*JIDDO*
*GIDAN AURE NA*
*BY*
*MAMAN NABEELA**Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y
_Chat me on_ :07042808467
*Page* 1️⃣7️⃣
_______Ƙafafuna ke neman kasa ɗaukata saboda tashin hankalin da na gani da yafi na da, kamar yarinya buduruwa nake hanguwa kwance tsirara cikin ɗakin. Ƙara zaro idanuna nayi bakina na rawa ina nuna cikin ɗakin cike da tashin hankali.
Wannan wace iriyar musifa ce nake gani!
Gaba ɗayansu suka zuba min ido suna kallona babu wani alamun firgici a tattare dasu. Wani irin murmushi naga Suwiɗi ya saki yana nufu gurin da nake hannunsa riƙe da wata ƙwarya ya na ta karanto wani surkulle, tamkar an sakan mazari haka jikina ya fara rawa duk yadda nayi ƙoƙarin motsa ƙafafuna dan nayi baya abin ya gagara, a cikin raina ina ta ƙoƙarin karanto addu'a amma bakina tamkar ansa min super glue an manne. "Yarinya kin sauƙaƙa mana aiki kin kawo kanki da kanki inda ake nemanki!! Hhhhhh” naji sautin murya kamar ta Suwiɗi na maganar sama-sama saboda kaina da ya fara juyawa.
Hayaƙi ya fara tirniƙe gurin take na yanke jiki na faɗi Dishi-dishi nake ganin inuwar Suwiɗi a kaina yana dariya ya ɗaga ƙwaryar hannunsa ya watsa min abinda ke ciki daga nan ban sake sanin mai yake faruwa ba.
★★★★★★★★
Sautin koke-koke da yake shiga kunnuwa na yasa na buɗe idanuna da suka yimin nauyi, saurin rufe idona nayi saboda hasken da ya shiga ina ƙara buɗe shi a hankali bin ɗakin nake da kallo kafin na juya da kaina ina kallon mutanen da suke kusa dani.
Asmau da Zainab da su Lubabatu ne da ban san yaushe suka dawo ba zaune suna ta kuka, motsa jikina nake ƙoƙarin yi inaso na tashi amma naji na kasa. Hannaye na na kuma yinƙurin motsawa amma suma na kasa tamakar wadda cutar laka ta samu haka jikina ya koma kaina kaɗai ke motsi, bakina na buɗe zanyi magana amma shima naje muryata taƙi fitowa hawaye ne suka fara zubuwa daga idanuna a zuciyata na fara faɗin “innalilahi wa inna ilaihirraji una" ina rintse idona.
“Ammey! Ammey!! Lah! Ummansu Salma kinga tana hawaye? ” Asma'u tayi maganar tana jijigani.
Dukansu matsowa su kayi inda nake a kwance“gyara Asama'u mu gani”Ummansu Harisu tayi maganar tana matsowa itama.Buɗe idona nayi ina kallonsu hawayen idona na ƙara zubuwa.
“Lah! Asama'u da gaske ta farka kalli ta buɗe idanunta, sannu Jiddo kwana biyu ace mutum na kwance shi ba gawa ba shi ba mai rai ba wannan wacce iriyar faɗowa ce ki ka yi haka? ”Lubabatu tayi maganar cike da alhini.“Sannu Ammey na kamaki ki tashi ko zaki iya tashi da kanki? ”Asma'u tayi min maganar tana kama hannuna.
Wasu hawaye masu zafi ne suka ƙara fitowa daga idanuna, jin abinda Ummansu Harisu ta faɗa “wa ya faɗa musu faɗowa nayi? Ko Suwiɗi ne ya faɗa musu faɗuwa? Tabbas irin su Suwiɗi su ake kira Kura lulluɓe da fatar Akuya”
nayi maganar a zuciyata ina kallonsu.“Asama'u kamata mu ɗagata yadda ta jima a kwancen nan ai ba lallai ta iya tashi ba da kanta, ke kuma Salma kiyi maza ki haɗa mata ruwan zafi ki kawo tasha in taji ƙwarin jikinta sai tayi wanka” Ummansu Harisu tayi maganar tana kamani.
