*JIDDO*
*GIDAN AURE NA*
*BY*
*MAMAN NABEELA**Follow my whatsapp channel on:* https://whatsapp.com/channel/0029VaEXHzuBPzjTpTqZm13y
_Chat me on_ :07042808467
*Page* 1️⃣8️⃣
Suwɗi yayi maganar yana ƙara matsowa gurin da nake a kwance.
“Eh wallahi kaga tunda ta farka bata magana sai kuka ga jikinta sam ta kasa ko tashi da kanta, gaskiya ya kamata a faɗawa iyayenta ko a kai ta Asibiti duba fa ka ga yadda ta koma! Oh! Ni ƴasu Allah kasa mu dace, tunda nake ban taɓɓa ganin me hawan jinin da daga faɗuwar farko ace komai nasa ya dena aiki haka kamar Jiddo ba wannan wace iriyar faɗuwa ce? Kamar wadda ta faɗo daga bene!” Lubabatu tayi maganar tana share hawayen dake fitowa daga fuskarta haɗi da fyace majina.
Wani banzan kallo Suwiɗi ya watsawa su Salma da Asma'u dake zaune, sum-sum suka tashi suka yi waje zama yayi gefen gadon da Jiddo take ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan yace “kin gama Uwar ƴan gwalan-gwaso? Toh ki buɗe kunenki da kyau ki jini babu wanda za'a kirawo yazu yayi mata magani ni Mijinta ni zan ringa kawo maganin da za'a yi mata har Allah ya bata lafiya, kuma wallahi ko da wasa naji wani ya kirawo wani a gidansu wallahi! Wallahi!! Haɗuwarmu ba za tayi kyau ba kinji dai na faɗa miki! ” Suwiɗi yayi maganar yana jijiga kai haɗi da gir-giza ƙafa fuskarsa babu alamun fara'a.
“Amma Malan Iyayenta fa nace ba wasu....”
“Lubabatuu!” Suwiɗi ya katse mata maganar da kiran sunanta cikin ƙaraje wanda har su Asma'u dake waje sai da suka razana.
A firgice ta ɗago tana kallonsa jikinta na rawa.
“Bani maganin!” yayi maganar yana miƙa mata hannu.
Jiki na rawa ta miƙa masa maganin dan ita yanzu Suwiɗi lamarinsa tsoru yake bata dan da taje ƙauye da, cewa tayi baza ta dawo ba sai da Yayanta ya matsa mata sannan ta dawo saboda irin yadda ta fara zargin Suwiɗi.
Ina kwance ina kallon duk abinda ke faruwa hawaye sharkaf idanuna, ƙara datsi bakina nayi ganin ya karɓi Rubar da yake ikirarin maganine a ciki ya nufu da ita bakina. Yanzu duk abinda Suwiɗi yayi min be ishe shi ba sai ya kuma bani abun tsafinsu toh ko dai kashe ni yakeso yayi....
“Buɗe bakinki kisha ” Suwiɗi yayi min maganar yana ƙara tamke fuska wanda shi ya katsi min zancan zucin da nake.
Ƙara rufe bakina nayi gamnaƙi buɗe shi duk yadda yayi na buɗe bakina naƙi buɗewa.“Malan kawo zan bata ta yiyu yanzu ta ƙoshi da yawa ne tunda bata daɗe da cin abinci ba kawo in anjima sai na bata” Ummansu Harisu tayi maganar ganin yana ƙoƙarin matse min baki ya ɗora min.
“Kin tabbatar zaki bata? Ni fa ba naso nayi asarar kuɗina” yayi maganar yana ɗagowa daga sunkuyon da yayi zai matsewa Jiddo baki.
“Eh eh! Zan bata Lubabatu tayi maganar cikin rawar murya.
Ina gani ya miƙa mata Robar yayi waje na saki wata ajiyar zuciya ina Addu'ar Allah yasa kar ya kuma dawo wa dan bana ƙaunar ganin shi taɓɓas da ƙafafuna lafiyarsu ƙalau da ko kwana ɗaya bazan ƙara a gidan Suwiɗi ba, Addu'ar da Anna ta faɗan na dinga yawan yi ce ta faɗo min a rai take na suma yinta ina fatan Allah ya kawo min ɗauki na halin da nake ciki ya kawo min mafita.
★★★★★★★★
Da daddare bayan an kaini banɗaki nayi alwala nayi sallah abincin Asma'u ta zuba ta suma bani ba laifi nafi ɗazu ci da yawa Addu'o'in da Asma'u tayi a ruwa ta bani nasha. Naji daɗin ruwan dan abubuwan da nake ji cikin jikina naji sun ɗan rago rubar da Suwiɗi ya bayar ta magani Ummansu Harisu ta miƙo tana cewa “Asama'u zuba a kofi ki bata tasha maganin da babanku ya kawo mata ne! ”
Karɓa Asma'u tayi ta zuba a kofi tana ƙare masa kallo ganinsa baƙi wulik har wani ɗaukar ido yake ta ajiyeshi a gefe tana cewa “bari a ɗan jima sai na bata ko in zamu kwanta baci ne”
“Toh amma ina Malan ya tambaya kawai kice tasha nima haka zan faɗa masa”
Ummansu Harisu tayi maganar tana tashi.“Toh”
Asma'u ta amsa mata.Fita Ummansu Harisu tayi Asma'u kuma ta kwashe kayan da naci abinci ta fita dasu.
Kamar jira ake su fita daga ɗakin na rufe idona kamar mai baci sai ji nayi kamar motsi a cikin ɗakin, tsoru ya kamani amma sai na fara karanto Addu'a ina buɗe idona duhu dunɗim babu haske mamaki ya kamani mai ya samu hasken ɗakin ya ɗauke lokaci ɗaya?Nayi maganar a zuciyata cike da tsoru na cigaba da duk Addu'ar da tazu bakina, tsoru ne ya kuma kamani jin kamar ana dambe a cikin ɗakin dan komai dake cikin ɗakin ji nai yana motsawa kamar a san-sanin yaƙi nake. Kuka na kuma saki ina ƙara karanto duk Addu'ar dake bakina“Allah ka kawo min ɗauki” nayi maganar cikin raina cike da tausayin kaina ina tunanin ina Asma'u ta tsaya bata dawo ba daga kai kwanikan?
Gadon da nake kai naji yana ji-jiga take na saki fitsari tsabar tsoru ina saddaƙar da shikenan rayuwata tazo ƙarshi....Ƙarar buguwar abu da jikin gadon da nake yasa na sume ba tare da na shirya ba.
“Ammey! Ammey!! Ga Yaya Asma'u can ta faɗi a falo tana fitowa daga kichin mai ya samu ɗakin ki ya hargitse?
Abdull da ya shiga ɗakin da gudu yana ƙwala mata kira yayi maganar yana kallon ko ina na ɗakin ganinsa kaca-kaca..... ✍️
Pls
_Share & comments_*MAMAN NABEELA CE* ✍️