*JIDDO*
*GIDAN AURE NA*
*BY*
*MAMAN NABEELA**DASHEN ALLAH WRITER'S ASSOCIATION*
_*PAGE* 9️⃣
Salma dake wanki a tsakar gidan ce baki washe cike da murna tace “lah! Ga Ammeyn mu ga Ammeyn mu ta dawo oyoyo oyoyo” tayi maganar tana nufar inda take ta rungumeta.
Jiddo fuskarta cike da fara'a take amsata. Su Asma'u ne suka shigo ita da Azima ko wanne hannunsu riƙe da kaya. Abdull ma da Zainab abinda zasu iya ɗauka suka ɗauko suka biyo bayansu, nan sabuwar murna ta kuma ɓarkewa Salma. Dan dama rashinsu a gidan yasa gaba ɗaya gidan baya mata ɗaɗi. Kasancewar ita ce auta gurin Ummarsu.
Wuce wa su kayi suka shiga ciki. Momy Maimuna ita ce ƙarshin shigowa bayan an gama shigo da komai ta sallami me Motar.
Haya niyar da ake tasa Lubabatu da ke baci, saboda rashin bacin kirki kwanaki nan da take tashi ta leƙo kanta tana karanto adu'o'i kala-kala dan gudun ganin abinda bata shirya masa ba.
Idanunta ta kuma murzawa ganin ƙofar ɗakin Jiddo jibge da kayan abinci “A'a Salma zakka yau muka wayi gari da ita ne? Ya naga kina kaiwa nan? Ko yau Harisun nan suka ce a kai kayan a ajiye? To karki shiga dasu nan kawo min ɗaki na, kai Allah ya yiwa uban gidan Harisu albarka irin wannan kaya haka! Ai zasu yi kusan dubu ɗari a yayin tsadar abin cin nan ai duk wanda yayi maka kyautar abinci inda abinda yafi godiya ma kayi masa kai Allah dai ya........ ”“Kai Umma daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, ai kya tambaya kayan waye ko?” Salma da tayi saroro tana kallon Ummanta ta katseta jin abinda take faɗa.
“Yuh! Salame me zan tambaya? Bayan nasan ba wanda za'a kawowa wannan kayan sai ni uwar Harisu da Shafi'u” Lubabatu tayi maganar tana ɗaukar jarkar mai.
“A'a Umma ki tsaya bafa naki bane na Ammeyn Asma'u ne yanzu ta dawo ita ta zo da abinta” Salma tayi maganar tana riƙe hannun Ummansu.
Daskarewa tayi a tsaye tana tunanin ko dai taji ba dai-dai bane “Salma me kika ce? ” tayi maganar tana tsurawa bakin Salma ido.
“Na Ammeyn Asma'u ne yanzu ta dawo ita tazo da kayanta ” Salma ta kuma mai-maita mata maganar.
“Su kuwa iyayenta me ya sami kansu suka dawo da ita tun bata gama..... "
Bata ƙarasa maganar ba Salma ta rufe mata baki tana nuna mata ƙofar ɗakin alamar suna jinta fa. Buɗe baki tayi zata kuma magana fitowar Asma'u yasa ta fasa, ta fara murmushi tana cewa “Ma'u ashe kun dawo, ina Ammeyn taku? tana ciki? ”“Eh Umma ina wuni” Asma'u ta gaisheta.
“Lafiya lau kai masha'Allah jibi yanda kuka yi kyau da kuka kwana biyu bakwa gidan nan kamar yaran masu kuɗi! ” Lubabatu tayi maganar tana binsu da kallo.
Ba tare da Asma'u ta kuma magana ba ta kama hannun Zainab da taga zata fara surutu su kayi hanyar soru.
Sai da suka fita sannan Lubabatu ta ɗauke kanta daga kansu, ɗakin Jiddo ta shiga.
“Salamu alaikum ashe masu jego ne suka dawo?” Lubabatu tayi maganar tana zama.“Eh wallahi Ummansu ina wuni” Jiddo dake gefen gadonta zaune ta amsa mata haɗi da gasheta.
“Lafiya lau kin sauka lafiya? ya kwanan Ussaini da ƙarfin jikinki? ”
“lafiya lau alhamdulilah”
Jiddo ta faɗa.Gaisawa su kayi da Momy Maimuna dake shiryawa Jiddo kaya a sif.
Azima ma gaisheta tayi ta amsa tana daɗa bin Jiddo da kallo ganin mugun kyan da ta ƙara ga mur-murewa da tayi, kamar wadda aka yiwa wankin inji sai kyali take, duk da kishin daya fara ɗan taɓɓata na irin yadda Jiddo ta ƙara zama wata kya-kyawa haka ta dane tana cewa“kuyi mini aikin gafara fa wallahi naso naje Asibiti na duba ku Suwiɗi ya hana ni, kinsan rashin mutuncinsa. Idan na fita ban san wane rashin imani zai aikata min ba yadda ya ɗau zafi a lokacin shiyasa ban je ba. Ranar suna kuwa shima nasu zuwa amma wata masifar na kuma gamuwa da ita, ita ta hanani zuwa”
Lubabatu ta ƙarashe maganar da fuskar tausayi.