Duk yadda suka yi ƙoƙarin ganin na zauna da kyau kasawa nayi sai da aka jingina ni da jikin filo, shayin da Salma ta haɗa aka miƙo min na karɓa amma ilahirin jikina ba inda nake iya motsawa sai kaina.
Kukan da bashi da sauti sai hawaye na kuma saki zuciyata na ƙara ruruwa da tsananin ƙiyayar Suwiɗi wadda a yau nake dana sani ta gaskiya gurin zamuwarsa Uban ƴaƴana, Asma'u ce ta karɓi shayin ta suma bani bansha da yawa ba na fara kelaya amai kamar zan Amayar da kayan cikina gaba ɗaya jikina ya ɓaci.
“Subahanallahi amai kuma take yi? ” Ummansu Harisu tayi maganar tana fitowa daga banɗaki tana ƙarasowa gaban gadon da nake kwance.
“Eh Umma amai take duk shayin da ta ɗan sha ma kinga ya dawo” Asma'u rayi maganar tana ƙoƙarin goge mata jiki.
“A'a kinga bari na kama miki ita mu kai ta banɗaki sai ki wa-wanke mata jikin, kinga ya ɓaci da yawa ko taji ƙwarin jikinta ma” Ummansu Harisu tayi maganar tana kamani.
Ta da ni tsaye Ummansu Harisu da Salma su kayi, ƙafafuna ne suka fara rawa nayi baya zan faɗi da sauri suka taro ni sai da suka saka hannunsu ta bayana suka rungumoni sannan suka kaini banɗaki. Kujerar da Asma'u ta kai aka zaunar dani aka jingina ni da jikin bango bayan sun fita Asma'u ta wanke min jikina tass idanunta cike da hawaye, kayana da Salma ta miƙo Asma'u ta saka min sannan ta yi min alwala suka kuma kamo ni aka fito dani.
“Sannu Jiddo Allah ya baki lafiya” Ummansu Harisu tayi maganar tana zaunar dani kan daddumar da aka shimfiɗa tana jingina ni da jikin bango.
Da kai na amsa mata hawayen idona na zubuwa.
Daga zaune nayi duk sallolin da ake bina, sai da nazo yin addu'a hawayena ya kuma ƙaruwa tsananin tsanar Suwiɗi na kuma ƙaruwa a cikin zuciya da ruhina. Nayi kuka kamar babu gobe na yadda Addu'a ma na kasa ɗaga hannuna nayi saboda iftila'in sharrin Suwiɗi da ya yi tasiri a kaina.Bayan sun kamani sun mai da ni kan gado aka kuma haɗɗa min wani shayin sai da na shanye shi tas sannan Asma'u ta fara bani abinci banci da yawa ba na gir-giza mata kai alamar na ƙoshi, goge min bakina tayi wanda yayi dai-dai da shigowar Suwiɗi.
“ashe kin farka! kufa masu hawan jini haka lamarin ku yake baku da wuyar yanke jiki ku faɗi, toh Allah ya kiyaye gaba, Lubabatu ungo wani magani dana karɓo mata ki ringa bata wannan tana sha wannan kuma ki ringa shafa mata a jiki ko da wani gurin ya dena motsawa a jikinta zai temaka mata” Suwiɗi yayi maganar yana miƙa mata maganin.
Tunda ya shigo kallo ɗaya nayi masa na ɗauke idona dan bana ko ƙaunar ganinsa maganar da yake tasa na ɗago ina kallonsa cike da mamaki idnuna cike da hawaye ina ta motsa bakina inaso nayi magana. Tabbas da bakina zai buɗe da sai na yiwa Suwiɗi wankin babban bargo da sai na tuna masa asiri kowa yasan waye shi....
“Buɗe bakin kisha kinji Jiddo ko Allah zai sa ki iya yin magana in kin sha” Ummansu Harisu tayi min maganar tana kai min robar maganin da Suwiɗi ya bata bakina.
Datse bakina nayi ina gir-giza kai na hawaye na kuma ambaliyar zuba daga idanuna.
“Au! Bata iya magana ne?
_Pls Share & comments_ 🙏🙏🙏
*MAMAN NABEELA CE* ✍️
![](https://img.wattpad.com/cover/361380842-288-k269912.jpg)