar tana duban Mame yanyinta na sauyawa saboda tuna yadda rayuwar gidan auren JIDDO ta kasance.

WACECE JIDDO?

Zuri'armu zuri'a ce da ta tashi da soyayyar juna da haɗin kai,  mahaifinmu Ibarahim  da mahaifiyarmu Hafsa sun kasance Ƴan uwa ne na jini wanda a al'adar zuri'armu da zarar Mace ko Namiji sun tasa sun isa aure za'a haɗa su aure ko da basa son junansu,  haka zasu haƙura su zauna da junansu ba tare da jayaya ba.
A haka Familyn mu ya ginu har kawo lokacin da namu iyayen suka isa aure, haka suma aka haɗasu aure cikin ƙanƙanin lokaci.

Cikin amincin Allah suka karɓi auren da aka yi musu hannu biyu suna zaune lafiya, sai da Mahaifiyarmu ta shekara biyar a ɗakin aurenta kafin Allah ya azurtasu da ƙaruwa aka Haifi  Ɗa Namiji wanda aka saka masa suna Ahmad shekara biyu tsakani Allah ya kuma azurtasu da wata ƙaruwar ta kuma haihuwa inda ta samu Ɗiya Mace,  aka saka mata suna Zainab shekarar zainab ɗaya a duniya Alah ya karɓi rayuwarta sakamakon ƙyanda da ta yi Allah kuma yasa ba mai tsahun kwana ba ce.

A wannan lokacin Mahaifiyarmu bata kuma haihuwa da wuri ba sai da ta yi shekara biyar inda Allah cikin ikonsa ta kuma samun ciki yana isa haihuwa ta kuma haifuni inda aka saka min suna Maimuna wanda a lokacin ne Baba tsohu mahaifin Babanmu ke shirin haɗa ƙanin babanmu aure da Hajjo  wadda da Babarta da Babar mahaifiyarmu uwa ɗaya uba ɗaya suke. Sosai aka sha fama gurin wannan haɗi domin shi kawo Auwalu  sam bashi da ƙaunar wannan auren zumuncin da ake,  da ƙyar aka samu aka shawo kansa ya yarda da auren bayan irin barazanar da Baba tsohu mahaifinsu ya yi masa, shekarata huɗu Allah ya kuma azurta Annarmu da wani cikin wanda itama Hajjo Matar kawo Auwalu a lokacin Allah ya azurta ta da ciki kusan tare sukai ta rainun cikinsu lokacin da cikin Annarmu ya isa haihuwa nan Allah ya kuma azurta ta da Ƴa Mace inda aka saka Mata Hauwa'u Maijidda,   sati biyu da haihuwar Jidda Allah ya sauki Hajjo itama lafiya ta haifu Ƴan biyu duka mata. 

JIDDA ta tasu da kazar-kazar ga ɗan karen wayoo da uwa uba biyaya ga basira, lokacin da aka saka mu makaranta cikin ƙanƙanin  lokaci Malaman makaranta da ɗalibai suka san Jidda saboda ƙwazonta tun tana ɗaukar na uku idan anyi Jarrabawa Jidda ta dawo tana ɗaukar na ɗaya a ajinsu, ba kuma iya isalamiya take da ƙoƙari ba har boko. Son karatunta da dagewarta yasa tun muna ƙanana ta taso da buri fiye da namu don ita ta taso da burin yin ilimi mai zurfi sosai.

Sosai ta taso da son aikin likitanci bata da magana sai ta likita ko labari aka zo ana yi indai aka sako  likitoci kaga  Jidda a gurin.
Lokacin da ta shiga secondary school,  Lokacin ni  ina aji uku na junior A lokacin ne kuma Baba tsohu kwatsam ya ce ya bada aurena mun shiga da muwa ba ƴar kaɗan ba amma sanin Baba tsohu baya magana biyu haka muka fawwala wa Allah lamarinmu muka dage da Adu'a saboda yadda Anna ta dinga yi min nasiha.

Ba'a ɗau lokaci ba aka tsai da lokacin bikina  da Tahir wanda ya kasance Mahaifinsa abokin Baba tsohu ne, a wannan lokacin ma nasha kuka kamar babu gobe kafin daga baya na dawo na danga na.

Lokacin bikina na zuwa aka yi shagali kamar yadda aka saba aka kawoni nan Kaduna. Ko da aka kawoni lokacin da su Jidda zasu koma da ƙyar muka rabu ita kuka ni kuka. 

Shikarata uku da ƴan watani a gidan aure Lokacin har na yi haihuwar farko ita kuma Jidda sannan ta shiga aji na huɗu a makaranta zuwa lokacin har ta sauƙe Al-ƙurani mai girma ta kirqni tana kuka take faɗa min Baba tsohu ya bada aurenta cike da tashin hankali nake faɗin “hello mai ki ka  ce Jidda? ” saboda yanda maganar ta dake ni sosai.  Tun bayan aurena duk da dacen  da na yi na Mijin ƙwarai da yake nuna min ƙauna   a kullum Adu'a ta Allah yasa a bar Jidda ta yi karatun da take burin yi.

Sosai na shiga damuwa har na kasa samun  kwanciyar hankali saboda tunanin halin da Jidda ke ciki, ina ta kuma neman wayarsu bana samu har tsahun yini biyu da kiran da ta yi min.  Ganini irin halin da nake ciki da Tahir ya yi yasa ya shirya min.....

MAMAN NABEELA CE

JIDDO(Gidan Aurena) Where stories live. Discover now